Kuyanga Hausa Novel Complete
Kuyanga Hausa Novel Complete: KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
United we stand and succeed Our ambition is to entertain motivate the mind of readers.
Kuyanga Page 1 to 5
Sarki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwau Anace mata UMMAH
Mebi mata itace Saratu MAMAH sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma FATU akece mata
UMMAH macece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga shaaninta ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawaBayi maxa da Kuyangin gidan da duk wanda ke cin gidan har kishiyoyinta Danta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa yaki dawowa Yasamu guri xan babu kwaba babu harara
Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho dashi
Yayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi zai laluba yadaura masa Aure da koma wacece.
Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake muamula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana raye raye
Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa mesuna RIHANNA wacce duk wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake danshan mintinta tasan takan iya kulawa da da namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware
Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amma ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari yasakeba
Anwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan sarkine me jiran gado
Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn
Sarki Abdallah akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine sarki agarin
Yasan da cewar Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi yahuta acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa rai.
Namijin Duniya Hausa Novel Complete
Sauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa LAMIDO
Ummah bata kaunar FATU da Danta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki
Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya bata dametaba
Kowane da daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi
Amma tun tasowarsu da suka girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa
Lokacin daya isa shiga jamia alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na bata yaro da canza masa halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya yakoyo wasu dabiun
Sarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan nata Turai yakuma gamsu
MAMAH ma bataga laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun
Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai
Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta
Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure yake baya futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita away
Rihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta ta biyoshi ta nemi inda yake
Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn gidan
Ba shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin ma kwana biyu yabata zaitafin
Da tunanin yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukun
Yana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar Alfarma ta sarauta
Bayi maza Da kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu ga Yarima sarkin gobe
Wata KUYANGA Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali dan gyalen data yane kanta ya xame bata saniba
Farace shar gata da hips ga nashanu suncika mata kirji
Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira
Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi
Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi me kikeyi acan
Da rawar murya tace inaina yinShara nakeyi
Yace Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza
Tayi kasa da kai tace ckn rage murya Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin
Yace MAHBUBwanene kuma MAHBUB
Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi
Tace Abokin shawaratane tamu tazo dayashima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi
Ayanda take maganar yabashi Shaawa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu yaga tana motsashi ahankali
Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai
Wani abu yaringa ayyanawa aransa
Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun
Tayi saurin yin kas da kanta don gudun kada suhada idanu
Yace mata meye sunanki
Tace sunana KUYANGA
Yace ke Sunanki nace zaki fadamin na gaskiy KUYANGA ba suna bane aguna wannan kalmar larabcine abangaren hausa kuma ace Baiwa
Tace Sunana ZEENATU
Ya gyada kai kawai yawuceta yana kara ayyana abubuwa ackn ransa
Koda yashiga cikin Dakin Mahaifiyar tasa tararta yayi hadimanta na mata hidima daga me matsa mata kafa ana mata tausa sai meyi mata furfita saikuma masu bare mata ayaba tana karba tanaci
Yana shiga hadiman suka miko tasu gaisuwar xuwa gareshi
Ya amsa da ka
Ta nuna musu kofa tareda alamun sufuta subasu guri
Saida suka futa kana yagyara zama yace UMMAH Barkanki da warhaka
Tayi murmushi Yawwa barkanka Abin faharina yarima Mejiran gado sarkin gobe da yardar Allah
Yayi murmushi yace Uwata maganin kukana yauma gani gabanki nakawo kukana nasan banda matsala tabangarenki zaki sharen hawaye Mai martaba kawai nakeji
Tace fadi ko meyeshi zanmaka zankuma saka ayi maka
Yace Ummah inaso inkoma Turai nagaji da zaman Nigeria niba aiki nake futaba kusan kullum nake gida bana motsa jiki kewa ta dameni kitaimakamin kisa baki me martaba yabarni intafi
Tayi murmushi Angama Yarima yaushe kake son katafin
Yace Jibi nashirya tafiyar
Tace Jibi jibin nan Amma baiyi kusaba kuwa nikaina bason kayi nesa dani nakeba gashi kaida akeso kahaye karaga wataran yaxaayi aga baka xama abaka
Yace kada kidamu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin kokari intafi
Tace kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau
Yayi murmushi yace Yawwa nagode Ummah saidai kuma
yai shiru yana sosa keya
Tace ehefadi mana yakai shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka
Yace ckn rage murya Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU zanso mutafi da ita tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan
Murmushi tayi tace bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke kanada ikon kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama yatake yarinyar
Take yahau kwatantata
Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa dakyawun yanayi tanada kyau nagani afurta
Jin mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya
Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana son akullum tafaranta masa bata son laifinsa
Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake ganinta
Amma baiyi saar ganin kome kamartaba
Tsaki yaja Aransa yace to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita
_Tabdijan muje zuwa_
723 1028 AM Ummi Tandama KUYANGA
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_
United we stand and succeedOur ambition is to entertain motivate the mind of readers
httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation
Nabilancy Luv
Auntyn SS
510
mai Martaba Sarki Abdallah yayi shiru bayan gama jin Bayanan da Ummah Tazo masa dashi natafiyar Anwar Turai
Yakalleta yana murmushi yace Naga alamar yaronnan inmuka ta tashi bazai gyara halin saba Nikam bana sonsa da zaman wajen nan nafisonsa akusa damu domin Aure nake so yayi tunda yakai munzalin Aure ko Lamido yanzun ya isa Aure barantana shi
Ummah tace Aure ai nufin Allah ne baisamu wacce tayi masa bane shiyasa saimu tayashi da Addua kada mutakura masa Tunda can din yafi jindadi gara kabarshin yaje aidebe kewa yakeso yayi
Kina baiwa yaronnan gudummawa naga alamar bakya son yagyaru shiyasa kike daure masa gindi
Ta dafe kirji tacanza fuska
Kamar yaya Nikam walh babu wani daure masa gindi danakeyi kawai bana son yashiga takurane da damuwa Tunda shi bayaro bane da hankalinsa ai ko yana nesa damu bazai lalace ba shiriya fa ta Allah ce Addua kawai yadace muringa binsa dashi
Mai martaba yace Amma dai kinsan bazaki hada halinsa dana Lamido bako Lamido yafishi nutsuwa da hankali harma biyayya da ace Lamidon ne babba dana more
Ta katseshi tana kuka Kawai dai kace kafison Lamido akan shi nikam walh banajin Dadi sai inga kamar kana nunan banbancine kuma komai lalacewar Yarima ai dai shine babba kuma dole shizai zama sarki acan gaba
Yakatseta dacewa Saurara Fulani kinsan dacewa Adalin Sarki me kamun kai shike cancanta da yin sarauta akowace masarauta dan haka dole sai inyarima yakasance da hakan sannan zai mulki garin nan inko bai canzaba to Alumma bazasu soshiba Tunda ko a yanzun sunfara farga da banbancin halayyarsu
Tace To walh koma meye Nikam Bazan taba barin Wani bayan Yarima ya mulki garinnan ba inba shiba dan haka koma meye zaa yi masa shine dai gaba
Yadaga mata hannu ya isa meye na tada hankali da kuka indai wannan maganar mulki ce Allah ketsara komai bamu zamu tsara ba tafiya turai kuma Yaje yaita tafiya Nadaina hanashi tunda bakya so inhana din duk randa yagaji da zuwa yadaina Amma kusan da sani zanbashi mata nan ba dadewa ba
Har zatayi magana kuma saita fasa tunda bazata ari bakin yariman ba tasan halinsa sarai shima bazai so Auran hadiba
Ta mike tafuce batareda ta gaya masa cewar da yar rakiya zai tafiba wannan tafiyar tasan Sarkin bazai bariba
Ana gobe zai tafin Ummah tasa aka kira mata KUYANGA
Koda tazo ckn biyayya ta durkusa gabanta tana jiran umarni domin tayi tsammanin aiki aka kirata tayi
Ummah tace mata Kuyanga Zeenatu ko
Ta daga kai sama
To kifara shiri daga yau gobe zaku tafi turai keda yarima zakijene domin kiringa hidimta masa komai nashi kece basai yace ba indai aikin wahalane kada kibari yayi Har sai ranar da yaga damar dawowa zaku dawo tashi kije
KUYANGA Tace Angama Ranki yadade
Ta mike tafuce daga dakin fulanin
Koda takoma sashinsu zama tayi a inda suke zama da MAHBUB Ta zabga tagumi tashiga tunanin wai itace zataje turai tabdijan lallai zataji dadin Rayuwa zata canza tawaye tunda tashigo gidan sarki tun tana karama bata taba futa wajen gari ba sai gashi abin farin ciki zata keta hazo
TO ABIN BAKIN CIKIN FA wata xuciyar ta tambayeta tare dayi mata tunin abinda zatajeyi turai dakuma tuni da wanda zataje din
Take fuskarta tacanza daga walwala zuwa Damuwa
Zuciyarta tahau bugawa to shin wane irin zama zasuyi Alhalin halinsa bame kyau baneance yana shan giya ance yana neman mata zance ya yadu agidan dan dai ana boyewane kada aji abakin mutum a hukuntashi
Jitayi antabata afurgice tadago kanta saitaga ashe MAHBUB ne abokinta abokin shaawararta
Takalleshi kawai yau babu dariyar datakeyi masa
Yazauna kusa da ita yafahimci akwai damuwa yau kenan
Yacire mata tagumin da tayi yace ZEENAH Haka yake ce mata
Takalleshi akaro na biyu tasunkui dakai
Yace mata meya faru naganki ckn damuwa anyi miki wani abin ne bayan nabarki anan din
Ta dago ahankali tace Bayan barinka nan gurin aka aiko kirana daga Fulani
Koda naje kiran saitake gayamin wai infara shiri gobe Yarima zaiyi koma Turai dani xai tafi domin hidimta masa da koma kuma inmun tafi ba ranar dawowa harsai inyagaji yadawo dankansa.
Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete
MAHBUB yadafe kirjinsa tareda Rintse idanu yana kiran sunan Allah
Tabbas yashiga tashin hankali domin ayau yashiga halin dabai taba shiga ba arayuwarsa tunda yazo duniya
Yana bude idonsa kwalla nabiyo baya yace mata ZEENAH tafiyarki Turai tana daidai da tafiyar farin cikina nackn gidannan Domin kece me deban kewa akoyaushe kuma ke nake kallo nake jin dadi koda ina ckn jin Yunwa ke nake kallo naji nakoshi kinsan da cewa Nadade ina son
Yayi shiru yana goge kwallar datake gudu akuncinsa
Yakalleta ido da ido yace ZEENAH bantaba gaya miki Sirrin zuciyata ba saiyau yauma dole ce zata saka domin naga zakiyi nisa dani Walh ZEENAH zaman da nake dake bana abokantaka bace Na SO Ne zallah dan Allah kisoni koda bazamui Aure ba kice kema kina sona ko naringa tuno kalmar inajin Dadi
KUYANGA Taji wani yarrrajikinta taringajin shigar wani abu tundaga tafin kafarta har zuwa kwanyarta tabbas Tafahimci wannan abun dayake shigarta bakomai bane illah Son MAHBUB ada itakam tadaukeshi aboki amini amma ayau saitaji yanayin yajuye mata da So
Tabbas tana sonsa itama bayama data tuno zasuyiwa juna nisa saitaji xcyrta ta karye hawayen da basu zubo ba saigashi sunxubo ganin nasa ma sunzubo din
Tace ahankali MAHBUB meyasa baka gaya min tuntuniba meyasa kaboye sai yau da muka makarowa juna zaka fada yanzu gashi zanyi maka nisa
Yace Duk nisan da zakiyi indai kina sona to tamkar muna tare ne kedai kitaimaka ki furta min ko naji dadi
Takalleshi tayi murmushi tasadda kanta akasa tace
INA SONKA MAHBUB
yai ajiyar zuciya tareda yin hamdala ga Allah yace nagode naji dadi ki rikemin Alkawari ki rike amana kikuma kula inkun tafi bamu da ikon kanmu ZEENATU akarkashin ikon Sarki da Matansa da YAYANSA muke bamu isa muyi musu da Umarninsu ba sai yadda sukayi damu amma kada kiyi biyayya da aikin zalinci kada kisake acuceki kikasance me addua aduk inda kike kikuma zamo me kamun kai aduk inda kika tsinci kanki domin kada ayi miki cutar da zata karya miki Lagon Rayuwarki
Taja ajiyar zuciyar Zuciyar xuciya tace Naji na amince nakuma gode da Shawararka ya masoyina
Ya mike yace mata maza tashi kije kifara shiri indare yayi kizo muhadu anan dan muyi sallamar karshe
Tayi murmushi tace sallamar karshe kamar wanda xan mutu inmunje can
Yayi murmushi yace ba haka nake nufiba nasan wataqila da sassafe zaku tafi kinga ai zaifi kyau mukadaita mu dade tare mukara yin wata hirar soyayyar ko
Tagyada kai tana dariya
Ya daga mata gira tareda kanne ido yana kallonta
Harya tafi yabar gun bata daina kallon saba tabbas MAHBUB yahadu rashin gata ne da yanayi yasa cikar kamalarsa bata fito ba harsai ankura ido ake hanga atattare dashi
Ta girgiza kai kawai takara gaba tabar gun tayi dakinsu
Tana shiga Taga Aminiyarta ZULAI
Zulaihat tace Hhhmmm inata nemanki ai saikuma nahangoki acan lambun soyayya
KUYANGA Tayi dariya tareda dukan kafadar Zulai tace harkin sakawa gurin zaman namu lambun soyayya lallai Zulaihat ke yar sa ido ce
Ba wani saido gaskiyace ba lambun soyayyar bane
Eh bashi bane to ai ba soyayyar akeba
Cewar KUYANGA Tana dariya
Zulaihat tace kifadawa keya yarinya kowa yafahimceku ingaya miki duk wanda yaga yanda kuke tabbas zaigano ckn mintina batareda yasha wuya ba
Hhhmmm to inma soyayyar akeyi saime Ko bamu daceba
Zulai takama baki tace ho Ni na isa ince baku daceba aji haushina to walh bari kiji kundace da MAHBUB tamkar danjunanku akayoku ina kuma Son tarayyarku
Zama KUYANGA Tayi kusa da ita tace Zulai gobe zanketa hazo fa
Da sauri Zulaihat takalleta da alamar tambaya tace hazo kumakamar yaya
Nan Ta zayyano mata komai nagame da Rakiyar da Zatai wa Yarima Turai
Zulaihat tace wayyo Allah na inama ni aka zaba
KUYANGA Tace tabdijan kenan har wani son tarayya kike yi da Yarimamutumin dakowa yasan halinsa marasa kyau To walh ni ckn bakin ciki nake ahalin yanzu da har aka zabeni
Zulai tace Dan dai zakiyiwa MAHBUB nisa ne amma aikinsan zaki huta zakuma kisami hutu da Aikin gidannan ZEENATU kifa tuna mubayine bayinma kaskantattu wadanda baa san inda iyayanmu sukeba ko suna rayeko sun mace Allah shiyasani mudai muntsinci kanmune agidan nan
Dan Allah kikwantar da hankalinki inkinje domin Allah ne yazabeki domin kihuta kedai kiyi biyayya dama ke me biyayyarce kowa yasani bakida surutu magana bata dame kiba inba sabo kikayi da mutum ba basawa ba hanawa dan haka ki ajiye soyayyar MAHBUB anan zuwa sanda zaki dawo kwacigaba
KUYANGA Tace to inma ban ajiyeba yazanyi bayan askiyazo gaban goshi gobe nefa zantafin dole inyi hkr da komai dama saiyau yabayyana min abinda ke ransa
Zulai tace hhhmmm keda bakida gano abu da wuri aisaiyau kika ji kika gane amma ai kowa yagane manufarku tabbas muna muku fatan Alkairi kedashi
KUYANGA Tace mungode
Nan KUYANGA Tahau shirya kayanta ckn wani Dan akwatin karfe me kyau dashi tana Ninka kaya tana sakawa tana ayyanota A turai shin ko wane Zama zasuyi insunje
muje zuwa fans
723 1028 AM Ummi Tandama KUYANGA
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_
United we stand and succeedOur ambition is to entertain motivate the mind of readers
httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation
Dis Page i Dedicated to My Best friend Hauwau UMMU ALEESHA wa WALEED
Nabilancy Luv
Auntyn SS
1015
Da Sassafe tagama kintsawa misalin Bakwai na safiya Aka aiko kiranta daga Fulani
Tana shiga Sashin Fulanin ta tararta atsaye Yarima na kusa da ita da akwatinsa babba guda daya da alamar zai dade din domin fam yacika akwatin da duk abinda yasan zai bukata duk da acan gidan nasa akwai kayansa na sawa
UMMAH Ta daka masa Yaji ta sa anyo masa dambun nama ta soya masa gyada me gishiri duk abinda tasan dai yana matuqar So ta tanadar masa taxuba masa ckn Akwatin
Yana ganin KUYANGA Da akwatin yahau kallonta fuska ba faraa yace ke wannan akwatin irin na mutanen da kumafa Kina nufin dashi zaki bini Kinsan kuwa Turai Bafa Me dile bace maza jeki canzoshi kokuma kitafi ba kaya inmunje xan nasiya miki wasu kawai
UMMAH tayi murmushi tace Yi mata hakuri Yarima ta canzo kasan sai ahankali kayi mata uzuri taje ta canzo kayan kokuma inshiga innema mata cikin akwatina na
Yahau girgiza kai yana duba agogon hannunsa
Barshi UMMAH saura mintina Jirginmu yatashi saima munyi wuta ahanyar zuwa Airport din don karmu makara
Yakalli KUYANGA Yace ke ajiye kayanki anan muje da najikinki inmunje zansai miki wasu kiringa sanyawa
Ckn ladabi tace to shikenan
Ta ajiye akwatin karfen nata agefe tabi bayansa UMMAH tana musu Adduua da fatan Alkairi
Wasu bayi maza ne suka kai masa akwatin nasa har ckn mota aka zura a boot KUYANGA Ta shige gidan baya
Motar natafiya zata fuce agidan Sarautar saitaji wani iri aranta tabbas zatayi kewar MAHBUB yau ranar zata zamo mata ranar bakin ciki tunda ta taso kullum suna tare gashi yau zasuyiwa juna nisa kamar ance ta dago kanta kuwa tana dagowa takalli bayanta saita hangoshi ta glass yana dago mata hannu
Ta zura hannunta tahau daga masa itama
Ashe Yarima yana hangosu ta mirro amma baiyi maganaba yai shiru
a Airport kuwa da sukaje Dakyar ta iya daga kafa tahau matattakalar jirgi saida ta rintse idonta
Jirine ma yaso kadata Allah yaso ya kula yai saurin rikota tayo luuu jikinsa yatarota yamannata ajikinsa yahau da ita ahankali
Yasan arina tunda yasan ba taba hawa tayiba
Koda suka shiga ckn jirgi akusa da juna suka zauna
Kujerarsa na kusa da tata
Idonta akasa bata iya hada ido dashi don kunyar abinda yafaru da kuma biyayya
Yakalleta yadauke kai yana so yai mata magana amma yarasa me zaice mata don baya son tana jin kunyar nan tasa shikam tana burgeshi amma baya son kunya shi faranse ne wayyayye
Gani yake duk kauyancin nan da zatayi masa bazasu shiryaba domin saiya wayarta kada tabashi kunya irin nayau
Da aka kawo musu abinsha kin dauka tayi saida yadaka mata tsawa
Ke Dauki mana meye na kunyar
Tasa hannu ahankali tadauki lemon taja ta rike takasa budewa
Yana kallonta tagefe taki budewa kanta akas
Saida yashanye kana yakalleta yace kawo inbude miki
Ta mika masa ahankali
Yabude mata na gongwanine me gas
Taringasha ahankali kusan awa guda kafin tagama
Anyi rabin tafiya Tafara bacci takwanto da kanta kan hannun kujera yatsura mata idanu yana kallon kyakykyawar fuskarta da dan bakinta yaji kamar yakai hannunsa yashafata saidai yana gudun kada tafarka
Can bacci yai mata dadi saiga kanta ajikinsa
Yarasa yazaiyi da ita saboda mutane nakusa dasu suna kallonsu
Haka yabasar bai motsaba gudun kada ta farka takasa komawa
Koda suka Sauka a England Kaitsaye suka hau mota ta haya har gidansa
Tamfatsetsen gidane da maimartaba yasiya don kawai insunzo karatu suzo suzauna ackn sa
Daki guda mekyau da tsari yakaita yace mata nanne inda zata ringa kwana
Dayake kayan jikinta riga da zanine tasanya hijabinta hannunta rike da carbi
Tazauna zagwade abakin gado tana so tayi sallah gashi bata san yazatayiba nafarko bata san inane gabas ba gashi Bandakin yawuce tunaninta batasan yanda zata sarrafa ruwa yazubo ba gashi ba agogo adakin
Data gaji da zama saita futo falon domin tambayarsa
Ta dade afalon azaune bayanan yana ciki tajiyoshi yafito daga wanka
Tananan zaune harya kintsa yafito
Yakalleta yace Ya kika baro dakin kika dawo nananan Qalau ko
Tace Dama Alwala zanyi inyi Sallah to bansan yazanyi ruwa yaxubo ba kuma bansan ina zan kalla ba gashi lokaci nakeson gani
Ya koma ciki yadauko mata agogon bango yadawo yace mata Taho muje
Ta biyoshi abaya har dakin da yace natane
Suna shiga ya ajiye mata agogon Akan mirro me lado ladone xata gane shi
Yashige bandakin yana kiranta
Tabi bayansa yaringa nuna mata yanda zata kunna komai takashe ckn Sauki
Da yanda zatayi wanka da shaya dakuma yanda intayi kashi zatayi fuloshin da duk abinda yasan dai zai gagareta
Saida ya tabbatar tagane komai kana suka dawo dakin yanuna mata Gabas sannan yace mata inta idar ta jirashi xaije yasiyo musu abinci yadawo
Kafin yadawo kuwa tagama komai don har wanka itama ta sallo ta maida kayan jikinta taxauna ta takure agado tana jiransa don yunwa takeji
Daya dawo yashigo yakawo mata abincin na take away sannan yabata wata ledar kaya yace Ga kayan sawa nan kala biyar na Siyo miki kafin nakaro miki wasu gaba
Takarba da biyayya tana godiya
Daya fita yabarta tacinye abincin tas tana santi kunnanta kamar yacire
Tayi mamakin ma data iya cin wannan kalar abinci domin a ido dai yaburgeta dama gashi abaka ma gwanin dadi bata taba ganin irinsa ko a hoto ba
Ta wanko hannun tasha ruwa sannan tazo ga Ledar ta zaxxage kayan tana daddagasu daya bayan daya tana mamaki da yatsina fuska domin kayan basuyi mataba
Asalima tayi tsammanin ko canzan leda sukayi da wani domin kayan bana sawar yar musulmi bane
Itakam ko da kudi bazata taba sasu ba rigunan yan bigil suke kanana wanda in an saka zasu damewa mutum jiki
Ga Wanduna pensil ga yan gajerun wanduna sai siket masu roba iya cinya da riguna marasa hannun harda bes tashan iska kayan sunyi kyau
Ga masu sawa Amma
Ta maidasu cikin ledarsu tana mamakin wannan kaya ai baxata taba iya sasuba haba aiko batada kunya wannan kayan sai a gidan mijinta yaushe
Sai bayan wasu awanni yashigo mata don ganin ko qalau take
Yana zuwa yaga kayan akusa da ita yahau tambayarta
Baki bude kayan banenakine fa nasiyo mk yakamata kigwada ma ingani don inga wanda sukafi miki daidai sbd xankoma siya miki irinsu nan gaba
Tace aranta Aiki game kareka
Afili tace kayi hkr nagansu baxan iya Sawa bane sunyi kanana dayawa
Yahade rai baya son kauyanci da Raini fa
Yace akan wane dalili tokisani nanba gida bane baxakiyi kauyan cinnan nakiba dolene kisaka su don awannan garin baruwan wani da wata dankin saka bame kallonki balle yaga laifinki kuma bazaki taba samini wadannan riga da zanin naku nagargajiya ba dan haka maza kisaka su ingani nabaki minti biyar ina jiranki afalo
Yana gama fadin hakan yajuya yafuce
Wani qululun bakin cikine yatsaye axcyr KUYANGA TABBAS tun daga yau tafara nadamar xuwa Turai lallai inko haka zata ringa shigar kayan arna gara bataxoba Gara kuma taita zama dana jikinta
Tasaka kayan agaba tana kallonsu data kalli agogo taga saura minti biyu lokacin daya bata yacika saitayi saurin tashi ta janyo ledar taciro wata riga me karamin hannu tacire ta jikinta tasaka dakyar
Sannan ta sille zanin tasaka wani dogon wando
Bata iya cire dankwalin kayan ba tabarshi akan nata don kada yaga gashinta
Takalli kanta a madubi
Ai dasauri ta rintse idonta tana fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun
Yanzu haka xanje gaban namijiyanzu haka zanje gareshi yagannin nashig uku yau naga takaina meye mafita
Fans kugaya mata mafita
Auntyn Sayyada da Shahida ce
723 1028 AM Ummi Tandama KUYANGA
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_
United we stand and succeedOur ambition is to entertain motivate the mind of readers
httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation
Dis Page i dedicated to my lovely Sister NABILA RABIU LADY a writer of BANI BANE Always i solute you my Namesake oh my Lord bless her and help her everythings
Nabilancy Luv
Auntyn SS
1520
KUYANGA Takara kallon kanta a madubi taga agaskiya bazata iya futa gaban Yarima ahakaba ai taxama mara kunya kenan inhar yaganta ahakanbashi yabaki umarni daki sakaba bashi yakawo miki don ki sakaba Wata zuciyarta tace mata
Azancen gaskiya kayan sun mata kyau domin wandon yamatseta tsam dam Yafito mata da shap sosai abin gwanin burgewa dai
Ga rigar ta kamata tamkar ajikinta aka kirkireta dama ita ba maabociyar saka bra ba saiga nonuwa tsaye tsar Me sifar kan tasa ga nipple nan tsir ya nuna kansa
Ita kanta abin bai mata tsari ba balle kyangani domin sifarta tafito tamkar komai awaje yake
To yata iya inhar taki futa taje gun nasa zaizamo hakan tamkar ta bujirewa maganar sane sannan umarni yabata ba zabi ba
Kuma ita din akan bin umarninsa take zaune sannan babu musu ko kiwa atsakaninsu akullum ita din baiwa ce makaskanciya agunsa KUYANGA me hidimta masa
Ta tuno kalaman mahaifiyarsa da take ce mata DUK ABINDA YA UMARCEKI DAKIYI KIYI MASA DONKI FARANTA MASA KECE MEYI MASA KOMAI ME KULA DA KOMAI NASA
Saikuma ta tuno da kalaman masoyinta MAHBUB da yake ce mata KADA KIBARI AZALINCEKI KADA KIBARI ACUCEKI SBD KINA AMATSAYIN BAIWA KADA KIYI ABINDA BAI DACEBA ACKN BIYAYYA
ta rintse idanu tana kwalla tana fadin MAHBUB kayi hkr gashi anfara zankuma karya maka doka Zanyi biyayya ga abinda bai daceba zanbi umarnin uban dakina
Tana gama fadin hakan tafuce gurinsa
Yana zaune afalon yadora kafa daya kan daya yana latsa waya
Tun daga nesa yakura mata idanu itako kanta na kasa
Saida ta isa dab dashi tadago kanta taga ashe shidin ita yake kallo saiTaji wata kunya ta mamayeta
Yai saurin kawar da ganinsa daga kanta yace Very nice sunyi mk kayan daga yau sune Kayan sawarki kada nakara ganinki da zani domin nanba kauye bane ina muamula da wayayyu bazanso suga dawa nake tareba inhar ba kin kile ba tunda duk bakon danayi saikinzo kinyi masa hidima
Ta gyada kai kawai
Yace oya muje kicin na nunnuna miki kayan amfanin da zaki ringayi akullum
Ya wuce gaba tabi bayansa adarare
Yaringa nuna mata abubuwa komai har gas yanuna mata yanda zatayi amfani dashi domin acan gidan sarauta Manyan bayi ke girki ba yaransuba
Balle su iya komai su kananan Bayi saisun kai munzalin Aure ake fara Trenasu
Saida yaga ta kwashe akwanyarta na wasu abubuwan kana yace suje su zaga gidan domin can ma akwai abinda zai nunnuna matan
Tana gaba yana bayanta yana karewa mazaunanta kallo
Yawu yake hadiya kawai domin yasha Mamaki aransa yarinyar ta da ita amma komai yaji
Yakaita gurin shukoki don yace ita yakeso taringa basu ruwa kana yakaita gaiding nanma yace hurumin tane
Cai ashe zaki wahala KUYANGA
Yakaita yanunata ga mai gadinsa domin su san juna sosai tunda ita zata dawo girkin gidan zata ringa bashi shima
Au ainaxaci gadinma ita zatayi
Kwanan KUYANGA Biyar agidan takwashe komai akwakwalwarta ta iya kunna gas tayi masa sassaukan girki takan mikawa me gadi intayi
Girkinsa bai wuce indomie Cuscus da suyar dankali da doya da kwai sai sauran abubuwan da basuda nauyi masu Saukin yi
Dan wahala shiyasa bakada kiba
iyakarta dakinta in yana falo bata yarda tafito inba abinci zata kai masaba shima a kunyace take zuwa sbd kare mata kallo yakeyi duk kayan kuma data sanya saiya furta cewar sun mata kyau
Magana me tsayi bata hada su to me zatace masa Bayaga ina kwana ina wuni sai tambayar wani abun kuma
Cikin Sati biyu yazamto tafara sabo da komai hatta kayan datake sawa matsatstsu yazame mata jiki tasaba dasu tunda yakaro mata wasu yakawo mata dayawa
Tun tana kunya inta sakasu harta daina
Yakawo mata manshawa masu kyau da man wanke kai da sabulai nagyaran fata dai
Tana tsafta sosai tana gyara kanta dayake tanada tsahon gashi da cika saidai kullum yasha gyara ko tayi masa manyan kalba ta bazo jelar kalbar baya aiko takanyi balain kyau dama ga fuska kamar ba india sosai kyanta yanata bayyana don hutu yanata shigarta ba koina take zuwa ba kullum bacci daga dakinta sai kicin sai falo
Sai intafuta kaiwa me gadi abinci ko aikin farfajiya
Zaman gidan yafara damunta to amma bayanda zatayi tunda baice tazo tafuta wajenba aibaxata iya futa batare da izinin saba
Yakan futa tun dare sai tsakar dare yadawo tarasa wane aikine haka kamar na barayi
Hhhh bakisan club yake zuwa ba kenan to zauna wataran zaki sani
wata ranar Lahadi tana Daki akwance tayi rub daciki tanata tunanin masoyinta MAHBUB Tasan akoina yake yanzun hakan yananan da kewarta
Kawai taji yashigo mata ba sallama
Ta tashi da sauri tace Sannu dashigowa akwai abinda kake bukatane
Yaja yatsaya yaruke murkar kofa yace kitaso maza kidafa abinci ga bakina nan zuwa gidannan yan Nigeriane amma anan suke karatu Abokina ne sosai Shi din Jinin Sarautane kitsaya kinitsu kiyi abinci me dadi bawai bamuda inda zamu ciyo bane akwai hotels kawai dai yafison abincin gidane nasan sa sarai
Ckn ladabi kai akasa tace to angama
Yajuya yafuta yana karewa yar shimin dake jikinta kallo wanda agaban rigar aka rubuta HOT KISS Da manyan Harufa
adaidai lokacin da bakin nasa sukazo adaidai lokacin Allah yabata saa tagama komai
Har juice ta hada na mango da Banana da kayan fruit dai
dayake yakawo komai yasaka afurji
Itako akwai basirar iya yin komai wani abunma ba koya tayiba datayi nazari aranta tsaf zata hada
Tab kaga KUYANGA YAR Baiwa ho Allah yabamu yataki zeenatu
Tayi musu sallama falon yarimane sai bakin su biyu kawai kallo suke suna hira
Bakin suka bita da kallo
Ta dire akan table tareda durkusawa tagaidasu
Yarima yana kallon yanda suketa kallonta
Saida takoma ciki Yarima yakaiwa nakusa dashi duka yana fadin kai SAHABI kashiga hankalinka wannan kallo haka na miyene
Wanda aka kira da SAHABIN yakyalkyale da dariya yace yo mutumina ai abu nagani kamar Zinare agidanka tabbas inhar zai dauku saina daukeshi
Yarima yasake kai masa bugu
dan ubanka wannan ba kalar taku bace kafi karfinta KUYANGA Ce fa da ita nataho ita tadabance ackn BAYIN ma
SAHABI yace kai anya kuwa zanyarda da batunka ace wannan KUYANGA CE tabbas ackn kuyangun ma ta dabance kaga halitta fa ga kyau ga cikar halitta Ga kuma
Yarima yarufe masa baki yana fadin basaika karasaba abar maganar akoma wata wannan munwuce ajinta
SAHABI YACE kaga yarima kabarni nikam wannan tayimin ta furgitani dayawa domin ko ackn KUYANGIN gidanmu bantaba ganin mekyau irinta ba
ASHRAF da sukazo tare ya bushe da dariya yace Kai SAHABI kadai tafi dayawane Plz cool your mine kada kafara ma you are handsome and gentle fa karike girmanka dai
Yarima yace yama fara mana nikam dai bazan yardaba badani a wannan abin kunyarba domin yafi karfin ajinta shima yasani
SAHABI YACE Kai yarima bangane bafa kodai dama kaine aciki
Yarima yaja wani mugun tsaki yace Allah yakiyaye niko mezan da wannan kamanta nine ko a mata cikakku ba kowacce nake kulawa ba balle ackn Bayin gidanmu haba Abokina Me Yarima irina zaiyi da KUYANGA
Yahau bude abincin Duk Dan abar maganar yana fadin Kufara cin abinci tukunna dai
Anyi haka da kwana guda yacimmata har daki yace mata Ke Daga yau inhar kinjini da baki kidaina Saka kananun kayan dana kawo miki
Tace to amma babu wasu dazansaka sai wanda mukazo dasu kuma sun tsufa
Yace bakomai kisasu ahakan inzaki fito gun bakina kafin asan abinyi
Ckn ladabi ta gyada kanta alamun xatabi umarnin
Ammafa ta dade tana tambayar kanta shin ko meyasa yace mata hakan Toko tayi ba daidaiba ko sunyi maganar dasu akanbai dace bane Dayake dai batada Amsar tambayar sai muje zuwa
Auntyn Sayyada da Shahida ce
724 815 PM Ummi Tandama KUYANGA
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_
United we stand and succeedOur ambition is to entertain motivate the mind of readers
httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation
NABILANCY LUV
Auntyn SS
2025
Ranar wata lahadi Tana mopping a falo daga ita sai 3quater da body hug me karamin hannu kanta da kallabi bata taba yarda tabar kanta abude ba sbd akullum lokacin tana gida sai MAHBUB Yahaneta da hakan
Wakarta takeyi ahankali tana Dan motsa kafada
SAI WATARANA MASOYI ZANBARKA SAI WATA RANA INA MAKA BANKWANA _bankwana_
ASHE SABO YANADA DADI AMMA IN ZAAI RABO DA ZAFI MAHBUB NATAFI NABARKABANSAN HALIN DA KASHIGE CIKI BA _Bankwana_
tahau goge hawaye domin wata kewar MAHBUB ce tazo mata shiyasa take masa waqa
Ashe duk abinda takeyi Yarima yashigo yana bayanta yajingina da bango yana kare mata kallo ga muryarta ta masa dadi ga shigar da tayi ta fusgeshi domin wata shaawarta ne yashigeshi lokaci guda
Saida tagama tajuyo zata bar gurin da tsumma da mofa ahannunta kawai taja tunga kanta akasa tana masa barka da shigowa wata kunyace ta lullubeta domin tasan yaji irin waqar da takeyi
Yayi gyaran murya bayan amsa mata da yayi yace mata kishirya anjima zaki rakani wata unguwa
Ta gyada kai tana amsawa da to
Tagama shirinta ckin wata doguwar riga daya hado mata dasu ckn kaya da siririn mayafi
Tayi kyau ainun tamkar balarabiya tafuto sak
Yaleko yace ta futo sutafi
Takwas ta wuce alokacin
wani Store suka fara zuwa ROYAL STAR
Yajibgo kaya aleda yabata tarike suka fito
Yakarbi kayan yasaka a boot
Tashiga gidan gaba
Yaleka fuska ba faraa yace mata futo kishiga gaba niba Drivern ki bane
Ta futo sum sum tashige gaba domin itakam kunyar rabarsa takeji tanajin nauyinsa tafi son bayan domin tana shiga takura takuma fi son taringa nesanta dashi
Suna tafe suna saurarar wakar Nancy Ajram ackn motar daya kunna yana son wakokinta sosai
Yakatse shirun da watso mata tambaya
Zeenatu Wanene MAHBUB ne Kuma meye alakarki dashi
Tahau sinne kai ahannunta tana in inar magana
yace mata alamu sun nuna masoyin kine kenan
tayi masa shiru fuskarta dauke da murmushi
Yace Amatsayinki na KUYANGA Meye ribarki in kika Auri BAWA
ranta taji ba dadi kalmar batayi mata dadiba tunda aiduk mutanene kuma Allah ne yayo KUYANGA yayi BAWAN
Dayaga batada niyyar magana saiyaci gaba
Wato nafuskanci kina cikin soyayya kuma kina ckn kewarsa ko Inban mantaba naganki aranar da zamu baro gida kina daga masa hannu
Anyi hakan
Ta daga kanta
Ya daga kafada yace Well Zancire miki kewarsa domin kiji farin ciki ayau
Itakam bata ce kanzil ba domin bata fahimce shiba sam
Kaji sokuwa hhhmmm muko fans mungane
dayaga taki cewa komai saiyace Zan baki farin cikin da Saurayin naki yake baki domin farin cikinkiTa dago da sauri tasadda kanta akasa ckn mintina kwakwalwarta tahau aiki to me yake nufi kenan soyayya zaiyi da ita
Bawai zamuyi soyayyar da kukeyi dashi bane zandai ringa debe miki kewarsa da baki jin dadi
Gabanta yaringa bugawa ina sambazata iya ba yana ubangidan nataba da itaba
Dayaga batada niyyar magana dai saiyakyaleta yaci gaba da tukinsa yana kallon waje yana kiyasta tayanda zaibi da ita don da alamar zatayi duhun kai awannan harkar
Saida yabiya da ita ta club dinsu
Ya ajiyeta agefe yace tajirashi
Taita kallon mata da maza anata cakudedeniya ana ta shan giya da masu shan sigari
Saikaga mace acinyar namiji suna manne ana tsotse tsotse ba ruwan wani da wani acan gefe guda wasu sunata rawarsuanne ajikin samarinsu wasu acan kan filo ana dance
Abin mamaki yabata duk da kasar masu jan kunnece akwai musulmai bakake agun kuma har dasu ake wannan harka
Daga nesa ta hangoshi da wata mace yana mata kiss agoshi sannan ta rumgumeshi suka rabu tana dago masa hannu
Kafin yakaraso gunta saiga wani bature dufagabanta ya tsaya dab da ita yana mata magana da harshen turanci
To dayake bawani ji take sosai ba don kadan kadan takejin turanci tsintar binda baa rasaba takeyi daman tunda ana musu daraci da islamiyya da bangaren koyarda harshen turancin duk ackn gidan Sarkin
Ta juyar da kanta
Aiko dai wannan bature yai gangancin kama hannunta yana mata faraa
Yarima na zuwa ya fuske hannun nata sannan ya wanke baturen da mari
A furgice baturen ya ranta ana kare domin yai tunanin ko mijin tane yadawo gunta
Tashige motar da sauri gabanta na dukan uku uku
Saida suka fara tafiya sannan yace mata ke bakida hankali zaki kulashi dahar zai rike miki hannu
Tace ahankali bansan yaxo gunba walh kuma kafin inyi masa magana yarikoni
Yaja tsaki kawai ransa na msa quna baisan daliliba
Amaimaikon yawuce gida saiya nufi wani makeken hotel da ita
Saida yakama daki sannan yace ta biyoshi
Yabude dakin da key wanda ke a saman hawa na biyu
Dakin babbane daya jal amma ahakan VIP ne domin yakawatu yaji kayan alatu ga komai nan daka danna wata tarho maaikata zasu iso maka da gaggawa
Gadone makeke da mayan kujeru adakin duk sunciye ga furji da toilet ack
Ya kwanta akan gadon yana nishi waishinan yagama gajiya
Ta zauna akan kujera tana kallonsa
Yakalleta da ido guda yace
Zoki daddanna min jikina
Ta mike ahankali ta tsaya akansa
Yacire kayan jikinsa dagashi sai gajeran wando da bes
Hankalinta yadaga ganinsa ahaka tunda take bata taba ganin halittar namiji abayyane ba saiyau domin yar bes dinma cireta yayi
Tayi kas da kanta gabanta na faduwa domin jikin yarima na dabanne akwai gargasa ga kwanji ga cikar halitta
Ya janyota kan gadon yana fadin
Matso sosai kiyi min tausa bacci xanyi
Batace komaiba tahau yi masa cikin biyayya ba musu
Yalumshe idonsa wani magana disu na shigarsa
Tabbas abubuwa sun gama motsa masa babu abinda zai hanashi jin dadi ayau dama tun dawowarsa Kasar sau daya yayi da wata baby Rihanna tayi tafiya karuwar tasa
Tuni yabirkitota jikinsa yana neman zille mata rigar jikinta
Gabantane yaci gaba da bugawa tana addua ckn ranta domin dai tasan tashiga hannu babu me kwatarta sai Allah sannan bata isa tayi masa musun komai ba ayau sai alokacin ta tuno kalamansa na ckn mota wato nufinsa zaisha mintinta amma ba soyayya zaiyi da ita ba
To ai ita gara suyi soyayyar yabar mata mutuncinta
Hawaye taji zai taho mata tayi saurin mayar dasu don kada yagani yazaci zata bujire masane
Itako kanta take tausayi ayau tasan batada mafita sai Allah
tabdijan Fans akawo mata taimako
724 816 PM Ummi Tandama KUYANGA
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_
United we stand and succeedOur ambition is to entertain motivate the mind of readers
httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation
Wannan Page Sadaukarwane kyauta sukutum ga Takwara takaina wato NABILA DIKKO marubuciyar DANGIN MIJI _ina jinjina miki inayinki irin Sosai dinnan Alherin Allah yakai inda kike yakuma kawo mana Daukaka da tsari mu 4 Stars Writers_
Nabilancy Luv
Auntyn SS
2530
Tanajinsa ya hau sille mata kaya tareda shafata ahankali salo salo Yahau shinshinarta kamar wani kare ko mage
Itako tayi lakwas ranta baya so amma takasa motsawa don gudun bata masa
Yaringa wasa da sassasan jikinta axuciyarta addua kawai takeyi akan Allah yakawo mata dauki
Harya cire wandan jikinsa kuma sai yaji wata Izza tashigeshi yaji aikwata kwata bai dace yakusanci baiwarsaba domin hakan zai iya kawo masa ragin Aji
Ya turarta gefe tareda tashi da sauri yahau zira kaya yana fadin maza tashi kisaka kayanki mutafi
Ckn Sanyin jiki ta mike ta fara maida kayanta ajiki tana godiy ga Allah daya kubutarta
Koda suka baro hotel dinnan kai tsaye gida yamayarta
Da dare saida yadawo Club yasami mata yazaba ciki tareda diddikar giya son ransa yasha yayi tatil sannan yakebe da mata
Bai dawo gidanba saida tasakeshi giyar Wajen 4 na asuba yadawo
Duk bidirin da yakeyi nafutar dare da yawon dare bata ramfo abinda yake fita yiba Duk azatonta ko wani aikin yake futayi tunda bata sanin lokacin dawowarsa
Da Safiyar wata jumaa Yarisketa akicin tana kokarin dora masa abin kari
Yayi gyaran murya tayi saurin juyowa
Ta durkusa ta gaidashi ya amsa fuskarsa ba faraa
Yace mata kishiga kigayara min dakina Kitabbatar kingyara minshi tsaf domin yayi kura goge koina Domin Bakuwa zanyi
Ta gyada kai tana fadin angama Ranka yadade
Yafuce yabarta tana ci gaba da abinda takeyi
Aranar ta wuni aikin gyaran dakin nasa bata taba shiga ba sai ranar
Duk yanda yake kwalliya da kwalisa da izza da dagawa irin na Jinin Sarauta amma dakinsa cikin datti yake gado kawai yake hayewa yakwanta tun xuwansu duk da satinsu biyu baisa ta shareba saiyau
Damasu maza aisai a slow sungaji hakan
Saita hau tunanin ko wacece hakan da zatazo lallai tanada babban matsayi agunsa tunda har asbd ita akeyin gyaran dakin
Ta goge koina ta gyara dakin tsaf tafeshi da Air freshner me dadin kamshin Splash
Harta juya zata futa kuma saitayi tunanin mezaisa bazata bude dan furjin data gani adakinba ko shima cknsa zaibukaci gyara
Tadawo da baya ta budeshi
Aiko wani wari yabugi hancinta
Tayi saurin toshe hanci
Kwalabe tagani wanda bata fahimci kona meye ba
Saida tahau fito dasu tana dubawa tafara gano kona meye
A iya fahimtarta kwalaben giyane taga anrubuta
WISKY da manyan harufa sai wasu datagani sunfi yawa agun anrubuta ORIGINAL ALCOHOL
Tahau gyada kai tabbas giyace
Ta maidasu inda suke ashiryensu
Takama baki tana mamaki da zancen xuci
Yanzu dama giyar da aketa cewa yana sha da gaskene Lallai wannan ya iya takunsa Allah yashiryaka
Ta mike tsam tafuta abinta
Sai dare yadawo gidan amma bashi kadai tajiyoshiba
Ta fito da sanda tarabe a wata siririyar hanyar dazata sadaka da falo ta hanyar dakinta tana hangensa yashigo shida wata siririyar baturiya da kananun kaya ajikinta sunshige dakinsa
Ta tsaya kem agun tana Allah wadaransa Aranta domin yarima dai ba hali ga bin mata ga shan giya tabbas Duk wacce ta Aureshi batayi dace da uban yayaba Sarkinsu adali me kyan hali Allah yajarabcesu da Da mara kyakykawar zuciya
Takoma daki abinta tana tuno masoyinta MAHBUB ko yaushe Allah zaiyi komawarsu gida taganshi
Da safe tagama abin kari takai musu daining table Dankalin turawa ta soya da kwai sai shayi dayasha kayan hadi data dafa taxuba a flask
Takoma daki abinta
Basu fitoba sai karfe 11 daya suka fito tana rike dashi ajikinta
Tare suka ciyar da juna tana bashi abaki yana bata
Rihannah kyakykyawar baturiyace wacce itace mace kadai dayafi so tafi kuma gamsar dashi
Tasan salo salo da luggar gamsar da namiji
Macece me tsananin kishin tsiya saita kashe mutum akan kishi
Tunda suka fuce basu dawo ba sai dare daga yawon su
Yatarta da KUYANGA adakinta tana bacci
Yabubbuga mata kafa ta farka afurgice ta tashizaune tana mitstsika idanu
Yace mata nazone don inja miki kunne akan kada ki sake kiringa futowa alokacin da kikasan bakuwata na nan banason taganki zamu iya samun matsala da ita
Tayi saurin gyada masa kai
Yajuya yafuta yana waiwayenta domin tayi masa kyau ga surarta tar wacce yake tsananin kwadayi ckn wasu kananan kaya
Duk yadda yake gudun RIHANNAH kada taga kuyanga saida aka sami akasi taganta domin kwananta uku agidan akai kicibus a falo
Tafito tabaroshi adakin xatayi kallo ita kuma KUYANGA Tafito Zata dauki Abinta akicin kuma dole saita sada kanta ta falon tunda dakinta atsakiyar falon yake yana kallon nashi
Kallon kallo aka hauyi
Ita KUYANGA Ba damar yin magana gashi gabanta na dukan uku uku tana ganin tasaba doka gashi Ba turanci take jiba balle tagaidata ckn harshen turancin
RIHANNAH Tayo kanta tana fadin _hey girl what Are you Doing here_
KUYANGA Tasadda kanta kasa jikinta na kyarma
RIHANNAH takarewa kuyanga kallo taga yanda yarinyar tahadu ga kayan jikinta ya amsheta wandone pensil da riga bigil me siririm hannu ajikinta kanta ba kallabi gashinta yakwanto agadan bayanta
RIHANNAH Ta fuxgota Tana ihu kamar zata cinyeta don kishi _When are you coming This house_
KUYANGA takara furgita ta kankame jikinta takasa magana tunda bata fuskanci mema takece mataba balle tabata amsa
RIHANNAH ta gaura mata mari tana fadin _are you mad_ _If you talk me Rubbish i will kill you now_ ganin KUYANGA Batada niyyar magana yasa taga kamar raina mata hankali takeyi
Tashakota ta hadata da bango
Ihu da kakarin da KUYANGA Keyi yasa YARIMA dake can dakinsa kwance yasa yafito aguje
Yana ganin abinda ke faruwa yayo kansu aguje yakwaci KUYANGA Ahannun RIHANNAH yatura KUYANGA Gefe yana fadin taje maza dakinta
RIHANNAH ta cakumeshi tana masa ihu akan saiya gaya mata wacece tagani agidansa
Yazabga mata mari saida taga taurari
Agigice ta sakeshi tana rike da gurin taji marin har kwanyarta tahau kuka tana tumami agurin
Yawuce ta afusace yayi dakinsa
Ta tashi tabishi tana cewa saiya kori yarinyar kokuma ita tabar masa gidan
Tasan yana sonta sosai shiyasa take fadin hakan
Amma agun yarima wannan ba abune dazai yiyuba yama xaai yakori KUYANGA To inya ma koreta ina zataje itada batasan kowa akasar ba shine dalilin xuwanta ai inhar yabiyewa son zcyr yabi zabinta tabbas zai aikata kure domin sai ya fuskanci bacin rai gun mahaifinsa inyaji toko mahaifiyarsa da bata son bacin ransa itanma ai baxata barshi ba
Dayagaji da hargowar tata saiya zare belt yaringa dukanta ko ta kyaleshi
Ranta yabaci da irin hukuncin da yayi mata wanda bata xataba
Kwana tayi tana faranta masa rai domin sau biyar yahauta kafin wayewar gari domin ita din jurauce itace tayi masa sabo da ZAZU
OhSU Rihanna yau ga karshenki sai akara gaba
Itadai KUYANGA tana jiyo ihunta ana dukanta saita kara cika da tsoro taji kuma baiburgeta ba domin shine yajawa kansa dabaya dauko mata da bazasuzo suyi masa hauka agidaba
RIHANNAH bata kwana agidanba tuni ta fuce da ita da komatsanta tayi fushi dashi sukayi baran baran aranar
Hhhhh muje zuwa
Auntyn Sayyada da Shahida ce
725 333 PM Ummi Tandama KUYANGA
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_
United we stand and succeedOur ambition is to entertain motivate the mind of readers
httpswwwFacebookcomkainuwawritersassociation
SHARHI
ZUWA GAREKU MAKARANTAN LITTAFIN KUYANGA INASO INYI MUKU WANI DAN TSOKACI MUSAMMAN MASU YAWAN KAWO NASU RAAYIN AKAN KUYANGA TOKU SANI BAWAI INA KUSHE GA BATUNKU BA INASO KUBARNI DA NAWA RAAYIN NAYANDA NA DAUKO ABUNA AKWAI MASU CEWA KIYI KAZA GURI KAZAKADA KIBARI YAYI MATA KAZAKYANTA DAMA KISAKA TAYI KAZA KO YAZAMO MEYIN KAZA TO DUK INASO KUZUBA IDO KUGA KARSHENSA WANDA YAGA ABIN HAUSHI MA YACE ABIN BAI MASA BA ZAIDAINA KARANTAWA INBAN YI KAZABA DON BAI DACE BA TO FALILLAHI HAMDI NI DAMA BANYI DAN INMUKU DOLE BA DOMIN INHAR NABI TA BAKIN WASU TO LITTAFINA ZAIYI KWANA NE YATAFI LABARIN WATA MARUBUCIYAR TONIKUMA BANA FATAN INYI SATAR FASAHA YANDA NA DAUKO LABARINA ABARMIN AHAKA DOMIN DIRECTOCIN INDIA DANA KASAR MU NIGERIA DA SUKE HAUSA FILM BA DAYA SUKE DANA INDIYA BA AKWAI BAMBANCIN FASAHA KARYAR MUTUM YAGANO YANDA FILM DIN INDIYA ZAI KASANCE AKARSHE TO NIMA KADA ACANXAN RAAYI INA KARA FADA WACCE TAGA NOVEL DINA YABATA HAUSHI AKAN STAR MACE KO NAMIJI ANYI ABINDA RANTA BAISOBA TABAR ABIN ARANTA BASAITA FURTA MARA DADIBA INA KARA JADDADA MUKU BABU FA DOLEDOMIN KUYANGA YASAMI DAUKAKAR DA BAZAI FADUBA KALAS _tank you fans inayinku yanda kuke yina Allah yabar kauna
Da daddare KUYANGA Tana kwance taji shigowarsa dakin nata
Tayi saurin tashi tana masa Barka da dawowa
Ya xauna bakin gadon nata yana mata murmushi tare da Amsawa
Tayi mamaki domin bata xaci zataga faraarsa ba ma tunda tasan ta karya masa doka tafuta alokacin dayace kada tasake tafuto in RIHANNAR tana nana gashi harsun sami sabani adalilinta tsorone ma yadarsu aranta tana tsammanin ko fada yazo yi mata
Ta takure jikinta agefen gadon
Daya fahimci atsorace take dashi sai yasha mur yace meye kike wani matse jikinki wato kina ganin ko wani abu nazo miki ne Ko a hotel kyaleki nayi bawai hkr nayiba yanzu kuma ba zuwa nayi na taba kiba tunda kinyi sanadin barin me debe min kewa gidan dole yazamo kece zakici gaba da deben kewar tunda dama dan hakan nataho dake bawai donki dafan girki koki gyaramin daki nake zaune dakeba don inji dadin rayuwa ta dakene dan haka kizama cikin shiri zuwa daren gobe yau baa gidan xan kwana ba inada Dinner din wani abokina till down kwana zamuyi acan
1 thought on “Kuyanga Hausa Novel Complete”