Cikakken Bayani Akan Ire-Iren Auren Hausawa

Awannan Shafin Mun Kawomaku Cikakken Bayani Akan Ire-Iren Auren Hausawa da  Kuma Ma’anarsu.

Ire-Iren Auren Hausawa

  1. Auren Buta
  2. Auren Bazawara
  3. Auren So
  4. Auren Zumunci
  5. Auren Dole
  6. Auren Sadaka
  7. Lauren Dangana Guwai

1. Auren Buta: wanna aurene da akeyi tsakanin tsoho da tsohuwa wadanda dukkansu sun haura shekaru (70), kuma zasu zauna tare har karshen rayuwarsu.

2. Auren Dole:  Wannan aurene da uwaye keyiwa ‘ya’yansu batare da suna son wanda za’a aura masu ba, wanda uba zai yanke hukuncin yaba wane ‘yarsa ko tanaso ko bataso.

3. Auren So: Wanna aurene da akeyi tsakanin saurayi da budurwa, wadanda zasu fara soyayya awaje har magana ta girma takaima iyayensu, to ananne uwayenshi zasuje wurin uwayen yarinya domin tsayar da maganar aure.

4. Auren Zumunci:  Wannan aurene da ake hadawa tsakanin ‘yan uwa misali dandan wa da diyar kane, zasuyi shawara tsakaninsu yakamata a hada wane da wance aure domin akara zumunta.

5. Auren Bazawara:  Wannan aurene da akeyiwa wadda ta taba aure tafito, kila harma tana da ‘ya’ya inda tabaro to wannan ita ake kira bazawara.

Auren bazawara ya banbanta da auren buduruwa, domin ita buduruwa ana iya mata auren dole amma bazawara kuwa sai ta darje ta zabi son ranta,  kuma zata karbi sadaki idan suka kai karshe da wanda zata aura.

6. Auren Dangana Guwai:  wanna auren shi ake kira (dauki sandarka): Irin wannan aure miji shine zai tare a gidan matar, wato gidan na matar ne amma aciki suke zaune idan suka rabu mijin shine zai barmata gidan ya kwashe kayansa.

Also readBukukuwan Hausawa

1 thought on “Cikakken Bayani Akan Ire-Iren Auren Hausawa”

Leave a Comment