Anya Baiwa ce Complete Hausa Novel

Anya Baiwa ce Complete Hausa Novel

Anya Baiwa ce Complete Hausa Novel: Tafe take tana an waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu an alheri aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke unshe cikin bakin ta aan diriri ce ta kalle shi ta ce

Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare

Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ara karantar yanayin ta sannan ya ce Tauraruwa mai wutsiya Kura kike ga tsoro ga ban tsoro Ina zaki kike sauri kina ta juyejuye haka Sai da ta juya hagu da dama ta kuma lea soron arshe tana mai mia wuya cikin asa da murya ta ce Gobara daga teku maganin ta sai Allah wata ura ce take oarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na ta arasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta

Jakadiya Kubura kenan ay harbi ga an jaki gado ne kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke ya faa cikin son jin labarin

Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce Kasan koda girgiza kurna tafi magarya mai tsoron a mutu shi yake maho ara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce aramar kyauta tafi babbar rowa ta arasa faa tana mia masa hannu alamar ya bata wani abu

Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana fain Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya kuma Kura kike mai manta alherin baya

Juya su tayi cikin jindai ta kunto bakin zaninta ta auresu tana fain Domin rana aya baa in zuguri kuturu da kuinsa alkaki sai na asan langa bue kunnen ka yanzu zaka sha labari ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce Lallai tsugunne bata are ba ansai da kare an sayi Mage naji dain wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki ya faa yana yin gaba abinsa

Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ofa ta ce masa Injunan ka sammako wani tafe ya kwana kuma hargagin an damisa bashi tsorata Namijin zaki ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata Tabbas inkaji mutum na tsoron dare baa aure shi ya wance bane Ki bar ganin allura arama itama arfe ce dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi yana gama faa ya sanya kai ya fice daga cikin soron

Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce Mai afa huu ma ya fai bare mai biyu ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe tana faa ta juya ta cigaba da tafiya kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa

Tana shiga ta zube asa cikin salon kirari ta fara magana Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai ar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki Uwar Sarki Allah ya ara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba aya ta ku ce Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin dain kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da fain Jakadiya anjima zan turo da saon mai mai ke tafe da ke russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki au mataki kuma asan abin yi Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama amma dukda haka ba zaa rasa abinyi ba dan baa rasa nono a riga ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai dai bane ranki shi dae

Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya fai saboda tasan labarin bazai mata dai ba shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya Jakadiya banasan Kewayekewaye tafi kanki tsaye Me yake faruwa ne

Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu kuma ayanayin dana lura har yayi wari cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta unduma wani ashar sannan ta ce Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri

Jakadiya ta bata amsa da A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk

Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na fain Ya isa haka Lallai Fulani Zaliha ta ebo ruwan dafa kanta Samun sararin kuturu gaa a cikin rama wato haka ta mie afa da yawa Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ara faruwa yanzu tabbatas dole labari ya ara maimaita kansa Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Ishai

Jakadiya najin haka ta kuma rissinawa ta ce ALLAH ya huci zuciyar Fulani Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haa sahu da Uwar akina ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci Jakadiya na gama faa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba aramin alheri zata samu ba

Tunda Jakadiya ta fito daga akin Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take abun duniya gabaaya ya isheta ita kaai sai saa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita Jaririnta an kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta auke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta

A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha

Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faa bakin ta auke da sallama Balaraba matar Ciroma dake tankae ta amsa mata sallamar tana fain

Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne cigaba da tankaenta tayi ta bawa Jakadiya amsa Ni na isa nace banten Sarki yayi urtu ai hanyar lafiya abita da shekara meye labari Dan nasan bakin ki baya rasa motsi

Murmushi Jakadiya tayi ta ce Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani kuma abokin cin mushe baa oye masa wua wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na auke da juna biyu Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi ta faa tana asaasa da murya

Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ofa tayi sannan ta cewa Jakadiya Da gaske kike wannan maganar aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata dai ba kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya

Jakadiya ara matse bakin zanin ta tayi ta ce Ai a bakin wawa akanji magana wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar

Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji dain maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani Tafasar tukunya bata gefe aya bace haka nan abinda baki ya ulla hannu bashi iya kunce shi idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haia ya taka dutse Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito kuma ni nan da kika gani na iya taku na

Miewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara aurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ofa sannan ta juyo ta ce Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama bai bakinki dai anin afarki kuma harshenki linzaminki bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_
26092021 0158 Ameera Adam FIRST CLASS WRITERS ASSO

ANYA BAIWA CE

Na

AMEERA ADAM

_LITTAFIN NAN NA KUI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI GAME BUATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400 GABAAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT IN FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZAA TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624 DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_

FREE PAGE 2

 

Da daddare Bayan sallar Ishai Jakadiya ce tafe tana lalube har ta arasa sashen Fulani Maryama da sallama ta shiga ta russuna tana cewa Barka da hutawa Uwar akina ance kina san ganina yanzun nan

Fulani Maryama dake tsaye hannunta auke da Salman miawa Jakadiya shi tayi ta ce Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba batare na nemi mafita ba
Rie Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai wace shi sannan ta ce Duk abinda kika ce haka zaayi bani da ikon bijirewa umarninki da kai da kaya duk mallakar wuya ne

Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin akinta cen asan adakarta ta bue ta auko wani kurtu tasa hannu ta ebo waansu irin wuri guda biyu da wani an aramin zobe maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye

Miawa Jakadiya Wuri aya tayi sannan ta fara karanta waansu irin alasiman tsafi baa auki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ace daga cikin akin

Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani suruin daji mai matuar duhun gaske Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara walawa bokan kira har sau uku Marduska Marduska Marduska tana gama faa ta bue idanunta

Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka an auki lokaci anayi sannan aka tsagaita sannu a hankali haske ya mamaye gurin cikin wata irin murya aka fara basu umarni Ku sanya afafunku cikin waccen ar oramar sannan ku tako ku shigo ciki

Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa gaba aya jikinsa lullue yake da gashi tamkar ba bil Adam ba Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya

Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya aga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana

Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaarsa tai ruwa Maryama kin auke mana afa na wasu shekaru sai da buatarki ta tashi zaki waiwayo mu

Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce A gafarceni sarkin bokayen duniya nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu bazaa sake ba

Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake kalli nan ya janyo wata warya mai cike da jini yana nunawa fulani

Tana leawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance jinjina kanta tayi ta cewa Murduska Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba aya domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba

walawalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zai badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta are gaba aya A zabure Fulani Maryama ta ce Ban fahimce ka ba Marduska

Wani mudubin tsafinsa ya auko yasa wata jelar auna dake hannun sa na hagu cikin waryar ya yarfawa mudubin inuwar wani an ananin Yaro ce ta bayyana na an wani lokaci sannan ta ace maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce Alalami ya riga da ya bushe duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi Zata haifo a namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne mahaifinsa ba Aminullah ba

Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na

Wani Allon jar asa ya auko ya jingine ya na faan waansu irin kalmomi yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani oon kan warangwal yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar asa ya ruguje wani irin hayai mai wari na fita daga jikinsa

A tsorace gaba aya suka ja baya Marduska ba aramin tsorata yayi da ganin faruwar haka cikin yanayin firgici ya fara magana Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho

Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi

Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ebo wani garin magani mai hae da garin naman mage da haoran jemage ya zuba aciki take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ar aramar orama ta bayyana aciki daga cikin oramar wasu litafan tsafinsa ya ebo guda biyu ja da bai bain ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin warya sannan ya zura kansa yana karewa waryar kallo dake ta zaalala

Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani Tabbas cikin biyun zaa iya gudanar da aya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne zaa binciko domin kuwa allura ce zata tono garma

Fulani Maryama harta fara jin dai arshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce Bangane mai kake nufi ba mayar da waryar yayi cen gefe ya ce Abinda na gani kenan zai ya ragewa mai shiga rijiya kowanne zai kika auka yana da nashi alubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba haka ba zakiyi gudun gara ki faa gidan zago

Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke fain Lallai Fulani Maryama kema ba aramar makira ba ce amma ajuri zuwa rafi Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere amma lallai wannan a na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah wata ila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya dama ance kayun an warai ya gaji Ubansa

Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce Fulani Maryama ta faa

Mie afafunsa yayi da gaba aya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da zaa zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Nauda zaki turara mata karki bari yaro ya fao ba tare da kin turara shi ba to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda zaa furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa

Murmushin jin dai Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata Sai dai akwai sharain da zaki kiyaye akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi zata shigo cikin gidan masarautar ku tana asantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar abubuwa marasa dai zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haa ido a ranar aljanun dake rie da afafunsa zasu tarwatse aladarinsu zai karye idan kika yi sake ta au wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke rie da bakinsa zasu gushe zai fara magana sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba yayyautawa kamar zai amayar da an hanjinsa hakan zai aga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_
26092021 0213 Ameera Adam FIRST CLASS WRITERS ASSO

ANYA BAIWA CE

Na

AMEERA ADAM

_LITTAFIN NAN NA KUI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI GAME BUATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400 GABAAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT IN FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZAA TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_

FREE PAGE 3

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa Wace ce yarinyar Kuma daga wane gurin zata xo Babu damar dakatar da zuwan nata Ya zaay na gane ita ce dan na auki matakin daya dace akanta

Boka ya ce Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita in FILSIFI ce abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci tarraya ko haakar shuaun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta zo ki duba nan ya arasa faa yana bue mata wannan jan littafin da ke gefensa

Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga asan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu ta farko ya fara nuna mata yace Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata ar Sarkin jinsin Fararen Aljanun arashin asa ce tunda take bata taa taka doron asa ba

Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faa ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat ar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron asa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf AS ita kuma tunda ta ke bata taa nutsawa arashin asa ba a matsayinta na jinsin aljanu kuma ita Kalimsiyat mace ce mara hauri mai faan gaske kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne sai dai banbancin nahiya da zamani
Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aarshen zamanin nan sunanta Rayzuta ita ta haa dukkan abubuwan da waancen suke dashi harma da wanda suka rasa ar baiwa ce me auke da oyayyun alamura ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba

Yana rufe baki cikin azarai Fulani Maryama ta ce To itama ta ukun nasu Aljanar ce kuma meye alaar su da junan su Kuma meye alaarta da gidan masarautarmu

Maryama kenan azarain me kike yi Ai duk gaggauwar asara ta jira samu kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi hauri sannusannu bata hana zuwa sai dai adae baa je ba

Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da Hmmm Marduska ai Ranar biyan buata rai baa bakin komai yake ba na agu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaarsu ta ke

Marduska ya cigaba da cewa Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora asa sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan sai dai bincike ya nuna akwai wani oyayyen alamar dake bibiyar jinin zuriar sarki Aminullahi

Damuwa ce arara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta

Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yaui wata irin ara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata cikin damuwa Bokan ya ce Gaskiya gaba aya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta

Abin duniya gaba aya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana fain Ka taimaka mun kayimun wani abu ni da kai kaai na dogara

Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai babu uwar da zan iya taimaka miki bincike na biyu da zan gaya miki shi ne idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin asa da makwanni goma zai faa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki dai ba dabara ta ragewa mai shiga rijiya

Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka Kaina ya kulle fa dan Allah ka bani mafita katse ta yayi da arfin gaske yana cewa Da alama kin manta dokar kogon dutsen azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki sunkuyar da kai asa tayi ta ce Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ara ja da zamanin ka

Motsa bakinsa yayi alamar jindai sannan ya auko wani ruwa dake cikin tukunyar asa ya aga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya lea wani tiriri ne yake fitowa sai da ya gama kallon waryar ya ce Akwai wasu oyayun alamura mai tafe da saraiya da alama shuaun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa amma bani da tabbas harsashe ne nayi ari wannan Ya mia mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani

Ita wannan layar ki saaleta aakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki wannan kuma ki binneta akan ofar shiga gidan masarautarku bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane to ki saale ta gun da kikasan bazata fao ba ita wannan ta ofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ofar don hana ta shigowa amma banda tabbaci yaini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faowa wata ila kuma bazata fao ba kuma na lura da fauwar gaba a duk lokacin da zaku hau da ita wannan yarinyar sai ki rie wannan duk lokacin da kikaji fauwar gaba ki dinga lura da waanda suke tare da ke ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri

Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke fain Au dama Salman ba jinin Takawa bane Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen babu ko tantama an wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata akin anwa Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya lokaci na nan zuwa da kwaarki zatai ruwa tafiya sannusannu kwana nesa

Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki bakinki anin afarki kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida dai idan na sake naji wata magana ta illa waje to daga gareki ne kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba

Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai asa ta ce Wane ni da wannan anyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi ai duk wanda ya ona rumbunsa yasan inda toka take tsada ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daawa kaina wua ne

Fulani Maryama auke kanta gefe tayi tana fain Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faa domin ni ginshiin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka fai idan kunne yaji gangar jiki ta tsira Jakadiya haiye yawu tayi mai aci saboda jin haushin maganar Fulani cikin zuciyarta wafa tayi ta ce Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya

Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buata ba amma ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har arshen zamani Fulani Maryama ta faa tana karar layun da ya bata

Cikin jindain kirarinta ya ce Taewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu zan ara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu yana gama faa ya ace daga gurin Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta alasiman tsafin atake haske ya kuma mamaye su suka ace daga gurin

Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ananan dabobbi Fulani karar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata uda wajen kwaayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba rissunawa Jakadiya tayi ta ce Ina ankare ya shugaba ta

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_
10102021 1711 Ameera Adam FIRST CLASS WRITERS ASSO

ANYA BAIWA CE

Na

AMEERA ADAM

_LITTAFIN NAN NA KUI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI GAME BUATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400 GABAAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT IN FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZAA TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR0706 206 2624 DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_

FREE PAGE 4

 

Fulani tae baki tayi ta ce Yayi miki kyau ai kowa rai ya yiwa dai baya mai shi ba magana ta arshe da zan gaya miki kiji ki i ji ki gani ki i gani zaki iya tafiya tana gama faar haka ta juya ta shige ciki ta bar Jakadiya a tsaye

Jakadiya bin bayanta tayi da harara sannan ta juyo ta fi ce daga sashen Fulani Maryama ta wuce cen sashen su

Washe gari tun Asubar fari Lantana ta araso akin Jakadiya hankali tashe tana kwala mata kira tana bubbuga ofar kasancewar bacci bai ishi Jakadiya ba taji haushin tashin da Lantana ta yi mata cikin masifa ta fara magana Ke Lantan wannan kiran mafarautan da kike mun da farar asubahi na lafiya ne Sai kace naci na wani ban biya ba Mtsswwww jaraba kai ko yaushe baka da hutu ta arasa faa tana zare sakatar ofar

Lantana haushi ne ya fara kamata cikin tsiwa ta ce Ke Jakadiya kullin cikin yiwa mutane jaraba kike to kizo kiga abunda Sahura take yi muma farkawa mukayi muka ga tana wani irin abu gaban Jakadiya ne ya yanke ya fai da sauri tayi gaba Lantana na biye da ita

Suna shiga suka samu idanun Sahura sun kakkafe jikinta sai wani irin karkarwa yake bakinta na fitar da dafara Kuka Jakadiya ta fashe dashi tana rungumo Sahura dake cikin wani hali lokaci aya taji Sahura na shauwa jikinta ya sandare daga nan numfashin ta ya auke

Jakadiya rungume Sahura tayi tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya sai da tayi mai isarta cikin jimamin rashin jikarta ta fara magana Shikenan ni Kubura bani da kowa Sahura ke kaai kika rage mun yanxu kema babu ke kin mutu kin barni kaico mutuwa baki mun adalci ba babu aa babu Jika Allah ya jianki Sahura haka Jakadiya ta dinga surutai da yar aka raba ta da gawar jikarta ba aramin tausayi Jakadiya ta bawa mutane ba musamman yanda kowa yasan irin aunar da ke tsakaninta da jikar ta ta aya tilo kafin wani lokaci tuni mutuwar Sahura ta arae cikin gidan bayan ansallaci Sahura mutane suka shiga sintirin zuwa yiwa Jakadiya gaisuwa

Jakadiya ce durushe a akin Fulani Maryama har zuwa lokacin hawaye ne kwance a fuskarta Fulani ce ta fara mata magana Jakadiya ya arin hauri Jakadiya goge kwallar idonta tayi sannan ta ce Da godiya Ranki shi dae

To Allah jian musulmi ga wannan ayi sadaka da shi wata jaka ce ta miowa Jakadiya Jakadiya da tsanar Fulani ta arsu a zuciyarta ji tai kamar bazata kara ba amma gudun kar Fulani Maryama ta ganota yasa ta mia hannu biyu ta kara tana zabga godiya zuciyarta a dagule ta fito daga sashen Fulani Maryama

Jakadiya haka ta shafe kwanaki bakwai cir bata cin abincin sadakar da akeyi da yake ma tana cikin jimamin mutuwar ko yunwar bata cika damunta ba inma taji yunwa sai dai ta nemi gasara ta dama kunu ko tayi faraufarau a duk duniya yanxu babu wacce Jakadiya ta tsana take jin haushin ta sama da Fulani Maryama dan gani take ta sanadin ta ne ta rasa ar jikallenta guda

Bayan kwana biyu Fulani Maryama sai saa da warwara take a cikin zuciyarta tana tuna maganganun da Boka ya sanar mata fargabar abin da zai biyo bayaTa kau sosai da yadda karon farko Boka ya bankao wani muhimmin oyayyen sirrinta amma data tuna irin tuggun da zata shirya sai ta mayar da komai ba komai ba ta zubawa sarautar Allah ido tayi da jiran tsammanin lokacin haihuwar Fulani Zaliha Domin a nan ne zata aiwatar da dukkan udurinta

Bayan kwana biyu Mai Martaba na zaune a turakarsa Fulani Maryama na gefe a zaune ta kalleshi sai dai gabaaya baya cikin walwala cikin kissa ta ce Mai Martaba wannan yanayin sam bai kamace ka ba Allah ara lafiya da nisan kwana shugaba kamar kai wannan yanayin bai dace da kai ba Bango madafar bayi idan har zaka dinga shiga cikin damuwa to mu da sauran talakawanka ya zamu kasance Mai martaba cikin damuwa yace Wallahi ina yawan yin mummunan mafarki akan anwarki Zaliha ina yawan mafarki mara kyau akan cikinta gaban Fulani Maryama ya fai aci rai ya sauka a zuciyarta amma da yake ta iya duniyanci sai ta aro damuwa ta yafa a fuskarta ta ce Haba taamar bayi adalin Sarki mai adalci ai zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi ka kwantar da hankalinka Fulani Zaliha zata sauka lafiya tunda alamar arfi tana ga mai iba nidai a iya sanina Fulani Zaliha tana cikin oshin lafiya kuma zata haife mana anin Yarima lafiya farinciki ne arara ya bayyana a fuskar Me martaba janyo hannunta yayi ya sumbaceta yace

Allah ya yi miki albarka Maryama ke in ta daban ce saboda haka kike ara birgeni naji dain yadda kika rii an uwanki da zuciya aya kuma kika rie girman da Allah ya ora miki hakan ne yake sa nake tunanin ko bayan raina zuriata zata haa kanta Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce Dole anwar nai wa ya isa ya ja da abin da Mai Martaba yake so ai duk abin da ka nuna kana so har bada ina aunarsaMai Martaba dai yaji sosai yadda take bashi kulawa akan sauran matansa Cikin zuciyarta Fulani Maryam ta ce Da ikon Allah bazai zo duniya lafiya ba mu zuba mu gani

BAYAN WATA UKU

Fulani Zaliha ce durushe tana nauda gefenta Marka ce sai Jakadiya dake rie da ita daga bakin zaure Shamaki ne yake sallama da sauri Jakadiya ta fita gurinsa warya ce da rubutu aciki ya mia mata yana fain Gashi Takawa ya ce a bata ta sha ashafe cikin da shi kara Jakadiya tayi ta koma ciki ta ago kan Fulani Zaliha da ta haa uban gumi a wahalce ta sha bayan ta gama sha aka Shafe cikin da sauran

Bankaa labulen akin akayi ko sallama babu Jakadiya na ago kai tana shirin masifa suka haa ido da Fulani Maryama fuskar nan tata babu annuri wani tunani Fulani Maryama tayi lokaci aya ta sauya yanayin ta cikin ruewa ta ce Jakadiya ashe Fulani na kan gwiwa amma baa turo ansanar mun ba sai yanxu labari ya je mun Jakadiya cikin rawar murya ta ce Ai watoNima zuwa na kenan na fito zanje wajenki Takawa ya ayko da rubutu

Marmushin Markirci Fulani Maryama tayi ta ce Bari nazo na rieta kije ki kawon garwashi yanxun nan ga ragowar turaren da akamun lokacin naudar Yarima Suna haa ido Fulani ta watsawa Jakadiya mugun kallo ba shiri Jakadiya ta fice

Fulani na shiga ta rie Fulani Zaliha tana mata sannu

Jakadiya na kawo wuta Fulani Maryama ta kunce turaren wajen boka ta barbaa baa jima Jariri ya fao yana tsanyara kuka Fulani Zuwaira da Fulani Bilkisu na kawo kai suka ji kukan jariri da sauri Fulani Bilkisu ta ce Lallai mun shigo a saa Barka da arziki suna shigowa kowa yayi turus saboda ganin Abunda Fulani Zulaiha ta haifo sai dai kowannen su haiye abinda ke ransa yayi gudun kar afuskanci halin da Suke ciki

Bayan an yanke mabiyar angyara gun ruwa aka kawo na wankan jariri Kasancewar Fulani Maryama ita yaro ya fao a hannunta ita aka bawa ruwan fakar idanun su tayi ta dami garin gurin boka hae da afar jaririn ta sa acikin ruwan wankan

Lokacin da garin maganin ya garwaye jikin sa wani irin kuka ya fashe da shi amma babu wanda ya kawo komai sai ma tsokarsa da Marka ta ke cikin waa tana fain Ka zama Jarumin maza karka zama rago mana matsoraci bashi zama gwani jinin Aminullahi yafi arfin wasa kyawun an warai ya gaji ubansa

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_
12102021 1942 Ameera Adam FIRST CLASS WRITERS ASSO

ANYA BAIWA CE

Na

AMEERA ADAM

_LITTAFIN NAN NA KUI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI GAME BUATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400 GABAAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT IN FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZAA TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR0706 206 2624 DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_

FREE PAGE 5

Fulani Maryama zuciyarta fes wani shuumin murmushi tayi har ya bayyana a fili ta ce Marka ai ana jarumi ne kamar yadda an uwansa salman yake Jakadiya ce ta fita ta yiwa Sarki albishiri Marka ta fara oarin gyara Fulani Zaliha Har aka gama yiwa Jaririn Fulani Zaliha wanka bai daina tsanyara kuka ba tana gamawa ta gyarashi sannan ta ce Fulani barka da arziki bari na arasa ciki na bar yarima yana bacci kar ya tashi ki samu ki ci abinci ki kwanta ki huta Fulani Zaliha ta ce To na gode Yaya Allah ya huta gajiya Fulani Maryama ta wuce sashenta

Kafin wani lokaci tuni haihuwar Fulani Zaliha ta zaga cikin gidan masarautar sanira bi yake ko ina yana shelar sanar da aruwar da Mai martaba ya samu cikin lokacin anani cikin garin Kano ta samu sakon haihuwar da aka yiwa Sarkin Kano Aminullahi

Jaririn Fulani Zaliha tun ranar da aka haifeshi yayi wannan kukan bai ara wani kuka da arfi yadda wani zai iya ji ba Fulani Zaliha bata kawo komai ba saboda wannan ce haihuwarta ta farko kuma bata taa kawowa ranta komai ba tafi alaanta haka da yaro ne shi mara rigima saboda wasu jariran basu cika rigima ba Matan cikin masarauta da sauran bayi tsegungumi sukeyi akan Fulani Maryama na rashin nuna matsanancin kishinta akan an Fulani Zaliha duk da yadda kowa yasan Fulani Maryama da matsanancin kishi Fulani Zaliha ba ta shan wahalar rainon Jaririnta dukda akwai masu kula dashi amma sam bashi da rigima Tun daga ranar kuma Fulani bata ara takawa ta lea saahen Fulani Zaliha ba har sai da yayi kwana uku da wata yammacin ranar ta shirya cikin shiga ta alfarma irin ta jiaun matan sarakuna tafe take cikin takun asaita da taama kamar ba zata taka asa ba Ga duk wanda yayi arba da Fulani Maryama kallo aya zai mata ya tabbatar da ita in tabbas jinin masarauta ce gaba da baya duk yadda ka kai ga kallan urulla zai yi wuya ku haa ido da ita batare da janye idanuwanka ba kuma duk sanka da ka fahimci a wane yanayi take zaiyi wuya ka fahimci halin da take ciki Tana tafe kunyangarta na biye da ita da Salman a hannu har suka arasa sashen Fulani Zaliha lokacin da ta shiga sashen Fulani Zaliha na zaune tayi kwalliyar ta fito shar da ita ga wani kyau da ta arayi irin na masu jego Fulani Maryama zama tayi kan lallausar shimfiar Fulani Zaliha baiwar ta tsaya daga rumfaDa faraarta Fulani Zaliha ta ce Barka da shigowa Yaya da fatan kin wuni lafiya ya kwanan Yarima Fulani Maryama wani murmushi tayi mai wuyar fasaltuwa ta ce Lafiya kalau masu jego ya kwanan annawa Fulani Zaliha kunya taji bata amsa ba ta walawa baiwarta kira tana bata umarnin kawo Jaririn a fakaice Fulani Maryama take arewa Fulani Zaliha kallo tana ara jin wata irin tsanarta a zuciyarta

Lokacin da aka kawo mata Jaririn karar sa tayi tana murmushi sai dai asan zuciyarta har wani zafi take ji saboda yadda taga kamaninsa dana Mai martaba na ara fitowa a fili ta shafa fuskarsa ta ce A jinjira bawan duniya yana rigima kuwa Fulani Zaliha ta ce Tun kukan farko da yayi bai arayi ba bashi da rigima Fulani Maryama na shirin yin magana taga hawaye na gangarowa daga idanuwansa bue baki yakeyi yana an juya kansa wanda yake nuna yunwa yake ji Fulani Maryama murmushi tayi me sauti ta ce Ai dama bazai yi ba indai ya biyo gida kinsan Yarima ma haka nayi goyonsa ungoshi naga kamar yunwa yake ji a kunyace Fulani Zaliha ta kareshi miewa Fulani Maryama tayi tayi mata sallama zata wuce har ta je bakin ofa ta juyo ta ce Sai fa kinsa ido akansa saboda oyayyun maiya duk yadda kika kai ga ganosu sai kin gaza a masarautar nan dan haka ki bi sannu murmushi Fulani Zaliha tayi ta ce In sha Allah Yaya kinsan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi Fulani Zaliha zuciyarta aya ta fai haka ita kuwa Fulani Maryama juyowa tayi amma sai ta wayence da murmushi auke a fuskarta ta ce Kinyi gaskiya kuma nasan da haka amma duk da haka tsugunne bata are miki ba amma fa shawara ce na baki tana kaiwa nan ta fice daga akin

Tun daga ranar Fulani Maryama bata ara shiga sashen Fulani Zaliha ba kuma zuciyarta fes ta fita daga akin saboda yadda da dukkan alama haanta ya cimma ruwa Shiryeshirye ake ta gudanarwa na shagalin suna daga sassan angarori na cikin masarautar Ranar suna Mai martaba ya raawa Jariri sunan Saifullah suna kiransa da Saif anyi shagali sosai aki daga garuruwa suka kawo ziyara wajen taya Mai Martaba murnar samu a namiji a karo na biyu

Anyi taron suna angama lafiya kuma daga angaren Mejego da jaririnta suna cikin oshin lafiya Bayan wata uku Mai Martaba ne zaune a fada shi da Waziri ga duk wanda ya dubi yanayim Mai Martaba zai fahimci tsantsar damuwar da yake ciki amma da yake namiji ne jajirtacce farat aya bazaka fahimci ainihin yanayin da yake cikin ba Waziri ya uar da kai cikin sigar girmamawa yace Allah ya taimaki takawa ya arawa Sarki lafiya Muna zaune aka aika da saon kiranmu Sarki Aminullah ya jinjina kai sannan ya ce

Waziri wani abu yana damunmu kuma babu wanda muka aminta da mu tattauna dashi sai kai Waziri ya ago yace Wannan haka haka yake Sarki yace Mun lura da yaron wajen Zaliha kamar bashi da wadatacciyar lafiya kuma na lura da yanayin Mahaifiyarsa ita kanta ta fahimci haka sai da tana shakkun sanar dani Waziri ina san maganar nan ta zama sirrin saboda kunnuwa da idanun Fada suna bibiyar halin da ake ciki banasan a fuskanci halin da yaron nan yake ciki inasan ka nemo min mai magani a sirrance ta yadda babu wanda zai fahimci halin da ake ciki

Waziri ya numfasa yace Allah adiran alamanyashau gaskiya akwai matsala babba dukda kasancewar ba shine Yarima ba amma sirrantawar yana da matuar faida A cen garin Zaria akwai wani mai magani dana sani yana bada magunguna sosai dan haka insha Allah zan shirya naje na karo maganin sai a jarraba da ikon Allah zaa dace Mai Martaba yace Waziri me zai hana ya gayyato mana mai magnin ina ganin kamar hakan zaifi Waziri yace Duk yadda kace haka zaa aiwatar da kai da kaya duk mallakar wuya ne Mai Martaba yace A shirya tafiya gobe aje a gayyato mana shi Waziri ya amsa daga nan ya fice daga fadar

Da daddare Fulani Zaliha ce zaune a turakar Sarki ta zuba uban tagumi Sarki Aminullahi ya kalleta yaceMe yake damunki Zaliha idanunta ne suka ciko da walla muryarta na rawa ta ce Mai martaba Saif ne nake lura da yanayinsa bashi da osasshiyar lafiya na lura fa ko gani kamar ba ya yi gashi har yanzu kansa baya tsaiwa hatta irin gwarancin yarannan banji yana yi ba abu aya kawai nasan yanayi idan na kira sunansa zan ga yana an motsawa Fulani Zaliha na kawo nan a zancenta ta rushe da kuka Rungumeta yayi ajikinsa tsam kamar wani zai waceta ya fara rarrashinta yana buga bayanta harta lafa da kukan sannan yace Ina lura da halin da kike ciki kuma na fahimci duk abinda kika gayamun dan haka na aika a kira mai magani a sirrance inasan ki zama jaruma karki bari magauta su ga kukanki Insha Allah Saif zai samu lafiya ki kwantar da hankalinki Haka dai Sarki yayi da lallashin Fulani Zaliha har ta sauko ta daina kuka

Bayan kwana biyu Mai magani suka arasa ta ofar baya suka araso akin sirri wacce take bayan gari Saif na hannun Mai martaba mai maganin ya shigo hannunsa auke da wata jakar fata ta magunguna yana zuwa ya urawa Saif kallo nan take ya fara tsanyara wani irin kuka jinjina kai yayi ya ce Tabbas ancutar da shi da guba mai tsanani sai dai zan iya taimaka muku da yardar Allah koda kuwa bazai warke gabaaya ba Mai maganin kwance jakarsa ya farayi nan take ya dafe irjinsa ya fara wani irin kakari kafin wani lokaci ya yanke jiki ya fai asa matacce

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_
13102021 1853 Ameera Adam FIRST CLASS WRITERS ASSO

ANYA BAIWA CE

Na

AMEERA ADAM

_LITTAFIN NAN NA KUI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI GAME BUATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400 GABAAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT IN FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZAA TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR0706 206 2624 DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_

FREE PAGE 6

Hankali a tashe Waziri da Mai martaba suka kalli juna ganin abinda ya faru da mai magani anin Mai maganin da ke gefe da sauri ya faa kan an uwansa yana kuka Mai Martaba cikin alajabi hae da tashin hankali ya kalli Waziri yace Waziri a ji da bawan Allahn nan bamasan a tara mana jamaa ashirya tafiya asar Zazzau a sirrance batare da wasu sun sani ba zan aiko da takarda akaiwa da iyalansa tare da kyautuka masu yawa Yana gama faa ya juya ya fita ta ofar baya cikin jimami Lokacin da Mai martaba ya arasa cikin turakarsa dare yayi sosai babu komai sai kukan tsuntsaye da ananan dabbobi Fulani Zaliha na tsaye sai safa da marwa take yi da ka ga yanayinta zaka fahimci tana cikin damuwa tana jin motsin Mai Martaba da sauri ta arasa ta tarbeshi gabanta sai fauwa yake tunaninta aya wacce amsa Mai martaba zai bata

Ganin Mai martaba tayi ya shigo cikin shigar da yayi ta adda kama sanye yake da kayan bayi fuskarsa nae da rawani sai Saif dake rungume a irjinsa har kusan gware sukayi da Fulani Zaliha ta an ja da baya tana kallan yanayinsa a hankali ya taka kan lallausar shinfiarsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a hankali Fulani Zaliha zama tayi a gefensa ta ari Saif dake hannun Sarki Aminullah yana shan an yatsansa kallan an nata take zuciya a karye ta ce Allah ya taimakeka har dace ba ko Sarki Aminullah yace Mai maganin Allah yayi masa rasuwa a hargitse ta ago tana kallansa bakinta na rawa ta ce

Mai Martaba azu kace Mai maganin yana akin sirri yana jiranka Sarki Aminullah yace Zaliha lamarin Ubangiji yafi gaban komai yana gabda haa magunguna Allah ya kari rayuwarsa Fulani Zaliha ta jinjina kai ta ce Allah ya fimu sanin dalilin faruwar haka Amma gani nake larurar Saif anya babu sihiri a ciki Kallan da Sarki Aminullah ya yi mata ne yasa ta haiye wani yawu tana sunkuyar da kai asa ta ce

Allah ya huci zuciyar Takawa a gafarceni ban fai haka saboda acin ranka ba Sarki Aminullah yace Zaliha karna ara jin makamanciyar irin wannan maganar daga bakinki kina nufin yafi arfin Ubangiji ya jarrabceshi da wani ciwo ne Karki bari shaian yayi tasiri a zuciyarki har ya kaiga kin fara zargin abinda ba haka bane Fulani Zaliha kukan da take oyewa ne ya wace mata wani irin kuka take me tsuma zuciya Mai martaba jin kukanta yake har cikin zuciyarsa takowa yayi a hankali ya kari Saif ya kwantar da shi sannan ya rungumeta yana lallashinta sai da ya ga ta tsagaita da kukan sannan yace

Zaliha dole na gaya miki gaskiya koda bazata miki dai ba saboda gujewa faawa ga halaka zato a musulunci haramin koda ya kasance gaskiya abinda nake so da ke ki cigaba da kai kukanki gurun Ubangiji shi zai magance mana duk abinda yake damunki karki nufi kowa da sharri sai kiga Allah ya kare ki duk wanda ma ya nufe ki da shi koda yana nasara wata rana mugun abinsa zai koma kansa saboda ramin arya urarre ne Allah ya fimu sanin daidai amma ni bana zargin akwai wanda zai iya cutar da abinda kika haifa a cikin masarautar nan ki rii ibada kamar yadda nasanki da ita Allah zai kawo mana waraka cikin udurarsa Fulani Zaliha goge hawaye tayi tana gyaa kai Sarki Aminullah ya cigaba da kwantar mata da hankali

Fulani Maryama banda zarya babu abinda take yi a soron baya cikin shigarta ta baa kama motsin tafiya taji da sauri ta matsa cen kusurwar bango ta maale kamar ba kowa a gurin Shigowa yayi yana an dubedube murya asaasa yace Allah ya taimakeki da sauri Fulani Maryama ta fito ta ce Ya ake ciki oyayyiyar Fuska Mutumin yayi murmushi mai sauti yace Allah ya taimakeki tabbas kin tabbata murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya tuni ya riga da ya mutu har lahira Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce Lallai ka tabbata lumbulumbu wutar aiayi Mutumin da take kira da oyayyiyar fuska yace Ya gara ta kanyi da dutse Fulani Maryama tayi dariya mai tsauti ta ce Sai kallo kallonma daga nesa suka bushe da dariya lokaci aya Fulani Maryama ta sunkuyo ta ce Kasan idanun Masarauta na lura da shige da fice sai wani lokaci idan mun ara hauwa tana faar haka ta juya fice ta ofar baya

Tun daga ranar Mai martaba ya cigaba da neman masu magani amma wani abun damuwa duk wanda aka auko sai dai ya fai take ya mutu wani kuma a ranar da aka shirya zaa gurinsa zaa je a samu labarin ya mutu ko kuma ya kwanta matsananciyar jinya Tun Mai martaba bai fara damuwa ba har abun ya fara damunsa daga angaren Fulani Zaliha duk ta rame saboda damuwa Sarki Aminullahi tun yana neman masu magunguna a oye har ya fara nema a fili masu magunguna daga sassan garuruwa suke zuwa domin kawo nasu maganin amma babu nasara nasara aya aka samu masu Maganin sun daina mutuwa sai dai idan sunzo babu wani canji da ake samu daga jikin Saif Haka aka dinga tsegungumi a cikin masarautar musamman yadda mutane suka lura da yadda Sarki Aminullahi ya ora soyayya akan Saif Hakan ba aramin atawa Fulani Maryama rai yayi ba da sauran Matan Sarki Aminullah sai dai su basu wani damu sosai ba dan sun san har abada babu shi babu karagar mulki

Haka aka cigaba da tafiya har Saif ya shekara guda a duniya amma ko zama bayayi hatta kwanciya sai Mahaifiyarsa ta juyashi Fulani Zaliha ta riga da ta tabbatar da Saif baya gani sai dai ji da kunne tana yi masa magana take fara jujjuyawa har zuwa wannan lokacin Sarki Aminullah bai osa da nemawa Saif magani ba amma babu wata nasara ko cigaba da ake samu

Jakadiya ce urushe gaban Fulani ta ce Barka da hutawa giwar mata uwar Yarima hasken talakawa an aika kina nemana Fulani Maryama cikin Isa da asaita ta ce Yau zamu kaiwa Marduska ziyara A firgice Jakadiya ta ago tana kallan Fulani Maryama amma ta kasa furta koda kalma aya ne Fulani Maryama ta cigaba da cewa

A yanzu nake san zuwa basai anjima ba bata saurare ta ba ta wuce cikin aki ta auko Yarima Salma ta mia mata tace Zamu je domin biyan buatata ina ara jan kunnenki Jakadiya bakinki anin afarki ina tausaya miki azabar da zan aiwatar miki muddin sirrina ya fito daga bakinki wuri ta mia mata sannan ta fara ambatar kalmomin da Boka Mardusk ya bata ta dinga ambata aduk lokacin da take san ziyartarsa

Durushe suke gaban Boka Marduska ya kalleta sannan ya wage aton bakinsa yana aaka dariya bakyan gani sannan ya ce Maryama buatarki ta biya Kin fito da udurun a juyar da hankalin Sarki daga kan Zaliha da anta Saif ko Fulani Maryama ta gyaa kai Boka Marduska yace Wannan dai ta biya sai dai wata buatar kuma Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce Tsafi ya dafa ka dae kayi arko irin na dabino hatsabibancinka ya dauwama har arshen duniya tana rufe baki ta ire masa jakar kuin da ta taho dasu sannan suka mie zasu tafi har sunje bakin ofa yace Sai dai kiyi hauri Maryama wannan karan makusancinki zamu auka a tukwicinmu lamarin bazai miki dai ba Yana rufe baki ya ace daga gurin gabaaya.

Also Read: Namijin Zuma Hausa Novel Complete

Leave a Comment