Fansar Budurcina Hausa Novel

Fansar Budurcina Hausa Novel

FANSAR BUDURCINA Written by HUMAIRAH MELODY

Bismillahir rahmanir rahim_

Praise be to ALLAH who made me to be alive gain to fill your heart with such a beautiful and interesting novel

NOTE _it is a fiction seems to be like a true life story I didnt do it to curse or abuses somebody I guest if it comes across your life story am apologising I didnt do it bcos of you_

01

Hadari ne gagarumi ya hadu daga gabas da yamma kowa sai gudu yakeyi yana neman inda zai fake tun kafin ruwan su sauko
Cikin kakkanin lokaci ruwan sama mai tarin niima yafara sauka shaaaaaaaa

Dishi Dishi nake hangota acikin hazon ruwan saman Wata matashiyar budurwace ke tafe cikin ruwan tana zubda hawaye iskar dake tashi na kada mata Himar ilahirin suranta duk ya bayyana saboda kashib ruwan datasha
Rike take da zungureran trolley tana janta dakyar a hannunta nake hango wani irin kyankywan kunshi wanda yasha rani yayi jajir abinka ga farar macce sai zanen yafito tsintsa haka zalika kafarta yasha kunshi daganinta kasan amarya ce tafiya take tana dingishi ga dukkan alamu tagaji sosai haka takejan trolley din kamar zata fadi a hakadai harta karasa bakin kofar wani dan karamin mai kyau Tana isa kofar gidan tarar kofar gidan a rufe a hankali tasa hannu tana dukan kofar tana jan nunfashi jikinta sai kyarma yake saboda tsabar sanyin datakeji
Tana jima tana dukan kofar sai cen wasu samari sukafito su biyu ganin dasukayi mata yasa dayan ya zare edo anty ummi lafiya kuwa yafada a tsorace
A hankali ta kutsukai cikin gidan tasaki trolley din a bakin kofar gidan da kyar da iya furta kushigo da jakar nan ciki tana gama fada bata jira sukayi maganaba ta wuce cikin gida tana hawaye
samari suka shigar mata da akwatin cikin gida

Koda tashiga falon mutanen gidansu da wasu sauran yan biki suna zaune a a cikin falon suna breakfast tayi sallama tashiga suduka suke kallonta
Baki bude kowa ya tsaya kallon ikon Allah amaryar da akakai jiyajiya itace a gida yau safe
Sai sallallami akeyi harda ragowan yan biki dabasu tafiba
Ummi naji ankirata dashi
Lafya kika dawo gda
Wani abunne ya faru
Kinyi shuru ummi Kuka ta fashe dashii taki cewa uffan
Aunty ki tsaya mama ta dawo kila ita tafadi mata abunda ya faru

Bayan an idar da ruwan ne mama tadawo
Nidai Humairah ina zaune inajiran inji abunda yake faruwa
mama ummi tadawo gida munyi munyi tagaya mana meyafaru taki ki shigo kila keta gaya miki

Nashiga uku ni Dije meyafaru ummi
Tana ganin mama tace umma ya sakeni dam taji kirjinta ya buga
Ummi laifin me kikayi

Ummi tace Mama kinji na rantse bansan menayi masa ba Wallahi ban saniba ina tashi da safe kawai naga takarda a kan gado ina budewa naga yasa

Ni MUSAB nasaki ummi saki uku aranan sha biyar ga wayan nuwamba 2016

Mama ga takardarda Sauri mama ta amsa ta karanta tace tabbas babu karya amma yaxama dole inje wajen uwarsa inji dalilin da zaisa ya sakeki kwana daya dayin aure
Dasauri mama tazari Hijabi ta Zara sai tafita

Bayan ta isa gidan Koh sallama babu ta shiga mai gadi yana tsaidata koh saurararsa batayiba
Tawuce kai tsaye cikin falom tana fadan Hajiya Fatu Hajiya Fatu
Dasauri hajiya fatu tafita daga daki takaraso falo Lafya kiketa hayaniya hjy Dije acewar hajiya Fatu

Mama tace Inafa lafya
danki yasakomun ya shiyasa nazo inji akanme akan wane dalili kodan batada gata Shiyasa zai watsa mana kasa a Ido kuka mama ta fashe dashi tsabar takaici

Haj fatu tadafe kai ita abin yayi matukar girgizata tadaga edo ta dube sama tace Oh ya Allah ka dubemu da idon rahma bansan a ina wannan Dan ya samo wannan mummunar dabiar ba sannan tasauke edonta kasa tadube mama tace Hajiya kiyi hkr Wallahi banida masaniya akan wannan sabon alamarin amma zan kirashi duk abunda ake ciki zanxo in sanar dake dan Allah kiyi hkuri kitafi muje narakaki
Mama tayi saurin daga mata hannu tana kuka a a basai kin rakaniba tana gama fada Da Sauri ta fita tabar gdan cike da bakin ciki zuciyarta cike da fargabar kilama ya lalata ma yarta BUDURCIN ta domin kuwa shine kadai abinda yakeso

Dedicated to all youth

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH MELODY

Story by
ILILEE

Edited by
Xarah Bukar

02
Tunda haj fatu takirashi a waya take tsaye a falo tana jiran isowarsa ranta yayi matukar baci zuciyarta harwani zafi take mata

Kamar daga sama taji yafara kiranta tundaga waje Ammi Ammi Ammi
Tana jinsa tayi banza dashi saboda wani haushinsa datakeji
Shigowarsa falo yayi anan yayo kicibus da ita a tsaye tana huci musab yace ammi kinanan nake kwalla miki kira kinyi Ignoring dina
Ammi tadaka mishi tsawa dakata Son ta cewa Musab banason jin komai daga bakinka don bakada abun cewa wlh musab kabani kunya meyasa zakamun haka Nayi zaton wuta a makera sai gata a masaka
Me ummi tayima zaka saketane takarasa maganar cikin hargowa
Dasauri takaraso wurinsa cikin bacin rai ta kamo Kwalan rigarsa ta chakumeta tana hawaye tace
Son irin tarbiyan da nayi maka kenan

Musab shikam ko ajikinsa cikin gadara yace Ummi batayimun komaiba Ammi kawai naji banason zama da itane batarai yayi yana gama magana yafirgi rigarsa yafice yabar ta tsaye a tsakiyar falon tana kuka
Batafi minti biyarba taji anyi sallama hakan ya sata dago fuskarta mahaifin musab ne yashigo ganin tana kuka yasa yayi tsaye sororo yana tambaya hajiya lafiya kike kuka
Ammi tace dole inyi kuka musab ya saki matarsa kwana daya dayin aure
wannan ai bacin sunane ace kamanni yaronnan zai watsawa kasa a Ido yar aminina yanzu me kike tunani hjy dije zatace na wulakantata saboda mijinta baya Raye mahaifin Musab ne ke magana cikin karaji

Sannan yakara maganar da kisan sunansa Musab musab

Ammi tace Ina musab yayi gaba dole muyi Abu akai mai gda inba hakaba zaici gaba da zubar mana da kima da mutunci a bainar jamaa
Kwarai hjy maganarki gaskiyane

Hjy dije gda ta wuce inda tasamu ummi tanata kuka
yi hkr daughter karki damu Allah yasa rabuwanki da musab shine mafi alkhairi
Kituna wani Hanin ga Allah baiwane Karkiji komai yata Allah zai kawo miki mijinki anan gaba Wanda saimunce gwamma da akayi
Juyowa ummi tayi tace mama Aduarki a gareni itace mafita kawai kitayani da adua

BAYAN WASU WATANNI

An shafe watanni ba musab ba labarinsa harta gama iddarta
Manema suka fito ciki harda abokin musab
Kwatsam saiga ciki
Abunda ya girgiza hjy Dije kanan
tayi bakin
ciki kwarai amma tayi farin ciki Ummi dake zaune bayan sun dawo daga asibiti wajen gwaji

Mama tace dole ko sunki ko sun so su karbi wannan dan amatsayin fansar budurci shi kadai ya ishi musab da iyayensa ishara barina naje gidan
Nan ta mike tafita

Sallama hjy dije tayi cikin gdansu musab ta kutsa har tsakiyan falo gdan
tace hjy fatu kinyi babbar bakuwa mai babbar sako
Dariya ta sakko tanayi duk boring kunya ya isheta sai wasu yan kame kame takeyi
Inataso inzo inga diyata amma abun sai a slow banda sukuni yau ina Dubai sgobe muna UK shiyasa
Zauna mana ah ah niba zama naxoyiba nazone inyi miki albishir dacewa yata yarku tana dauke da cikin danku Musab harna tsawon wata uku
Amma tace what Ta girgiza sosai

Mama tace Kwarai kina mamakine Toh hjy fatu kidaina mamaki da ikon Allah kinga takardar inyaxo saiki sanar dashi
batajira komai daga bakin Ammi ba ta fita abunta

Kusada ATM din Stanbic dake PZ na hangi motar musab dagani ina cikin layin masu cire kudi
Da Sauri na tsalako wata budurwa naga tayi packing motarta bayan nasa
tasha uban gilashi daganinta kasan tasha Hutu tayi dankam

Layi yana gab da yazo kan musab tace excuse me Dan Allah kayi hkr inci arziki
Am in a heast
Wani irin kallo tayiwa musab ta kashe nasa edo saida ATM dinsa ya fadii

Kuyanga Hausa Novel Complete

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH MELODY

Story by
ILILEE

Edited by
XARAH BUKAR

03

Sannan musab yayi murmushi yace Gaskiya nafi ki kaguwa saidai kibari inci arziki inna cire saiki cire

Toh tace tana taunan cingam Saida yagama tsaf yashiga mota sai a lokacin ya lura da wata mota a bayansa
fitowa yayi yafara masifa wane wawanne ya aje mana mota yasan cewa ATM nazo ba dadewa zanyi ba
Cikin isah da gadara ta fito daga cikin motar tana fadan Nice nan koh dakwai maganane Sai wani muzurai Kake kaman kayiwa sarki karya

Ran musub yabace dasauri ya zufe kofar motarsa yazo gabanta Ke dallah kiyi mun shiru kidauke akwalar motarki kubar wurin nan tun Kafin insa adagaki daga ke har motar taki
Cike da hargowa tanuna masa yatsa Karya kake Dan matsiyata karka kuskura ka rainani don ka ganni a gabanka l Am very expensive as you can see am from a wealthy family

Tun bata karasa maganarba ya kwasa mata wawan mari sannan yace daga yau nidake muzuba saikinyi dakin saniii Niba irin samarin da kika saba yakushi bane kibarsu da tabo
Ni damusane bana jira sannan banida tsoro kuma baidai mace ba saidai namiji Wallahi

Tuni ta shige motar tana kuka takunna tayi wani irin reverse saura kadan ta tsallaka dayan length din

Sai bayan tatafi sannan yashiga motarsa Shima HK ya kunna motar cikin bacin rai amma yarasa meyasa yake ladaman abunda yayi mata

Gida ya wuce direct inda ya taradda Ammi a falo zai wuce tace SON dasauri yace naam Ammi
Dauki wannan takardar ka karanta
Matarda daka aura ka saki tana dauke da ciki
Dam kirjinsa ya buga haba Ammi kwana daya awani ce ciki this is unbelievable In possible wlh Ammi sunaso kawai suyi inheriting wani Abu daga arzikinmu ne kawai amma cikinnan banawa bane
Ammi tadaka masa tsawa dakata karka maidamu kananan mutane kai ka isa kaja hukucin Allah ne
muryan mahaifinsa ya katseshi yana kokarin fitowa daga dakina daman shi yake jira tundaga nesa yake cewa Amma kasan dacewa Kaine kafara saninta a matsayin mace Banga dalilin daxaisa kace ba cikinka bane sannan likitoci sunyi ittifakin cewa mace tana iya daukan ciki daga tagama wankinta
Sannan da gabanin fara aladanta dan haka da nakane yaxama dole ka amsa shuru musab yayi yace naji Abba na amsa amma Ku rikeshi a matsayin danku amma ba danaba yana gama maganar yayi ficewar sa

kulawa ummi tana samu sosai an mallaka mata kudi daga ciki har haihuwa har rainon dan

Da gudu tasauka tashiga tana kuka wata mata nagani buxuwa gashinta har gadon baya ta tsayar da ita dacewa
Lafyarki Ambil kinshigo kina kuka
Kedawa kinje kinyi halin naki na Rashin kunya
Ambil tana kuka tace Yanzu umma harni zai Mara bari Abbana ya dawo Wallahi kodan gdan uban waye sainasa an horamun shi
Umma tarungumeta tace meyasa bakiyimai hkr ba kinsan kowani Dan Adam da irin baiwan da Allah keyimai
Bakisan inda rana zata fadiba kimun alkawari bazaki gayawa Abbanki ba
Nayi miki umma
Amina ta fadi tana cikeda shagwaba

Waye Musab

 

Dedicated to all youth

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH MELODY

Story by
ILILEE

Edited by
XARAH BUKAR

Ina kiraga masoyana ina barar aduarku gobe insha Allah zan fara jarabawa daga mai kaunarku har kullun HUMAIRAH BASHIR Melody
Love you ol

04

Musab Ahmad rufai shine ainihin sunansa da ne daya tilo a wajen mahaifinsa Alhaji Ahmad rufai ya fito daga karamar hukumar Soba LGA shararren Dan kasuwane a central market dake Kaduna ya kware wajen saida gwala gwalai
Yana safara daga Dubai zuwa Nigeria
Mahaifiyarsa hajiya Maryam sunan ta anfi kiranta da Fatu Ammi
Yar asalin garin lere ce tallan fura take kawowa cikin kasuwar soba inda yaganta ya aureta

Ankai ruwa rana saboda yanuwan Alhj Ahmad sunki jinin yan gdansu Ammi
Saboda tsananin bincike saida allura ta tono garma
Shiyasa Ammi batada wani farin jini acikn family din mijinta Musab shine dansu na uku yanada yayye biyu Wanda Allah yayi masu rasuwa sana diyyan gubar feshin gona dasuka Shaka

A yanzu shine dansu Wanda suke masifarso musab dogone black beauty
Gashinsa luf luf kaman Dan India yanada Jan Lebe da idanu wadatattu
Yayi karatun primary a therbow school secondary a ALBANI COLLEGE dake magume Zaria daga bisani yasamu Admission a crescent university Abeokuta bayan ya kammalane yasamu aiki a kamfanin layin MTN

Musab Takadarine na karshe Wanda yayi kaurin suna a cikin birnin Zaria

_Wannan kenan_

Cigaban labari

Tashi tayi tashiga wajen abokiyar zaman umman ta tace Ummu ayman kinga yadda wani ya mareni koh Ammu wai ummata tace inyi hkr kuma gayen inaso akoyamai hankali koya kika gani ummun ayman

Ammu tace kwarai ki gayawa Abbanki inba hakaba gobema karawa zaiyi

Amina tayi tarike hannun ammu tana dariya tace yes shiyasa nake sonki nake kara sonki tana karasa maganar tasaki hannu ammu tatashi ta wuce a guje tana jin dadi Amma takasa kawar da tunanin musab acikin ranta

Bayan tashigo daki tayi zaune gefen gado still tunanin musab ya fado mata a zuci take cewa
Hey was wrong with you Amina Y do you have feelings on that Margot oh no am in for him noo bazansa daddy ya hukuntamun shiba
Itada zuciyarta take zance

Bayan takarasa zancen zucinta Tashi tayi ta fesa wanka wasu kaya tasa shokin gefe a tampha exclusive taji dinki
Komai too match takalmi da jaka da hangles dinta iri daya
Hatta Dan kunnayenta masu kaman Green ne

Keys din mota ta dauka sannan tafito falo anan taci karo da umma
Bayan takarasa wurin umma tace umma zanfita naga gari
Kinsan yau weekend ne dey are alot of fun out there
Umma ta washe baki tohm autana adawo lafiya Amma dan Allah banda tsokana
Amina tace tohm umma sannan tafara taku cike da kasaita harta fita harabar gidan
Motarta tashigo ta kunna tafice tabar gidan akan tati Tuki take ta kure sautin kida waka takeji Wanda saurayin HUMAIRAH ya tsantsara mata Dayake beat din wakan akwai duma hka kaji motar tadau sauti dum dum dum koh horn bataji tafe take cikin motarta kirar Yarix
Go slow ta hada a wajen roundabout din tudun wada nikaina danake Sauri saida na shagala da kallon Amina bare wani da namiji

musab ne ke bayanta gashi bayaso yayi missing tseren dawaki da ake a polo club fitowa yayi a fusace yana masifa yakaraso wurin kofar motar saida ya buga mata glass sannna tabude a daidai lokacin suka hada edo musab yaja tsaki yace Haba dole yar koyoce a cikin motar dole asamu go slow I wonder Wanda ke barinki da mota Wallahi tunda ke yar masu kumban susane sai a hadoki da danjagora

Amina takasa cewa komai kallonsa kawai takeyi cikeda raini tace amma anyi asara kaida kace badai maceba saidai namiji meye na tsayawa kayita kumfar baki akaina Kafin in irga uku ka matsamun inba hakaba intureka inture banza
Dan kauye bakada maraba da dan kauyen soba

Sakin baki kyau yayi yana kallonta azuci yake zancen wannan yarinyar meyasa muke clashing da itane Amma na lura ansangartata da yawa zan koya nata darasii
Shikadai yake zancensa na zuci

 

Dedicated to all youth

 

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH MELODY

Story by
ILILEE

Edited by
XARAH BUKAR

05

Tabbas ran Amina yayi fari kal amma cewa take for goodness sake meyasa nake haduwa da wancan garan ne Nidai cewa nayi na love
Saida suka shafe kusan wata guda basuga junaba hakan yafarune
Saboda Rashin lafya da Musab yakeyi Wanda saida ya kwanta a asibiti

Amina tashiga damuwa kwarai kullun saita fito don taganshi amma shiru kakeji Malam yaci shirwa shima Musab yadamu da rashin ganinta amma Dayake namiji ne bai wani sama kansa damuwaba

Tunda ya kwanta ciwo bakoma samun damar fita
Yau takasance week end hakan yasa yayi wankansa cikin kananun kaya yadauki key na motarsa yafita falo
Anan yaci karo da umma tana zaune tana karatun jarida yakarasa bashin kujera yazaune sannan yagaida bayan amsa ya dube yace Ammi bari nadan zagaya kozan samu fresh air
Ammi ta janye jaridar datake karatu gefe ta dubesa tace kaji shuumi cikin gdan ba fresh air ne kagaNidai nakosa inyi surikata

Kusada ita yaxo yace Ammi karki sawa kanki damuwa very soon
Ammi taji dadi kwarai saboda tana masifar son dan nata ya kara aure

Bayan yafito daga gida yahaura titi zuciyarsa na masa yan sake sake akan amina
Daidai wurin chicken republic dake opposite ecobank na pz ya hangota tana kokarin shiga wurin tabba yaganota
da aauri ya juya kan motarsa yana hangenta ta glass dayake yamma tafara yi gashi yanzu longer nyt muke shorter day

Saida ya daidaici zata fito yashiga da saurinsa ya bangaji ledar Icecream din dake hannunta tuni ta watse a fuskanta cike da masifa tasaka ihu kadan sannan tace What who did dis i guest he must be foolish for committing a crime lyk dis

Musab koh kallon inda take bai ba dayake yasan da gangan yamata

Da sauri tasa hannu ta janyo bayan rigarsa dayake bata gane shiba cike da hargowa tace Malam kai makahone zaka bangaje mutun kawuce batareda kaba mutun hkr ba
After ol bacewa zanyi ka biyani ba don matsayin ka a tip din Dan yatsana yake bakada wannan matsayin Nan taci gaba da masifa kamar wata mahaukaciya kansa yana soke a kasa yaki ko kallonta
saida ta gama tsaf ya dago kansa a lokacin sukayi edo hudu tayi saurin sakinsa harda ja daba ta razana sosai da ganinsa yayi murmushi ganin yadda taja baya yace hmmm inason Sanin wai me sunanki ne ma da duk inda naje saikin biyoni
Amina tadan yi yake cike da takaici sannan tace oh God wani yaxo yatayani jin abun dariya nicema nake binka Shigowa zakayi nikuma fita zanyi cikinmu wake biyo wani nice ko kaine takara maganar da nunashi da yatsa
Musad yayi tsaye yana kallon ta the way yadda take furta lazafi a bakinta yadda bakin ke motsawa tana burgeshi hakan yasa ya tsinci kansa da Kasa kawar da edonsa akan kallonta

Amina me kikazo yi naga dukkin bata jikinki da Icecream wata matashiyar budurwa tafada wanda ga duk kan alamu tare da amina sukazo tayi tsaye tana kallon yadda jikin amina yabace da ice cream

Amina tatabe baki tana kallon musub Kinganshi nan shiya zubarmun dashi Sannan yake cemun wai duk inda yaje Saina biyoshike kanki kansan halina nayi kama da wacce zata dinga bin wannan chakus din
Dariya suka kwashe da ita da Jiddakawarta
Jidda ta yatsayar da dariyarta tana kallon wanda yayi tsaye kamar gunki yana kallonsu tace haba malam inbanda kai abunka ina ruwan biri da hada

Amina tace Tayani gani yar uwa
Jidda ta dube amina tace kawata kodai yana cikine Takarasa maganar tana dariya
Amina tatabe baki Allah shi kiyaye mezanyi da wannan dan kauye jishifa ko wanka bai iya dubi rigar jikinsa awajen yan baro yake siya fah suka bushewa dadariya ita da jidda

 

Dedicated to all youth

 

 

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH MELODY

Story by
ILILEE

Edited by
XARAH BUKAR

06

Musab duk yagama jin kunya yakasa cewa komai Sum sum zai wuce tace ina zaka Kake wani sanda
Dariya suka kwashe dashi harsaida yafara jin haushinsu ya tsaya cak guri daya

Amina tace naga bakasai komaiba tsaya koda snacks ne ka tafi dashi

Mtwzzz musab yaja tsaki yajuyo a fusace yace namiki kamada matsiyaci ne
Dahar zaki siyamun snackYou must be out of your sences ya wuce wurin motarshi

Jidda tace kawata mubishi mukara cika masa ciki suka kara kwashewa dadariya sannan sukabi bynsa har waje motar sukabishi Amina tana cewa oh my dear meye na fushi ai basai matsiyaci ake saiwa Abu baHarda mawadaci mah tayi stiring dinshi

Tayi saurin shiga gabashi tana murmushi tuni Musab yafara Jin kaman ya rungumeta Don jsaiwani shagwaba takeyi Dasauri yariko hannuta yajanyota tadawo daf dashi suna shakar nunfashi juna a hankali yasauke murya yace ina sonki amina

Saida taji kamar anmata sock duk jijiyoyin jikinta suka tsaya tayi tsaye saranda takasa cewa komai
Wani irin lallausan murmushi yasakar mata sannan yasa hannusa cikin aljihu yaciro katinsa sannan yakara janyo hannunta ya damka mata katin duk tana tsaye kamar wata gunki
Zagaywa yayi ta gefenta yawuce batare daya kara cemata uffanba sai bayan yashiga motarsa yatafi sannan jidda tazo ta tabata sai alokacinta zabura tadawo hayyacinta jidda tace ai shikenan karshe fada yazo saiki wuce muje gida nana suka wuce suka shiga mota suka nufi gida

BAYAN KWANA BIYU

soyayya mai karfi ce ta fara samun guri acikin zuciyoyinsu
Inda suka zama tib da taya
Hankalinsu baya kwanciya inhar basuga junaba kowa yagansu saiyayi shaawarsu saidai kash me hali baya fasa halinshi
Sannan baa canzawa tuwo suna
Magana tayi nisa har takaiga ansa musu rana dayake duka family din guda biyukowa ganin kudine
Babu raini

Musab duk ya kosa ranar aurensu yazo
Wata ranan larabane da misalin karfe uku na rana
Amina takaiwa kawarta ziyara wato ummi
Ummi wucewa nazoyi nace bari na biyo yaushe rabo Ance har kinyi aure kinfito Ummi kuma da ciki Amina tafadi cikeda jin tausayin ummi

Amma baida imani Sam Amina meye abun damuwawannan cikin dakike gani
Masifar son sa nake kallonta Amina takeyi tace yanzu cikin nan har wani abun sone Ummi
kwarai ai shine FANSAR BUDURCINA daace bulus yaci yasakeni babu ciki ai ya takaitani
Ya cuceni amma yanxu koh banza nasan zaa kirashi da sunan ubansa

Amina ta jinjina kai tace Kwarai Ummi kinyi gaskiya tabbas daace kin fita babu ciki daya kware ki ya bude ki gal Sannan ya sakeki
Allah ya rabamu da irin wannan auren Amin ummi tace
Sannan amina tacitro katin bikin tamikawa ummi tace yauwa katin bikina na kawo miki shine nace bansaniba Koh zakizo

Ummi takarba tana faraa tace Mezai hana Ai koh ina shiga nake da cikinnan tunda ba shege bane da ubansa
Kwarai kawata ko gaida hjy idan ta dawo Toh zataji
Bayan fitan Amina ne ummi ta bude katinnan sunan data ganineya tsoratata

A firgice tace Musab Shine zai auri Amina Tab lallai dakwai bikin zuwa babu zani
Dole ne inyi duk yadda zanyi in hana afkuwan wannan aure inba hakaba tabbas cutar Amina zaiyi yadda yamun
Muryar hjy dije taji Mamanta ta ruga falo ta tadda yan uwanta duk a zaune
Tace mama Amina wazatta musab zai aura dazu takawo mun invitation card din bikinUmma mamarta kawarkice pls kije ki fada mata cewa Musab mayaudarine

Kul inji hjy ba abunda ya shafeki haka yan gdannan Akanme kika sani ita ya zauna da ita
Toh ina gargadinki bakinki kanin kafarki
Banason jin wata kalma daga bakinki ummi tace toh mama Tun daga ranar taja bakinta tarufe saidai zuciyarta cike da tausayin amina

A KWANA ATASHI
Biki saura sati daya an hada event kala kala yayi inviting friends dinshi
Ya kashe kudi sosai a bikin
Amina koh sai murna takeyi amma mahaifinta bayason wannan aure
Saboda yaji kishin kishin a gari gameda musab Amma dayake Amina sunan mahaifiyarsa gareta kome takeso shiyake mata bayaso yaga bacin ranta don hk nasashi yaji kaman zaibar duniya Dukda ba ita kadai ya haifaba
Musab zaune yake acikin garden din gdansu shida abokinsa Sani gambari
Sani yace Mutumina kakusa zama angogu don banace angoba itama Amina waje zakayi da ita
Musab ya dube sani yace Sani kenan ai andinga kenan harsai naji bana numfashi
Mutumina zata kai ga adaina baka aurefa cewar Sani
Sai inkoma saikuma
yayi Shuru ganin mai aikinsu tace yallaboi ga coffee din

Musab ya kalleta awulakance yace Kinci gdanku da Kofi ubanme ya kawoki Muna fuka toh kisani inhar kika fallasa sirrina saina karar da duka danginki

 

Dedicated to all youths

 

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH MELODY

Story by
ILILEE

Edited by
XARAH BUKAR

Dedicated this humble page to my sweet loving cooling jumping jiggling swixting AYUSHA ILIYASUbunch of love abundantly
You deserve more from me

07

Shiru tayi batace komaiba
Kallon sani yayi yace abokina tashi mu tafi na lura yarinyarnan so take ta batamun tsariiii
Nan suka fita sukabar gidan
Indo kam abun ya dameta azuci tace Wato auri saki yakeyi abunda Allah ya hana
Duk abunda zaimun ya Dade sainaje na fada musu karsu sake su aura mishi yarsu inba hakaba zataje ta dawo
Nidai cewa nayi duk inda takwana Shane

Indo ana gobe biki taje gdansu Amina tasami uwar Amina tace Nazone na gargadeku karku sake Ku aurawa musab yarku auri saki yakeyi Auren dandane
kowa Shuru yayi Amina ta fito tace karya kikeyi
Musab dina bazai aikata hk ba kila dai wasune suka biyaki kudi don kizo ki hanani auren muradina
Kafin in bude idona kifita kibar gdannan
Babu yadda indo batayiba akan du amina su fahimce amma sam son musab ya rufe mata edo haka indo ta hakura tadawo gida
Amina kuwa taci gaba da shirye shirye biki

YAU DAI an daura aure Amina da musab akan sadaki 150

Da misalin karfe hudu na yamma aka wuce RAS akayi lunching
Karfe bakwai akakai Amina gidan musab daya sha kayan more rayuwa
Nidai kayan har tausayi suka bani itakanta Amarya abar tausayi ce

Kowa ya watse ango aka shigo da abokai anata dariya
Misalin goma abokai suka watse
daga Amina sai musab

Bayan musab yaje yarakasu yarufe dukkanin kofofin gidan sannan yadawo daki wurin amaryrsa amina

Kangado yazauna yana murmushi yace my life matso kusa dani mana inji dumin jikinki kinsan cewa ketawace

Amina itama murmushin take tace da dai ka tashi mnje muyi alwala muyi sallah mugodewa Allah daya nuna mana wannan ranar

Yace Toh amma ransa baisoba

Suna idar da sallah kawai yafara rabata da kayan jikinta
Daman a rikice yake
Pls stop it meye hk Amina tace duk ya rude Amma ina tuni yafara sarrafata yadda yakeso har Allah yabashi ikon rabata da kayan Adonta Wato BUDURCINTA

tayi kuka kaman ranta zai fita nidai nace kukama kadan kika gani

Wani bacci ne mai nauyi ya debeta

Washe gari
Tana farkawan taga
Babu musab ba alamansa
Tashi tayi dakyar ta shiga toilet tayi wanka ta gyra kanta
Tayi sallah har tagama Shiru musab bai baidawo ba ta janyo wayarta takirasa wayansa a kashe
Tayi jina Tana tunani kamar daga sama taji ana buga kofa
A hankali tatashi taje ta bude tazace shine saitaga bakon fuska
yallaboi ne yace gashi inbaki yakaeasa maganar yana mika mata wata takarda

Tace toh jiki ba kwari ta amsa ta rufe kofa
Kujera tasamu ta zauna ta bude takaddar abunda ke rubuce acikin takardar ne ya razanata ta kwalla wani uban kara
Tafadi kasa warwas

930am har a lokacin tana kwance a tsakiyar dakin somammiya kwatsam sai tayi baki sukayi bugun kofar sukaji Shuri watace Tayi dabaran bude slide din window taga Amina kwance bata motsi
Nashiga uku meyafaru da Amina gatacan kwance daga karshe balla kofar sukayi
Kanwar mahaifintace tafara daukan takardar taga saki uku Babu kome
Tayi salati ta sanar da ubangiji

Yanzu abunda yaronnan zaiyi mana kenan cin amana
Daman wata mata ana gobe biki tazo tafadii aka maidata mahaukaciya tabbas ga zahiri

Ruwa suka watsa mata suka kira aka taho da mota sai gda
Mahaifinta kam yakasa zaune yakasa tsaye
Amina sai surutai takeyi kaman ta haukace
Musab yanzu ka kyauta kenan Dan Allah musab karkayimun hk
Allah sarki saida kowa yayi mata kuka tayi kuka harna rashin kwatace saida aka hada da adua sannan aka samu tadawo daidai

Bayan sati daya
akaje aka kwashe kaya

duk Ammi batasan wainar da ake toyawa ba saida tayi bakuwa tace Ashe hk Abu yafaru musab yasaki Amina
Zare Ido hjy maryam tayi tace koda bakiji da kyauba
Yanzu ya fita nace ya Amina yacemun tana lafya Ammi mezatayi banda kuka tace shikenan zai bata mana suna a gari
ngd kinji dabaki zoba da a ina zanji
Allah ya shiryamun musab Amin

BAYAN WANI LOKACI

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah saida musab ya auri mata biyar
Amma wasu Sbd kundinsa Dana ubansa suke aurensa
Daman kuda garin kwadayi ake mutuwa
Ammi ta damu kwarai gari sai gulmansu akeyi daga karshe sukayi wani sabon gini shuka koma NAGOYI
Inda bawanda yasansu
Ammi ce kadai kewa musab magana banda abbansa

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH melody

Story by
ILILEE

Edited by
ZARAH BUKAR

08

Kyankywar unguwace wacca ko wanne dan adam zaizo zama cikin
Dayake sabuwar uguwace

Alhaji Ahmad rufai ne zaune yana kallon talabijin Daidai lokacin Da ake sanarda mutuwan mahaifin colonel sambo dasuki
Hankalinsa ya dauku Daidai da shigowan musab
Wucewa yayi unfortunately
Ya bugi wani table karan ne ya dawoda hankalin mahaifinsa

Barka da gda yace amma abba bai daga idonsa akan musab ba wucewa musab zaiyi

Batare da ya juyoba yace Kai dawonan kazauna ba musu musab yadawo
Abban yace yanxu kaxabi ka batamun suna a cikin garinnan koh Kaikenan ka auri mace ka sakaMe ka maida mace Riga yaukasa wannan gobe ka cire wannan Abunda ka maidata kenan Tabbas bakayo halina ba dabaka aikata wani Abu maka mancin wannan ba Amma inaso ka sani saikayi dana sani wata rana saika sa rigar dazata zamema kaya rigarda zatayima wahalan fita

Musab yakasa koh motsi bayan rabon edo babu abinda yake ganim baiyi maganaba yasa Abba yaci gaba dacewe
Sannan nabaka nanda wata biyu kasamo mata wacce zata zamema garkuwa a Rayuwa inba hk ba yafadi tareda tashi tsaye ya nuna musab da Dan yatsa
Zanyima zabi Wanda bakada tsumi bakada dabara Dole ka amsa husna zan aura maka wacce kafi tsana a rayuwarka itace zata zama matarka Fuuuuuu abba ya wuce koh kallonsa baiba a daidai lokacin ammi tafito tun a daki takejin fadan Abba hakan yasa tafito

Take musub yajuy a fusace yana kallon abba
Ganin Ammi yasa ya sassauta fuska

Ammai takaraso wurinsa ita takai cinsa take cike da gara tace tabbas mahaifinka yayi gaskiya nikaina halinda ka dauka Yana damuna
Kasa mutane a gari suna zaginmu da mutunci mu To idan Baccin kake yaka mata kafarka inba hakaba zaa wayi gari agama komai kana bacci Ammi ce take magana ranta abace itama tana gama maganar tafice tabar falon

Musab zaune yake shikadai yarasa abunda ke masa dadii
Amma babu alaman yayi ladamar abubuwan daya aikata Sannan bashida niyyar dainawa
Yanzu ina zanje in nemi aure bayan Abba yace dole sainayi aure nanda wata biyu
Nooo impossible I have to leave to another country before something get spoiled hear
Yanzu wace yarinya zanje in nema a garinnan
I will try my best inkuma nakasa samu yaxama dole ingudu inbar garinnan don baxan taba yarda Abba ya auramun Husnah ba don baxan taba barinta ta hada jiki daniba I hate her

 

Dedicated to all youths

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH Melody

Story by
ILILEE

Edited by

09

Gaskiya yau yasmin garin akwai iska iskan kuma mai dadin gaske
Wallahi kam kawata cewar Yasmin

jiyannan ga rana gashi muka isa bakin gate Aka shanyamu da yaune zama zanyi nasan har bacci sainayi INTISAR ce ke magana cikeda yanga Daidai lokacin suka kawo bakin gate

Bude gate akayi tundaga nesa intisar ce ta hango musab zauna a gefen motarsa
Dasauri tajuyo ta kalli yasmin tace Yasmin juya ki kalli gayen can wlh ya hadu yanada kyau Sosai sainaji inama yazama mijina Intisar tafada tareda marairai cewa Yasmin
Yasmin tasaki baki tana kallonsa tayi jim kamar mai tuna wani abu
Intisar tace bakice komai ba kinyi Shuru

Yasmin tace Inty inaso intuna inda nasan wannan fuskanne kamar nasanshi bara nayi tunani

Shikuwa musab Ganin yadda yan matan suke kallonsa yasa yatashi yanufi cikin motaraTunani Yasmin ta tafi har saida musab yafito da motarsa ya tafiyarsa bata dawoba

Inty takai mata dukan wasa tace Oh Yasmin wane irin tunani kikeyi saikace wacce tayi loosing komai
Kinga harya tafi kinkoga wani irin kallo daya mana ai saida nashiga taitayina

hmmmm Yasmin tace intisar taho mutafi kinsan damabln irin masu kudinnan sun iya rainin wayo
Kallon kowa suke a kaskance Kinsan wannan dakike gani nataba saninshi nasanshi a gyallesu
Wallahi auri saki gareshi

Intisar baki bude tace auren dandane kenan ba malam hudu yace mana Allah ya tsinewa mai auren dandane Kina nufin halinsa kenan inty ta girgiza kai cike Rashin gazgazata maganar yasmin sannan tace Amma gaskiya Yasmin fuskarshi kaman natsatse baiyi kama damasu irin wannan halinba

Yasmin ta harareta tace toh shikenan karki yarda da maganana kedaman haka kike wlh wannan dakike gani Humanizer ne manemin mata
Sannan kwana daya dayin aure zai saki yarinya yace tayi gdansu kenifa kingani hanyannan ma mudaina bi Sbd karyace yanason daya daga cikin mu
Don banaso nazama victim

Intisar tatabe baki cike da rashin yadda da maganar yasmin tace Nikam akan wani kato bazai daina bin wannan hanyarba amma kina ganin cewa wata rana bazaiyi ladaman yin hakaba

Yasmin tace Intisar baida niyyar yin ladama Sbd har kungiya garesu
yan auri saki

Intisar ta zare edo Tirkashi Yasmin Allah yayi mana tsari dashi saikuma intisar ta marairaice fuska tace amma kuma Yasmin nasan cewa inna gaya miki wani Abu zakiji tausayi na Wallahi nakamu dason bawan Allah nan kuma inada niyyan canza mishi duk wani hali nashi amma da taimakonki

Cike da tashin hankali yasmin tace Wa Ni a a kam ai idan kinganni a lahira kaini akayi bani nakai kaina ba mezai sani nashiga harkar wannan mutumen

Hahaha Yasmin kintaba ganin Wanda yakai kanshi lahira
Ai Allah keyiwa kowa ajalinsa Sai mutane sukai mutun kabari subarshi dagashi sai halinshi Intisar tafada tana dariya
Yasmin tayi saurin rike hannunta tace Kinga muyi Sauri karmuyi latti irinna jiya Malam hudu ya jibgemu

Sauri sauri gudu gudu haka sukeyin tafiya saiji sukayi antaka burki Daidai da zasu tsallaka titi Kiiiiiiieeeeeeeeee

 

 

Dedicated to all youths

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH Melody

Story by
ILILEE

Edited by

Juyowan da zasuyi musab suka gani
Da Sauri intisar ta tsugunna muryarta na rawa tace
Dan Allah Malam kayi hkr tuni yaji wani natsuwa har cikin zuciyarshi

Murmushi yamata Tashi karkiji komai nasan ba laifinku bane nawane kuyi maxa karku makara Da gudu intisar ta wuce Yasmin ma tabi bayan ta
Sai gudu sukeyi
Musab kuwa mezaiyi banda dariya
Just take a look ganina duk sun zabura motarsa yashiga yana kallon kyakkyawan fuskar intisar tana dawo mai

A zuci yace Allah ya hadani da hasken idanuwana yau gata karamar yarinya
Sweet sixteen yakarasa zancen zuci tareda shafa kasan gemunsa

Tundaga ranan bai sake ganin intisar ba yakasa cin abinchi yakasa komai
Bashida wani abunyi saina tunani
Office dinma yadaina zuwa

Ammi tana sane daduk wani halin da musab yake ciki Amma tarasa yadda zata bullowa abun

Yau musab yana zaune a falo yana kallon tv amma hankalinsa kwatakwata baya kan kallon fuskar intisar kadai kemasa gizo
Abba yaturo kofar falon yashigo tare da yin sallama ganin musab zaune a falon yasa ya tsuke fuska

Musab yana zaune baimasan da shigowar abba ba sai maganar kawai yaji yana fadan saura kwana ashirin yaragema kafito da wacce kakeso
Inba hakaba my decision take place

Bansan lokacin da na firgita ba saura kiris wayata ta fadii
Sbd wani irin kara danaji musab yayi

Hawaye kawai naga yanayi

A lokacin ammi tafito zata yiwa abba sannu da zuwa a daidai lokacin musab yasaka kara saida ta firgita hankalin Ammi ya tashi ganin halinda danta yake ciki Abba ko kallon ammi baiba dominshi ransa a bace yake ya wuce dakinsa
Ammi tayi tsaye a falon nadan wani lokaci daga bisani kuma takarasa gurin musab zauna tayi kusa dashi ta dafashi tace Son gayamun dalilin damuwanka
Da Sauri yadago yace Ammi zaki iya sharemun hawaye na

Ammi tace Kwarai my son inhar baifi karfina ba Koda dukiyana gaba daya zai kare akanka my Son

Musab yashare hawayensa yana kallon amma yace Ammi dakwai wata yarinya Dana gani nakeso
Amma narasa inda zan ganta kullun ina ganinta zata islamiyya Amma kwana biyu bata ba lbrinta Sai kawarta nake gani
Gashi banaso kawar tasan inason kawarta Sbd nataba ganin yarinyar a gyallesu
Tana yawan zuwa gdan kakanninta
Banaso ta gayawa yarinyar halinda nake ciki

Amma tayi ajiyar zuciya sannan tace Yanzu kana nufin yarinyar tasanka musab ya girgiza kai ammi takara saukw nunfashi tace Karka damu dani dakai zamuyi wannan farautan Sbd muba Abbanka kunya

Masu iya magana sunce hannunka baya rubewa ka yarda
Haka duk lalacewar masa tafi karfin kashin shanu

Umma yanzu haka zamu zauna da yunwa
Kinga kausar yunwa takeji tun daxu take kuka umma intisar tafada tana kallon ummanta

Intisar Yanzu Yakikeso muyi babanku bai dawoba
Kinsan yanzu dakyar zai shigo da kwatan gari yanzu wata yayi nisa masu cefanen wata baa biyasu albashiba kuyi hakuri yadawo sai mugani mezai zo mana dashi

Cikin fuskar tausayi intisar tace hakane umma Allah ya rufa asiri bari naje gdansu Yasmin inji ko sunada tsaki su sammaba
Muyi dantama lele Tana gama fada ta mike tsaye

Umma tace Toh saikin dawo

Tana fita musab ya hangeta daman yanzu kullun yana unguwar yana dakonta ganin gidan data fito a jagule yasa yafara zancen zuci yace daman dakwai mutane acikin wancan gdan
Kuma nan naga tafito
Yana karasa zancen yayi murmushi a Lokaci guda yace abu mai sauki kamar ruwansha zanyi saurin siye iyayenta da abun duniya Wato kudi dunda su talakawane amatse suke

 

Dedicated to all youths

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH Melody

Story by
ILILEE

Edited by

11

Aiko Saina aureki yana karasa maganar yashiga motarsa
Bai zarce koh inaba sai gida yana parking a harabar gidan yafito dasauri yanufi cikin gida yana kwallawa ammi kira
AmmiAmmi
I have a good news for you
Whr are you

Da Sauri ammi tafito daga dakinta
wane irin good news ne wannan musab ammi tafada bayan ta isa wurinsa
Musab yana faraa yace ammi nasamo yarinyar ashe yar talakawace
Ammi taji dadi sosai tace masha Allah yanzu meye mafita
Musab yace yawwa ammi abu nafarko dazan farayi shine na tsaye iyayenta da imanin kafuriwato kudi yanzu Ammi pls kije gdansu yarinyar kiyi musu magana ga kudi kikaimusu
Saboda naga mabukata ne

Ammi tace musab bafa najeba daga baya kasa naji kunya Dan Allah karka bani kunya
Kaba yan uwanka kunya kowa sai gulmanka yakeyi

Musab ya shagwabe fuska kamar wani karamin yaro ohhh ammi karki damu insha Allah wannan itace ta karshe
Ammi tace to shikenan

Yasmin Dan Allah kunada tsaki kusammana Wallahi babanmu baidawo ba
Gashi kausar sai kuka takeyi Intisar tafada tana kallon yesmin

Intisar babu tsaki amma barina baki abinchi kikaimata Yasmin tafada tare da mikewa tashiga kichin tadauko abinci acikin kula takawowa intisar intisar tayi godiya sannan tafita tabar gidan
Akan hanyan ta na dawowa takara cin karo dashi

Tana sauri sauri ta wuce ta wurinsa domin har yanzu tsoronsa takeji musab yace salamu alaikumlokacin dayasha gabanta

Koh kallonsa batayiba cikin hanzari tace Dan Allah Malam kayi hkr kaga in babana yaganni dakai Wallahi yankani zaiyitana karasa maganar tayi banza dashi ta wuce gida

Ammi sallama tayi cikin gdan tace sannunku da Sauri intisar ta ajiye shikafan datake bawa kausar
Tatashi dasauri tana mata sannu tace ga kujera kizauna bayan ta ajiye mata kijerar agabanta

Sannan ta kwala umma kira umma kinyi bakuwa
Umma tana cikin daki tace Toh ganinan zuwa

Bayan umma tafito daga dakin tsaya tana kallo ammi saidai bata waye taba amma saita karaso kusa da ita tazauna Sannu da zuwa akasa umma ta zauna
Ammi tace yawwa sannu ya yara ya sanyi ammi tana kallon gidan ya yatsine tace Kuna kokarin zama a cikin gdannan ga sanyi gashi rufin buhu ne

Umma tace Hjy anata ciki waketa rufi

Ammi tayi ajiyar zuciya sannan tace bawani dogo lokaci nakedashiba daman Nazone da arziki sannan in nemi alfarma ki dakuma ta yarki

Ni Umma tafada cikeda mamaki

Ammi tayi murshi tace Karki damu inaso muzama surukai ne
Yarki intisar nakeso Ku aurawa Dana Wanda shikadaine farincikina yana cikin damuwa akan intisar idan zaku amince bamuso bikin ya dauki wani dogon lokaci inhar intisar zata aminche

 

Dedicated to all youths

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH Melody

Story by
ILILEE

Edited by

12

Ga wannan zan dawo zuwa jibi inji shaawaran dakuka
Yanke
Kudi ta ajiye musu mai tarin yawa don saida umman intisar ta rude har kofar gda ta rakata tayi mata fatan alkhairi

Intisar tana fitowa daga daki ta hangi kudi matsowa tayi kusa da Sauri tace umma waya baki kudi cikin mamaki take magana

Umma tana kirga kudin tace Wancan baiwar Allah nan dakika ga tafita itata ajiye mana wannan kudin

Ihu intisar tayi tace yau akwai bidiri umma zamuci shinkafa da miya

Umma ta katsa mata farin ciki da cewa Intisar inada magana dake kiyimun biyayya insha Allah baxaki taba tagayyara ba

Intisar tayi danyi jim sannan tace umma zan iya komai don ganin farincikin ki
Koda haka zai kasance akasin nawa farin cikin Tafadi tana zubda hawaye tunkafin ummanta tafadi taji abunda hjyarnan data fita tafadi
Suna cikin hakane saiga mahaifinta ya dawo
Fuskarsa cikeda damuwa hannu rabbana yashigo
Kawai tozali yayi da makudan kudi tuni ya wartsake
Samira ina kuka samu makudan kudi hk Nanfa ta gayamai komai dayake iyayene masu kwadayi

Abba yace Ai taxo gdan sauki insha Allah dasun dawo kice ta amince yaro kuma nabashi izinin zuwa zance

Cikeda tausayin kanta tace umma baba zanyi muku komai inhar zanga murmushi acikin fuskanku
banida wani buri saina ganin kuna cikin jin dadii
Allah yasa shine mafi alkhairi a gareni
Tana gama fadi ta tashi ta shiga cikin daki

Allah ka hadani da iyaye kwadayayyu wayanda basa tunanin makomar rayuwata
Amma ba laifinsu bane tabbas na yarda talauci yana daya daga cikin yankin imani
Intisar tabani tausayi kwarai baniba harta mai karatu saiya tausaya mata

Bayan kwana biyu

musab yafara zuwa gdansu intisar nan mutane sukayi cha akai yanzu Malam magaji wannan Dan zaiba yarsa
Wanda kowa yasan cewa auri saki yakeyi
Amma hakan baisa mlm magaji yakaraya ba
koda inty zata je washe gari ta dawo ba komai inhar zanyi ban kwana da talaucihaka kawai malam magaji kefada

Yasmin tayi mamakin labarin daya risketa cewa inty zata auri Musab

Tayi bakin ciki Dan tasan wayanda suka fita
Basusha ba bare ita
Yar ta tsitsiya
Amma Duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka
Mudai yan musha bikine

intisar daman tana masifar sonsa amma sbd halinsa ne yasa ta cireshi a ranta ta gujeshi

Yau musab ne tsaye a gefen motarsa shida inty suna zance

Musab yace My love kinada kyau sosai inasonki ina kaunanki Bantaba jin son wata ya mace ya shiga zuciyana lokaci guda irin yadda sonki ya shigeni ba
Gobe Abbana zasuzo Neman aurenki kuma a gobe zaa sa mana rana
Lokaci guda annurin fuskantaya gushe tuni musab ya rude yace Nashiga uku Nayi laifine wajen fadin hakan

Da Sauri tace ah ah ina farinciki kwarai da wannan albishir dinka
Zan tafi gda sai anjima
Yaro yasamu bayan tafiyanta yace ungo mikama ta cikin gidannan yaron ya wuce da ledoji nikiniki na kayan alatu

A yaune asabar akasa ranan bikinsu sati hudu
Karkuyi komai cewar Ammi data dau son duniya ta daurawa Inty Toh sukace abun duniya baya boyuwa gari ya karade da zancen musab zaiyi aure
Kuma yar karamar yarinya zai aura
Mu abunda munsan komai Wallahi Malam rabe talauci ne yasa mlm magaji aurar da yarsa
Inba talauci ba yasan cewa yaronnan auri saki yakeyi yadauki yarsa yar shekara goma sha takwas aurama Gansanemen yaro sbd kudi Ku tsaya kuji ana biki yau gobe zaku ganta tadawo

 

Dedicated to all youths

 

 

FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH Melody

Story by
ILILEE

Edited by

13

Wacece intisar

Intisar magaji shine sunanta na ainihi
Inda mutane ke kiranta da Inty
Yarinyace kyakkyawa son kowa kin Wanda yarasa
Yarinyace ajin farko mai karatu har ajin karshe takai
Farace amma sbd wahala duk ta dafe

Asalinsu Fulani ne don zan iya cewa haifaffun Nagoyine
Kowa nasu anan yake
Samira shine sunan ummanta
Da kuma Kanninta hudu
Itace ta fari sai usama shine na biyu sai unaisa da kausar itace auta
sbd talauci tundaga makarantar primary Inty bata cigaba ba sai islamiya datake zuwa
Shima nauyinta malam hudu ya dauka

Cigaban labari

Biki saura sati biyu biki umma ta hada yarta babu irin abubuwan gyara daba tayiwa yarta ba
Ita a tunaninta ko matanne basu gyara Kansu shiyasa yake sakinsu

GDA yafara cika har lere da soba akakai goron biki
Wasu sunce Allah ya kiyaye suje bikin da gobe zai sako mata
Kowa da abunda yake fade

Itadai bata damuba danta ne jinintane batada yadda ta iya
Da ikon Allah

Yasmin ce kwance tana dannar wayarta intusar tana gefenta a zaune
Yasmin tadan kauda kanta daga kallon datake ta dube yasmin tace waike bikinki babu party ne

Gaskiya babu cewar intisar kinga walima zanyiYasmin inaso kisamo mun abunda zansha jinin watana yazo Sbd naci damaran zama gdan musab kota hakin kaka

Yasmin ta bushe dadariya tana kallon intisar tace Hahaha kinjiki fa wai kinyi damarar zama gidansa kota halin kaka to idan ya koreki fah Saiki zauna kamar wata Mara yanci

Intisar tasauke nunfashin tace Yasmin insha Allah sainaba marada kunya sainaba kowa mamaki saikuma ankafa tarihi akaina domin insha Allah bazanbar gidan musab baSaina kwatowa duk matan daya aura yanci sai na ansar musu FANSAR BUDURCINSU
Sannan insha Allah maza masuyin haka zasu dawo kan hanya madaidai ciya kedai kawai kisa edo kiga irin nawa aikin Yasmin aduarki nake nema
Sannan maganin nan nakeso Saidai muje chemist mutambaya
Kila mudace
Yasmin tace to muje nan suka tashi suka fita
Tafe suke suna hira wasu yan mata zasu wuce sukace kinganta can kuda garin kwadayi yake mutuwa

Ran Inty yabace tace eh naji kwadayinne Ku maiyasa bakuyi kwadayin ba Kokuma meyasa ya tsalake gdanku yazo gdanmu Toh ahir dinku inba hakaba yanxu zamuba hammata iska yan iska muna fukai dagaku har iyayenku

Dedicated to all youths

 

1121 905 PM 234 806 873 6032 FANSAR
BUDURCINA

Written by
HUMAIRAH Melody

Story by
ILILEE

Edited by

14

Nan dai taci masifarta mai isarta yaran basu kara kulataba
Yasmin taja hannunta suka wuce shagon mummy dake tsakiyan layi Abun murna aunty mummy suka samu sukayi mata magana
Daga bisani tabasu maganin suka wuce

Ana saura kwana biyar biki
Musab yazo yayi musu albishir da cewa an Gina musu gda subar Wanda suke ciki
Daman haya sukeyi a ciki mlm magaji kamar zaiyi fitsari don murna gaba daya ya rude fatansa dai Allah yabar yarsa a gdan mijinta

Komai ansa musu acikin gdan na more Rayuwa yan gulma sai zuwa sukeyi
Akwatina goma aka kawo ciki harda sarkar zinare
Wanda a kiyasin danayi yakai naira dubu Dari hudu da hamsin
Yan kallo sai zuwa akeyi komai na biki musab yayi amarya tasha lalle kaman ba iyaba
Duk Wanda ya kalli intisar Wallahi ya dinga kallonta kenan
Tazama kamar wata zinariya
Koda yake baiki a kirata da Apple of her parents eyes

Ranan biki akayi kaya taccen walima
Wanda yasamu hallatan zaratan abokanan ango
Daganinsu bawanda zakacema na banda
Ango sai sheki yakeyi tuni intisar taji magani yafara aiki daman ta shiryawa zuwanshi
ladies care premium dinta ta siyo don ance zatayi zuban jini sosai
Kallon Yasmin tayi mata signal da Ido daga bisani ta kalli angon nata
Waazi tace ayi mata akan masu auri saki
Ai kuwa malamin ya koro aya an koro hadisi daya bayan daya aka nemi abokan ango aka rasa
Ina abokan naka cikin Rashin gaskiya yace sunada wani meeting ne nima yanxu zan wuce
Zamu dawo daurin aure nanda karfe biyu

Ba musu da Sauri Yasmin tace kinganiko basuda gaskiya hmmm Yasmin kingansu kaman mutanen arziki koh Toh zanyi maganinsu daya bayan daya saisun gane cewa
Na banbanta da sauran mata

Yasmin tace kedai kibini asannu don shafin banfara ba bare in bude Sukayi tafi sukayi dariya sukayi shewa

Yan biki sai zuwa sukeyi Gda yacika yayi dankam

 

Leave a Comment