Bukukuwan Hausawa

Bukukuwan Hausawa

Awannan shafin mun kawo maku cikakken bayani akan bukukuwan hausawa da ma’anarsu.

  1. Bukin Sallah
  2. Bukin Aure
  3. Bukin Suna
  4. Bukin Nadin Sarauta

1. Bukin Sallah:  Wannan bukine da ake gudanarwa bayan an kare azumin watan ramadan, ko kuma bayan watan sallah babba wato sallar (layya), bayan yafita yakwana goma duk wanda yake musulmine to a wannan ranar zai tafi masallaci domin sallar idi.

2. Bukin Aure: Wannan bukine da ake shiryawa sakamakon wasu masoyan juna guda biyu da suka shirya kansu, kuma suka zabi suyi rayuwa tare kamar yadda addinin musulunci ya umurta, idan komai yakai karshe aka sanya rana idan ranar tazo shine za’a sanya kasaitaccen bukin ‘yan uwa da abokan arziki zasu taru domin tayaku murnar aure da zakuyi tsakaninku.

3. Bukin suna: Wannan bukine da ake shiryawa asakamakon samun karuwa, anyinsane domin nuna farin ciki karuwar da Allah yabayar, ana shirya bukine aranar da abunda aka haifa ya kwana bakwai da haihuwa, ranar za’a taru a kofar gida ko masallaci domin a radawa abinda aka haifa suna, sannan ayankamasa tunkiya, ko rago gwargwadon abunda yasamu.

4. Bukin Nadin Sarauta: Wannan bukine da ake shiryawa domin baiwa wani rikon wani sashe nagari ko anguwa.

Shima mutane sukan tarune domin shaidawa mutane wane shine shugaban al’ummar gari.

Also read:  Ire- Iren Auren Hausawa

2 thoughts on “Bukukuwan Hausawa”

Leave a Comment