Mallakin Waye Hausa Novel

mallakin Waye Hausa Novel: Compiled by Umar Dalha Mallakin waye 01 Written by Queen Samy.

Mallakin Waye Hausa Novel

Bismillahir Rahmanir Raheem

America

CaliforniaLos Angeles_
2011

Gidan yayi shiru banda sautin kukan mutanen dake ciki baka jin komai wata Dattijiwan matace wacce bazata gaza shekaru 64 ba a duniya ta fito daga wani daki hannunta dauke da jaririya wacce akalla bazata wuce watanni 4 ba
Zama tayi tsakiyan yaran dake ta sharban kuka cikinsu an rasa me ba ma wani baki itama wnn Dattijiwa kuka ne sosai ya kufce mata.

Wasu maza guda biyu ne suka shigo daya saurayi ne wanda bazai wuce shekaru 22 ba a duniya farine sol kyakyyawa yanayinsa zai tabbatar maka shima cikin tashin hankalin yake mutumin da suka shigo tare dashi yana dafe da kafadunsa wanda ko baa fada maka zaka gane mahaifinsa ne dan kuwa kammaninsu ya baci saidai kawai matashin ya dan nun masa kuruciya mutumin bazai gaza shekaru 48 ba a tare suka shigo cikin parlorn ai kiwa gaba daya yaran suka mike suka rungumesu suna kuka
Daddy is it true mummy has gone Yar budurwan ciki wacce bazata wuce shekaru 12 ba ta fadi cikin tsananin kuka da tashin hankali sosai mutumin da ta kira da daddy ya rungumeta kafin yace Nadiya dukkaninmu yan adam ne dukannninmu watarana zamu bar duniya addua shi zamuyi wa mummyn ku Allah yasa ta huta Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita.

Sosai suke kuka wasu yan yara maza guda biyu wanda da gani kasan tagwaye ne baza wuce shekaru biyar ba a duniya suka rungume dan matashin cikin suna kuka kankamesu yayi yana kuka shima sosai sun jima a haka ko wanni na kuka kafin daga bisani Daddy ya karasa ya karbi yar jaririyan dake hannun dattijiwan nan yace Amma kawota Amma ta mika masa ita tana gohe hawaye Kallonta Engr Nazif Mumtaz yake babu ko kakkautawa tausayinta da sonta a lokaci guda yana ratsa bargo da tsokansa sosai ya rungumeta yana sharan hawaye
Haka ranan gidan Engr Mumtaz ya wuni cikin tsananin tashin hankali da alhini na mutuwar matarsa kuma uwar yayansa.

 

Zaune yake cikin dakinsa ya kura wa hoton mahaifiyar sa ido har lokacin besaka komai a cikinsa ba ya kasance yana tsananin son mummin sa gashi mutuwa ta masu YANKAN KAUNA Allahu Akbar dukkanin me rai dama mamaci ne Allah ka bamu karshe me kyau ameen
Amma ne tayi sallama a kofan dakin yayi saurin ajiye hoton gefe gamida gyara zamansa murmushi Amma tayi na karfin hali kafin ta karasa shihowa dakin hannayen saurayin nan ta rike cikin nata kafin tace Irfaan you need to be very strong mu gode wa Allah Khadija ta samu kyakyawan shaida muna rokon Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita snn ka tuna kaine babba cikin yaran nan idan bakayi juriya ka jawosu jiki ba abun zaiyi affecting dinsu yanda baka tsammani Addua shine gatan mamaci ba yawan kuka da damuwa ba Irfaan ya share hawayen idonsa ya rungumo kakansa yana fadin Amma I still couldnt believe that mummy passed away kasa karasa maganarsa yayi dan kuwa sosai yake kuka rungumesa Amma tayi tana basa baki hadi da karfafa masa gwiwa
Sanda Irfaan ya fito parlor kannensa maza twins guda biyu suna zaune da gani kasan sun sha kuka karasawa yayi tsakiyansu ya zauna ya riko hannayensu Amir da Aiman suka rungume yayan nasu Irfaan ya shiga shafa gashin kansu ba tarda ya furta komai ba
Engr Nazif kuwa ranar bacci tare yayi da yar autarsa wacce suke kira da Nilam koda Amma ta dubasa a dakinsa dan karbo Nilam gani tayi ya rungumeta sosai cikin jikinsa dan haka juyawa tayi cike da tausayawa dan nata da jikokinta

Yau sati guda da rasuwan mummy hankuka sun soma dawowa jikkunansu duk da har yanzu Irfaan abin na tare dashi sosai
Zaune suke gaba dayansu a wasu kujeru mai table a tsakiya wanda daga gani ba sai ance maka na shakatawa bane dake a farfajiyan gidan daddy na rike da precious Nilam dinsa Amir da Aiman sunata wasa a can gefe fruits ne a gabansu wanda aka yayyakan kanana kaman friut salat cikin wasu cups masu kasa me dan tsini ko wani cup akwai dan stick a ciki wanda ake cin friuts din dashi
Irfaan ne ya fito daga cikin gidan yana sanye cikin armless shirt red da faran three quarter ya karaso fuskansa babu yabo babu fallasa ya gaida Amma da Daddy kafin ya zauna a daya daga cikin kujerun Nadiya ta mika masa cup daya tace ya Irfaan have some tabe baki yayi yace no thanks kallonsa duka sukayi kafin tace zai taimaka maka da appetite Girgiza kai yayi a karo na biyu kafin ya karasa ya karbi Nilam dake hannun daddy yace come here Angel Wasa yake kan yima Nilam tana dariya shi kansa sosai yake dariya su daddy da Amma harma da Nadiya saida sukaji dadin sakewan da Irfaan yayi
Bayan ya zauna ne Daddy yace irfaan dama fitowarka muke jira Irfaan ya dago ido yana duban Daddy kafin Dady yaci gaba da fadin mun yanke shawarin komawa Nigeria in the next few days what do you think
Shiru kaman nazaice komai ba sai kuma yace is that really necessary Daddy ya riko hannunsa yace Son hakan ne kawai zai mantar mana da rashi babban da mukayi a nan States and your siblings ya kamata su san kasarsu su san aladunsu I think lokaci yayi da zamu koma
Shiru Irfaan ya danyi kafin ya dago ya dubi mahaifin nasa yace but Daddy what about my sch na riga na fara university a nan shiru Daddy yadanyi na wasu lokuta kafin yace yeah son hakane Amma ce ta katse su da fadin Yes dole mu bar States in a couple of days na gaji da zaman nan snn mahaifinku ma gwara mu tafi ya samu yayi aure ai bata gama rufe baki ba Nadiya ta mike tana masu mugun kallo kafin tace Amma aure fa kikace daddy ne zaiyi aure for heaven sake this is ridiculous Wllhi daddy bazaiyi aure ba wato har kin mance mutuwan mummyn mu kina masa magan Enough Nadiya Irfaan ya daka mata tsawa ma Amma ne ko ma Daddy kike daga murya Amma da Daddy kam mamakin kishi irin na Nadiya suke ji karama da ita har tana taya late mother dinta kishi
Kuka Nadiya ta fashe dashi ta shige cikin gida a guje Irfaan na kwala mata kira inaaaa ko saurarensu batayi ba ta shige Aiman da Amir dake gefe suna wasa ganin Nadiya ta shige a guje tana kuka yasa suma suka fashe da kuka a tunaninsu wani ne zai sake mutuwa nan suma su Amir da Aiman suka rufa mata baya
Engr Nazif idan akwai abunda yafi tsana tofah shine bacin ran yayansa musamman da yanzu mahaifiyarsu ta mutu yayi alkawarin bazai sa su kuka ba zai zame masu uwa da uba zai kasance tare dasu a ko wani irin hali suke ciki Da sauri irfaan ya mike yabi bayan kannensa Daddy yabisu da kallo kafin ya juyo yana kallon Amma yace pls Amma you need to be more understanding with what they are going through you shouldnt have talk that way Ki tunafa they just lost their mother be kamata kimin maganar aure yanzu ba especially at their presence
Kallon mamaki Amma tabisa dashi kafin tace dole mu koma Nigeria bazan iya tsayuwa inaji ina gani dabiun turawan yamma yayi tasiri a zukatan jikoki na ba daga haka Amma ta mike ta shige cikin gida

Knocking Daddy keyi a kofar dakin Nadiya amma fir taki budewa Pls sweetheart let us talkcikin kuka take fadin no just go away I dont wanna see you you going to marry another woman arent you
Daddy ya fuzar da iska yace Sweetheart let me in first lets talk about this juyawan da Daddy zeyi yaga Amir da Aiman suna sharban kuka da sauri ya karasa wajensu ya tsuguna ya rungumosu yana fadin whats wrong boys cikin kuka suke fadin Adda Nadiya told us youre going to abandon us youll have a new family in Nigeria Dafe kansa Daddy yayi a hankali ya furta Lord of mercy rungumesu yayi yace that will never happen boys I love you ultimately I will never abandon you Oya come here ya manna masu kiss a gashinsu kafin ya mike yana rike dasu suka soma saukowa daga stirs

QueenSamyNovels
818 2021 Umar Dalha Mallakin waye 02

_Written by QueenSamy_

Haka Nadiya taki bude kofan nan har dare gaba daya hankulansu yatashi da kyar da magiya ta bude wa mahaifinta lallashinta ya shiga yi kaman wata karamar yarinya ita kuwa sai basar da dad din nata take wnn mummunan dabia na western people sosai yayi tasiri a rayuwan gidan Engr Nazif Mumtaz

Daddy promise me youll not remarry Nadiya tace cike da shagwaba rungumota Daddy yayi yace my dear stop thinking silly ok for now kula da rayuwarku shine a gabana ba batun aure ba your grandma wasa take kawai ba sabida aure take so mu koma Nigeria ba you see sweetheart akwai Company din late daddy na a Nigeria MM Builders so ever since your grandpa pass away amininsa shi yake running company din I think lokaci yayi da zan koma na karbi companyn dad dina na ci gaba da kula dashi what do you think
Shiru Nadiya ta danyi kafin tace what about your job here in the States Hannayenta daddy ya rike yace Ill resign darling

But daddy are you sure we gonna have a better life there I mean our sch and so on Cike da kosawa da tambayoyin Nadiya karama da ita sai yawan magana daddy yayi gyaran murya yace of course honey that will be even much better I promise you that

But daddy what about our friends here in the States am sure we gonna miss them ta karashe maganar tana turo baki
Daddy yace sweedy pls stop making this so difficult okay youll have a chance to say good bye to them okay now lets go and have dinner ok

A tare suka sauko downstairs daddy na rike da hannunta hes so friendly to his kids Amma tabisu da kallo kawai tana mamakin yanda gaba daya dabiun turawa yayi tasiri a rayuwan gidan danta.

Da murmushi Daddy yace kids tomorrow youll visit all your friends and say goodbye to them ok Amir da aiman suka soma murna suna fadin yeeeey we leaving to Nigeria Tabe baki Nadiya tayi ba tare da tace komai ba.

Irfaan ne ya shigo babu ko sallama sai cewa da yayi Hi everyone daddy yace Son lets have dinner Irfaan ya dan yamutsa fuska yace daddy I dont feel like eating just go ahead Amma tabisa da kallo kafin tace irfaan zo ka zauna kaci ko kadan ne kallonta Irfaan yayi da manyan idanunsa harda wani juyasu kafin ywce Okay granny just because you insist ya zauna a daya daga cikin kujerun yana duban Nadiya Spoon din gabanta ya dauka kafin yace hey are you still mad baki a tureta dago ido tana dubansa Daddy yayi karaf yace Son eat up is your favorite.

murmushi Irfaan yayi ya soma cakalan abincin kaman me tausayinsa
So when are you guys leaving Irfaan ya tambaya daddy yace in a couple of days Son be careful while youre here alone okay.

Irfaan ya gyada kansa yace you really dont have to worry about that daddy am not a spoiled child kai da mummy raised me well may she rest in peace duka suka amsa da ameen.

Daddy yace duk da haka Son you really need to be very careful kaga yanzu ka soma karatu just level 2 kake snn kace har masters zakayi kafin ka dawo Nigeria so kaga dole na damu.

Irfaan ya juyo ya kalli Amma yace Amma you see daddy is treating me like a kid again ko zamu zauna dake a nan States ne.

Tabe baki Amma tayi tace Allah tsareni da ci gaba da zama a nan yara duk baku san aladunku ba kun rike _aladun wasu_ kuna koyi dasu kaima da zaran ka gama sch zaka dawo Nigeria.

Murmushi kawai irfaan yayi yace a ransa _me zai kaini Nigeria for goodness sake I rather stay here all alone da na koma Nigeria_ Tattaunawa suka ci gaba dayi har zuwa lokacin da suka gama cin dinner

Nadiya ta dubi Amma tace Amma zamu tafi da Nannyn Nilam Nigeria knn Amma ta narka mata harara tace akan me taje taci gaba da koya mata dabiun wasu Ill find her another Nanny a Nigeria Nadiya tayi kicikicin da fuska tace pls Amma kinga mun yarda zamu koma Nigeria pls do this for us mu tafi da Patricia taci gaba da kula da Nilam itace tasan Nilam tasan abunda take so da wanda bata so pls Amma dont say no I beg of you ta karaso ta haye jikin Amma tana rokonta.

Dole ba don Amma taso ba tace alright fine naji zamu tafi da Patricia amma da zaran Nilam ta soma wayo zamu sama mata nanny musulma a Nigeria wacce zata koya mata dabiu masu kyau Nadiya ta dan turo baki ba tareda ta kuma cewa komai ba Daddy ma yayi naam da shawarin Nadiya dan kuwa Nilam bata yarda da kowa sai Patricia snn idan akwai abunda ya fi tsana tofah shine kukan Precious dinsa.

Kwana biyar suka kara a Los Angeles kafin suka daga zuwa gida Nigeria

Nigeria
_Abuja LifeCamp_

Unguwar LifeCamp dake birnin tarayya Abuja unguwace wanda gidajen dake ciki kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa gidajen masu hanu da shuni ne ko wani gida yana jere cikin tsari da kyau akasarin ginannukan gidajen bene ne
Gidan EngrNazif Mumtaz yana daya daga cikin jerin gwanon gidajen nan tsayuwa fadin irin tsaruwan da gidan yayi bata lokaci ne dan kuwa komai na gidan me kyau ne abin birgewa gwanin shaawa Kyaun gidan yasa Nadiya taji dadin dawowa Nigeria dan kuwa ita yarinya ce me balain son kyalekyale

MM Mumtaz and Maaruf Builders Of Company

Alhaj Maaruf ya kalli Daddy yace gwara da Allah yasa ka dawo dan dama ni gaji da rikon wnn mukami dan shekaru sunja nima ina bukatan hutawa Daddy yayi murmushi ya kalli Alhj Maaruf aminin mahaifinsa kafin yace Baba na gode da dawainiyan dakayita min da dukiyata Allah ne kawai zai biyaka
Girgiza kai Alhj Maaruf yayi yace Nazif idan akwai wanda yafi cancanta ya mika godiyansa to nine dan kuwa mahaifinka Mumtaz ya gama min komai a rayuwa Ya shiga bude files yana ciro takardu ya mika masa kafin yace an jima zamu kira meeting gaba daya staff su hallara the New President of MM Builders is here
Daddy ya girgiza kai yace Aa Baba youll remain the president ni zan rike mukamin Chairman Alhj Maaruf ya girgiza kai yace Nazif kai zaka zama president besides kaine me highest shears a MM builders ni zan yi retire ne daga rana me kamar ta yau kai zaka ci gaba da juya mun dukiyata
Haka aka kira meeting a babban conference hall dinsu tareda Shear holders da kuma staff dinsu aka gabatar da new President of Mumtaz Builders Daddy ya gabatar da kansa hadi da gaisawa da illahirin mutanen

 

Hajiya Karima ta cika tayi fam dajin irin batun da mijin nata yazo mata dashi ita fah zama dashi take dan ta mallaki MM Builders amma bacin haka me zaisa taci gaba da zama da wann tsohon wanda tasan nan bada jimawa ba zai zama gawa Mikewa tayi taci gaba da safa da marwa a cikin dakinta a hankali ta furta tabb inaa bazata taba sakuwa ba dole na san yanda zanyi na karba wa tilon yata Companynta.

Abban Sojoji Hausa Novel Complete Document

Queen Samy
818 2021 Umar Dalha Mallakin waye 03

_Written by QueenSamy_

Laila ce keta doka Sallama a kofa amma ko kadan Hajiya Karima bataji ba sosai hankalinta ya tafi ga tunanin da take da mugun mamaki Laila ke bin mahaifiyar tata da kallo har ta karasa shigowa cikin dakin
Hajiya Shiru hajiya karima bata amsa ba Laila tayi gajeren tsaki ta shiga buga kujeran da Hajiya ke kai tace Hajiyaaa Wnn karan da dan karfi sai snn Hajiya Karima ta dago tana duban Laila tace Ke kuma yaushe kika zo Laila ta jakanta bisa sofa tana zame mayafin kanta take fadin nafi minti biyar a nan ina sallama baki jini ba Hajiya tunanin me kike ne haka
Hajiya Karima ta sauke ajiyan zuciya kafin tace ke kuma daga ina
Laila tace na sauke Aziza gidan kawarta shine na karaso Hajiya wai meke damunki ne kinsan fa likita ya hanaki yawan damuwa
Galala Hajiya Karima ta kalli Laila kafin tace tunanin dan isakan tsohon nan nake
Da mugun mamaki Laila ke kallonta kafin tace waye kuma dan iskan tsoho
Tsaki Hajiya ta buga kafin tace Alhj Maaruf
Kan ubancan Hakan Laila tace a fili Ido cikin ido take duban mahaifiyar tata kafun tace wai dama Alhaji ne dan iskan tsohon mahaifi na
Tsaki Hajiya ta buga a karo na biyu kafin tace yo meye idan ba dan iska ba har nice zai dubi tsaban ido na yace ya cire hannunsa a MM Builders wai dan Late Alhj Mumtaz ya dawo daga States dan haka ya mallaka masa kampanin mahaifinsa
Laila ta gyara zama tace Hajiya ban fahimci zancen ki ba wai Alhajin ne ya mallaka ma wani MM kan wani dalili
Kan dalilin ubansa ne ya masa komai harta shears dinsa ubansa ne ya saya masa Wai hajiya na tambayeki dama MM Mallakin waye
Tsaki Hajiya Karima tayi kafin tace a iya sanina mallakin Alhj Mumtaz ne amintaka dake tsakaninsu da Alhaji ya mallaka masa babban shear a company n da farko sunan companyn Mumtaz Builders karshe har ya maida sunan kampanin ta koma MM Builders wato Maaruf and Mumtaz Builders
Laila ta sauke ajiyan zuciya tace tabdijam toh shi wann dan nasa me ya dawo yi yanzu Nigeria Hajiya tace matarsa ta mutu mana shida uwarsa sun tarkaso sun dawo dama uwar nasa tun mutuwan mijinta wato ubansa ta koma can American wajen danta sai yanzu ne zai tuna da kampanin ubansa bayan Alhaji ya gama masa shan wuya saida company ta ginu tayi kaurin suna a nahiyar Africa baki daya duk yammacin Africa babu kampanin da take shigo da ingantattun kayan gine gine irin MM Builders sai yanzu ne zai dawo ya mallaki kampaninsa
Laila ta girgiza kai ta furta bazai saku ba Hajiya MM Mallakin mu ne
Dariya Hajiya Karima tayi tace haba ai duk wanda yasha tuwo da Karime tofah miya ya sha na jima ina harin wnn Company ta zama mallakinmu nida ke da kuma diyarki Aziza Wnn dalili ne yasa na salwantar da rayuwar Hindatu matar Maaruf ta farko snn na salwantar da rayuwar tilon yarsa da jikansa Da mugun mamaki Laila kebin hajiya Karima da kallo kafin tace tilon yarsa Me Hajiya take nufi
Ganin Hajiya ba a hayyacinta take zantuttukan nan ba yasa Laila mikewa tsaye tana fadin Hajiya me kike cewa tilon yar Alhaji kinaso kice ni ba yarsa bace ko me Kinaso kice yaya Faty ce kawai diyarsa Sai snn Hajiya Karima tayi realizing me take cewa da sauri ta riko hannun Laila tana son zaunar da ita Girgiza kai Laila ta soma tana fadin wllhi sai kin fada min komai waye uba na
Hajiya Karima ido a kekashe tace banso kisan wnn boyeyyen sirri yanzu bam amma Allah ya kaddari yanzu zaki sani
Laila Alhj Maaruf da Alhj Mumtaz sun kasance aminan juna Alhj Mumtaz ya kasance hamshakin dan kasuwa wanda tun yana da kuruciya Allah ya albarkaci kasuwancinsa toh a dalilin amintarsu da Alhj maaruf yasa shi jawosa cikin kasuwancin wanda bayan ya bude kampaninsa me suna Mumtaz builders daga baya ya maida sunan Companyn MM Builders wato Mumtaz Maaruf knn ni kwa na kasance ina zuwa aikatau gidan Alhj Maaruf a lokacin ina yar matashiyan budurwa ita kuwa Hajiya Hindatu ta girme mun sosai babu ma hadi sun jima da aure itada mijinta Allah bai basu haihuwa ba kullum suna shaawan yaya musamman idan suka ga dan Alhj Mumtaz da Nazif matarsa Hajiya Salma kullum cikin adduan Allah ya basu haihuwa suke amma shiru babu haihuwa
Watarana Hindatu take cewa kawarta Salma itakam tana so mijinta ya sake aure ko Allah zai basu haihuwa Salma tace kiyi hakuri Hindatu haihuwa lokaci ne da zaran lokaci yayi sai kiga an dace tunda na labe naji wann zance dukda karancin shekaruna a lokacin saida na shiga na fita nayi yanda nayi Alhaj Maaruf ya aureni Salma matar Alhj Mumtaz ita tayita bawa Hindatu baki lokacin da suka fuskanci nice a matsayin amaryar da akayiwo wa Hindatu
Muna zaune a haka shekaru suka danja Hindatu ta rikeni tamkar kanwa bata nuna min komai nima de shiru babu haihuwa har abin ya soma damuna ana haka kwatsam Hindatu ta sami ciki aikuwa zo kiga murna wajen Hindatu da Maaruf harma da aminansu guda biyu suna taya su nan fah hankalina ya tashi sosai na shiga na fita amma Allah ya kaddara sai Hindatu ta haihu cikinta wata tara kuwa ta haifo diyarta kyakkyawa Nan kulawan Maaruf ya koma kanta kwacaukam dama yana tsananin sonta bare ta haihu nan fa na koma tamkar saniyan ware a cikin gidan shiru shiru ban samu ciki ba har diyar Hindatu Fatima ta soma girma yarinya me shiga ran jamaa mussaman Maaruf Fatima ta shiga ransa sosai dan sunan mahaifiyar sa taci
Ana haka naji kishin kishin Hindatu nada wani ciki gashi ni shiru aifa nan nace banci ta zama harta kasashen ketere sai na tsallaka dan nemo magani a wnn yawo nawa nayi yo cikinki babu maganin da bansa wa Hindatu ta mutu ba ita da binda ke cikinta amma shiru wata rana da daddare na shiga har dakinta na murkusheta da pillow har ta mutu ita da jaririn cikinta da baifi na wata biyu ba
Kuka wajen Alhj Maaruf baa magana babu yanda Salma batayi abata Fatima diyar aminiyanta ba amma fir naki nace kaji kini bini banza haka nayita falfala mata rashin kunya dole ta hakura shima Alhj maaruf nason kasancewa da Fatima dan tana debe masa keyawan uwarta Bayan na haifeki ne kuka taso Fatima a matsayin yarki koda Fatima ta girma takai aure aka mata aure nan fa na soma tuanain watarana dukiyan Alhj Maaruf zai zama mallakinta ita kadai idan tana raye a lokacin sunso juna ita da Nazif dan Alhj Mumtaz da Hajiya Salma amma fir naki bari suyi aure dan kuwa sai abinda nace hana Nazif auren Fatima danayi ba karamin tashin hankali ya shiga ba tindaga wnn lokaci yayi tafiyarsa can kasar America yaci gaba da karatunsa bayan tadiyansa na tilasta aka aurawa Fatima wanda bata so dan kuwa Nazif shine masoyinta
Koda Nazif yaji Fatima tayi aure nan yace bazai dawo Nigeria ba har ya sami wata wacce suka hadu a makaranta ya aureta suka hayayyafa
Toh Fatima ta jima bata haihu ba har kema kika kai aure sanda naga Fatima ta samu ciki na tabbata watarana dukiyan Maaruf zai zama mallakinta da abinda ke cikinta toh tunda ga nan na mata asiri ta haukace ta shiga uwa duniya wanda daga baya nace maku ta mutu muka hada baki da mijinta bayan na cika masa aljihu da makudan kudi mukace ma Alhj Maaruf mutuwa tayi ita da abunda ke cikinta har rana me kaman tayau bamusan yanda ta dosa ba ko ta haifi abunda ke cikinta oho mata ko bata sai Allah amma boka ya tabbatar mani bata sake dawowa cikin rayuwata ba
Hajiya Karima ta riko hannayen Laila tace Laila duk wnn abubuwan danayi nayisu ne dan inganta rayuwarki dana diyarki Aziza Kinga yanzu ko Maaruf ya mutu dukiya de namu ne mu kadai ni da ke da kuma diyaki Aziza snn ni nayi sanadiyan mutuwan Alhj Mumtaz duk dan wnn Company da ya tsolen ido ya dawo mallakin mu Bayan na gama sa ran Nazif da uwarsa Salma bazasu dawoba kwatsam sai su dawo rayuwata Bazai taba sakuwa ba Dole musan abinyi Dole mu kashe mijinki ki auri Nazif
A zabure Laila ta mike tana duban Hajiya kafin tace A kashe mijina kuma hajiya tsaki hajiya tayi tace yo se me Ke barin fada maki Nazif yafi wnn mijin naki komai da kika sani a sanin da na masa da kyakyawan saurayi ne wanke hannu ka taba balle yanzu da Amurka ta dada goge fatarsa
Murmushi Laila ta soma kafin tace Kai Hajiya baki da dandanin imani aiko tundp a baya tun inda kuruciyata idan nagansa yazo wajen yaya Fati wani haushi nake ji dan bana mance kamanninsa kuma har yanzu ina sonsa Ta ru gume Hajiya tana fadin shawarinki yayi Hajiya

4 years later

Namijin Duniya Hausa Novel Complete

Cibiyan goya marayu
_Gidan marayu_

A hankali take takun sadaf sadaf har ta samu tafice daga kofan ta juyo tana kallon ta gefenta tace Yusrah wllhi yaukam da wuri zamu dawo kafin Anty Larai ta capke mu Yusra tayi dariya maras sauti tace kai Deejah dadina dake akwai tsoro harara Deejah ta galla mata tace muje yana can kasa yana jiranmu A tare suka nufi yanda yayi parkin motarsa
Kwankwaswa sukayi ta glass din motan aiko da sauri ya bude masu yana mayaudariyan murmushi yace Deejah gayu bismillah yamutsa fuska Deejah tayi tace kaga Safwan banson irin wnn kashe idon naka ni na fada maka ni ba yar iska bace Tsaki yusra tayi tace Deejah dan Allah ki shiga mu tafi kadin yan sa idon Anty Larai su ganmu Harara Deejah ta galla mata kafin ta shige gaban motan
Safwan kuwa dariya yayi yace a ransa kaji Deejah dai da wani maganar rainin hankali tana aikin rawa a club tana ce mani ita ba yar iska ba ko yar meye ita oho daidai nan sukayi parking a kofar Amazing Club

Queen Samy
818 2023 Umar Dalha Mallakin waye

_Written by QueenSamy_

Safwan na gama parking ya fito da sauri ya buewa Deejah harda wani nade hannunsa ta baya guda daya ya dan sunkuya kafin yace here we are gwanar rawa Murmushi kawai Deejah tayi kadin ta sako kafarta ta soma fitowa takalmin kafar high hill ne sosai baki me dan farin duwatsu tana sanye cikin ash din top ta daura black boyfriend jacket a sama wandon jikin red ne sai veil red data daura a kanta Deejah budurwa ce yar kimanin shekaru 19 ba fara bace snn bata layin bakake ba wani kyau sosai take dashi ba amma baa kirata maras kyau ba tana da kyaunta daidai misali hakan nan gashin kanta me tsanti da tsaho ne kyaun jikinta shi yafi komai daukan hankalin da yawan mazan da sukayi tozali da ita Allah ya mata diri irin na wacce zaka gani kace lallai wann ta cika mace Deejah gwanar son rawa ce wnn dalili yasa tayi kaurin suna a Amazing Club takan je tayi rawa akan Stage mutanen da suke club din susha kallo yayinda da yawa suke mata barin kudi da yawan maza suna son kawo kokon baransu wa Deejah amma babu fuska dan haka nan take da azaban masifa bata barin kota kwana balle tayi tsami wnn dalili shi ya ceceta daga idon maza yan bariki maabota zuwa club Safwan ne kadai Deejah take kulawa shima din dan babu yanda ta iya dashine ko fada ta nemo Sadwan ke tare mata tun tana hantaransa har karshe suka koma tamakr abokai

Yusrah na taka mata baya Safwan na gefenta suka shigo cikin club din nan fah waje ya kacame da ihu da shewa da pito fadi suke ga Deejah ga Deejah wasu kuma na fadin the Great DD wato Deejah Dancer tana isowa kuwa ta shigadaga masu hannu nan ta haye kan stage gamida cire jacket din jikinta tayi jifa dashi nan fah aka kuma saka shewa wakan da take tsananin so aka saka mata nan ta soma rawa kama babu kashi cikin jikinta Nana aka soma tururuwan zuba mata kudi Yusra na tarawa
Karfe 1130pm daidai Deejah ta sauko daga kan stage ta jawo Yusra suka kebe tace Yusee we need to leave this place right now Yusee ta dan hada rai tace kai Deejah daren fah da saura Deejah taja tsaki a hankali kafin tace Yusee kindai san yanzu dole Anty Larai ta saka mana ido sabida gulman mu da ake kai mata ya soma yawa kinga dai kallon malaman addini take min yanzu idan ta gane ni yar rawa a Club ne me kike tunanin zai biyo baya
Yusee tayi murmushi tace toh Deejah mu daina wnn sanaa mana am pretty sure kudin da kika tara yanzu zai isheki ki soma karatun jamianki Deejah ta sauke ajiyan zuciya kafin tace wllhi Yusee inaso nayi university yanda baki tsammani snn inaso watarana na rinka taimakawa Orphanage foundation ina tausayin waenda suka tashi babu iyaye iri na rawan da nakeyi a club yana daya daga cikin burina na tara kudi dan taimakawa marayun da suke Orphanage ba zallan wnn ba kinsan rawa hubby na ne
Yusee ta saka hijabinta kafin ta mikawa Deejah nata tace oya saka mu tafi Deejah ta karba ta saka gamida cire dogon takalmin kafarta kafin suka fito can gefen titi
Safwan na zaune na jiransu cikin club ashe su tuni sun fice Ta glass yake hango su suna kokarin taran mashi Ai a sittin Safwan ya mike ya fito ya nufesu Kallon mamaki ya bisu dashi kafin yace da dan mashin din malam jeka abinka
Deejah ta dan hararesa kafin tace kaga Safwan yanzu gari yayi shiru idan ka kaimu zaa iya ganinmu Murmushi Safwan yayi kafin yace Deejah bazan iya barinku ku tafi ku kadai cikin daren nan ba duk da nasan kun saba wuce haka a waje but this is very risk is dangerous someone might harm you bai jira cewansu ba ya karasa ya kawo motarsa har gabansu yace oya ku shige mu tafi
Babu musu suka shige a cikin mota Safwan yake cewa Deejah meyasa baku so asan kuna wnn sanaa
Wata uwar harara Deejah ta watsa masa kafin tace malam kaga this is non of your business idan zaka kaimu muje idan bazaka kaimu ba fine ai dama ba saka mukayi dole ba murmushi ya kuma yi kafin yace Allah huci zuciyarki ni da zaki bi shawarata ma da kin bari na turo maganar auren bai gama rufe baki ba Deejah ta dakatar dashi Au me Kaga Safwan ni bance maka aure zanyi yanzu ba karatu nake shirin farawa kuma da kaga bamu so asan muna zuwa club a Foundation dinmu sabida kar a mana aure ne anaji zaa hadamu aure da koma waye idan har kana so alakarmu ta ci gaba toh kaja bakinka kayi shiru idan lokaci yayi naga zan iya aurenka fine Da mamaki Safwan ke kallonta bata taba kawo masa magana makamanciyar wnn ba wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa shikuwa ko yaushene yana iya jiran Deejah muddin zata yarda ta auresa

A can hefen layinsu yayi parking kafin suka fice cikin sanda suka shigo Orphanage ta kofan baya dan dama har spire key na kofar garesu Suna shigowa suka samu kowa yayi bacci kai tsaye dakinsu suka wuce suna shiga suka soma shirin bacci motsin da sukaji ne yasasu saurin rufe idanuwansu kaman masu bacci
Anty Larai ce ta shigo ta tarar suna bacci a hankali ta rufe kofar tayi ficewarta tana fita suka bude ido hadi da yin dariya

Washe gari da safe Deejah tayi wankanta ta fito cikin shiri dan dama tana daukan ajin yara a makarantar su dake cikin Orphanage kai tsaye wajen karywa ta nufa Anty larai na zuba wa yara breakfast Deejah ta karaso haba nan fa yaran suka soma Anty Deejah Anty Deejah nan Deejah ta soma wasa wa yaran nan kaman yanda ta saba Deejah akwai farin jini wajen yara da manya dake rayuwa a Orphanage wnn dalili ne yasa wasu suke hassada da ita
Deejah ta karbi abincin daga hanun Anty Larai ta ci gana da rabawa yaran bayan ta gama ne tace dasu Ok kids kowa ya wuce aji ina nan zuwa banda makara duk wanda ya makara zan masa bulala tana fada tana masu alamau da hannu fuskanta dauke da murmushi Da gudu yaran suka nufi wajen wanke hannu suka wanke kafin suka doshi ajijiwansu
Anty Larai ta dubi Deejah tace Deejah dama akwai maganar da nakeso muyi Deejah ta dawo da hankalinta gareta tace naam Anty Anty larai ta dubeta tace Deejah maganganu akanki da Yusra a Foundation din nan ya soma yawa labari ya riske cewa kuma yawon dare Da mamaki Deejah ke kallon Anty larai kafin tace Haba Anty meyasa zaki rinka daukan zantukan mutane akanmu kawai de hassada suke yi damu ta juya tana watsawa Tani dake can gefe harara kafin taci gana da fadin Anty fada mun wacce munafukar ne ta kawo maki wnn labarin kanzon kuregen yanzu taga yanda koyawa muafuki hankali kawai dan sunga kinaso na shine bari a nemi hanyar rabamu ta karsa gaban Tani tana girgiza taci gaba da fadin wllhi duk munafuncin munafiki duk sa idon basa ide nan gani nan bari haka zai ganmu da Anty Larai ya barmu Tani cikin kuluwa ta mike tana fadin ke da wa kike Dake nake good for nothing hypocrite nan fah fada ya soma tashi tsakanin Tani da Deejah a fusace Anty Larai ta karaso tana masu fada Yusra kuwa hayaniyar da taji yasata saurin fitowa cikin uniform dinta da alama makaranta zata dan ita bata gama sakandare ba
Sosai Anty Larai ta masu fada Tani rai bace ta bar wajen Yusra sulum sulum zata wuce Anty Larai tace zo nan yusra Yusra ta zaro ido tace naam Anty kinjini sarai Anty larai ta bata amsa Anty zanyi lattin sch kallon da Anty larai ta watsa mata yasata saurin karasowa
Ku fada mun gaskiya kuna fita da daddare kokuwa kwalla ne ya ciko idin Deejah ganin haka yasa jikin Anty Larai yin sanyi dan kuwa tana tsananin son Deejah wani sain daughter ma take kiranta wasu nannys a wajen ma Deejhn Larai suke kiranta Da sauri Anty larai ta karasa ta riko hannun Deejah ta dubi yusra tayi mata alama da hannu kan ta tafi Yusr hamdala tayi a ranta kadin ta fice
Hannu Anty larai tasa ta soma sharewa Deejah hawayenta kafin tace Deejah youre like a daughter to me bana son abunda zai sameki tun tasowarki kimsan da haka duk fadin gidan nan babu yarinyar da nake so irinki kowa ya maki shaida da hali na gari ba yara ba ba manya ba ina tsorin kar ki bata rayuwarki Dole na damu da jin zance da yake tashi a gidan nan yau idan labarin nan ya isa ga gwamnati kinsan hukumcin aure zaa maku da kowaye so banaso haka ta faru dake daughter da inada halin turaki makarantar gaba da sakandare da na turaki kin sani nan foundation zuwa sakandare kawai ake biya maku nima dawainiya sunmin yawa ne ga iyayena ga marayun yayana bacin haka kinsan babu abunda bazan maki ba rungumeta Deejah tayi kafin tace kiyi hakuri Anty larai nima ina sonki donke uwace a gareni mutane ne kawai suke neman rabamu insha Allah bazan taba baki kunya ba
Anty larai tayi murmishi tace thats my girl maza jeki koyar da yaranki nasan suna can suna jiranki Da murmushi ta wuce ta shige ajin yaran nan suka soma tsalle ita da yaran dan dama rabin karatunsu talle ne da rawa a ajin Deejah

Maxico
_Chicago_

Yana zaune kan wata benchi dake gefen hanyan street din da zai kaika _mexico city_ dake a birnin _Chicago_ shigan da yayi zai tabbatar maka lokaci ne na sanyi yana sanye cikin gray shirt da blue jeans ya daura bakar jacket a sama hannayensa rufe ciki hand gloves kafarsa sanye cikin bakar booth gashin kansa sai fifituwa yake alamun iska na kadasu Kallon mutane yake yanda suke ta wucewa a lokaci guda kuma yana sipping hot coffee din dake hanunsa
Wayansa ne ta soma ringing ya ajiye coffe din a gefe kafin ya daga wayan da fariansa ganin granny dinsa ce me kira
Hello my amazing granny how you doing pretty
Murmushi Amma tayi kafin tace Irfaan bazaka canza ba knn yanzu kuma me ya kaika Mexico daga Los Angeles jiya daddynku yace mun kana Chicago
Murmushi Irfaan yayi kafin yace there you go again granny da sauri Amma ta katse sa kaga ni idan kana magana dani kayi hausa dan nasan yanzu da kyar idan baka mance hausa ba
Dariya me sauti Irfaan yayi kafin yace Come on granny you know am not use it I cant speak it fluently Koma de yaya ne haka nake so kamin Amma ta fadi
Murmushi yayi yace Alright fine na gama final exams dina so sai na karaso nan Mexico zan danyi spending couple of days sai na koma States daga nan kuma idan na kammala hada takarduna zan zo Nigeria na ganku dan am damin missing you guys
Murmushi Amma tayi tace muma muna son ganinka Irfaan nan suka soma hira sosai da Amma kafin ya tambayi kowa Nilam ne ta shigo ta girma tayi wayo yarinya yar shekaru hudu Amma ta bata wayan ta shiga masa surutun gwalamniya

 

Aziza ne kwance jikin Mum dinta Laila sai sharban kuka take Laila ma sai matso hawayen karya take Hajiya Karima sai faman basu baki take itama tana sharan hawaye
Amma tayi sallma ta shigo cikin parlorn dake cike da mutane yan karban gaisuwa rabonta da Hajiya Karima tun mutuwan mijinta Alhj Mumtaz sai yau suka hadu wajen karban taaziyan mijin yarta Laila ga mamakin Amma sosai Hajiya Karima ta tarbeta sai nan nan da ita takeyi Amma ta masu taaziya gamida shawarwari na ban hakuri wa Laila Amma ta dubi Hajiya Karima tace Nazif yana tare dasu Alhj yana so ya shigo ya maku taaziya da sauri Laila ta dago kanta jin an ambaci Nazif Hajiya Karima ta washe baki tace ya shigo mana ta dubi wata yatinya dake gefe tace maza ce masa ya shigo Amma tace aa barin masa waya sai ya shigo
Engr Nazif Mumtaz wanda a halin yanzu yake da shekaru 52 a duniya idan ka gansa zaka zata dan shekara 40 ne yana sanye cikin ash din jampa da hula sallamansa cikin muryansa me cike da charisma ya daki dodon kunnuwansu aiko nan Laila ta dago kai tana binsa da kallo bata yi tsammanin haka ya koma ba ko gasan matasa ya shiga wnn zai lashe sanda yake gaida Hajiya Karima sai nan nan dashi take koda tace masa ga Laila su gaisa bai ko kalleta ba kasa yake kallo har suka gama gaisawa Laila ko wani mayen kallo ta bisa dashi har ya fice ta gama ayyanawa a ranta ta samesa an gama Haka har bayan kwana uku Hajiya Amma tana zuwa karban gaisuwan mijin Laila ita kanta Amma tana mamakin canzawan da kishiyar marigayiya aminiyarta tayi wato Hajiya Karima wani sabon alaka ne take son kullawa a tsakaninta da Amma

Yau ta kama alhamis Anty Larai ne zaune tana kallon labarun tara a NTA nan ta hango gidan wani taaziya ana nunawa kaman daga sama aka hasko fuskan uwar dakinta da ta jima da barin kasar nan ta koma America zama ta gyara tana kallon ai kuwa ba gizo take mata ba ita ce dai Hajiya Salma jwar dakinta a da kafin ta soma aiki da cibiyar goya marayu

Queen Samy
818 2041 Umar Dalha Mallakin waye 05

_Written by QueenSamy_

Yau kwana biyu da komawar Patricia nanny n Nilam kasarsu America kuka sosai Nilam keyi hardasu Aiman da Amir harta Nadiya saida tayi kukan tafiyan Patricia Amma kam hakan yafi mata yanzu zata samu nanny musulma ta kula mata da rayuwar jikokinta
Gaba daya hankalin EngrNazif ya gaza kwanciya musamman idan yaji sautin kukan Precious Nilam tana kwance kan kirjinsa yana aikin rarrashi Daddy I want her back Nilam ta fadi cikin kuka
Oh my Precious I promise you Ill find you a new nanny here a very good one who can take good care of my Precious ya karashe maganar yana kwantar da ita bisa kirjinsa
Nadiya ce ta turo kofa ta shigo Good morning daddy ta fadi sanda take karasawa kusa dasu murmushi Engr Yayi kafin yace good morning Sweed are you ready for the sch
No daddy am stayin at home with your Precious ta karashe maganar tana shafa kan Nilam tace right daddys precious
Take mood din Engr ya canza dan kuwa idan akwai abunda baiso to yaro yayi missing sch
Girgiza kai Engr yayi kafin yace No Nadiya zakije sch you know youre writing your Waec examz soon so I dont want you to be missing classes ok
Nadiya ta dan turo baki tace Daddy am tired of wearing this uniform for heaven sake is awkward su a nan Nigeria wai dole mutum yayita saka uniform am dammn sick of it dad
Youll soon graduate sweedy and shiknn kin daina sakawa oya jeki shirya barin saka ma Precious nata kayan Ok daddy ta fadi sanda take fita
Engr da kansa ya shirya Nilam suka sauko downstairs nan Amir da Aiman suka nufosa a guje suka rungumesa good morning daddy suka fadi rungumesu yayi yace good morning my boys how was your night Amir yace daddy were missing Patricia so awfully arent she coming back to us
Engr ya zaunar dasu bisa dinning yama rasa me zaice ma yaran nasa Amm na tsaye tana kallonsu daga stirs tausayin dan nata ne ke damunta a bangare guda kuma laifinsa take gani kwata kwata baison bacin ransu ya sadaukar da farin cikinsa garesu ya hakura da aure sabida yaransa basa so
Hajja cook dinsu ne keta faman jere abincin bisa dinning din bayan ta gaida Engr A gurguje yaran suka gama karyawa dan sun kusan makara Engr Kuwa da kansa yayi feeding Nilam dinsa Saida ya tabbatar sun shige mota driver yaja su zuwa sch kafin ya dawo danyin nasa break din
Zaune ya tarar da Amma bisa dining da alama dawowarsa take jira Gaisar da Amma ya fara yi kafin ta soma zuba masa abincin Kallon Amma yake sosai yana son gano abunda ke damunta murya a hankali yace Amma na are you alright Kallonsa Amma tayi kafin ta tura masa plate din abincin tace am fine son kaci abinci zakayi lattin office kasan bai kamata shugaba yana latti ba
Hannunta Engr ya riko cikin nasa kafin yace pls Amma tell me is something bordering you You seems quite depressed
Amma ta gyara zama tace Nazif to be honest with you halin dake ciki ya fara isata this is too much Nazif yeah na sani kana son yayanka but that doesnt mean you cant be happy youre a human Nazif a iya sanina kai lafiyayyen namiji ne wanda ko wani na miji me lafiya na bukatar mata Im your mother and Ill not goin to allow you to ruin your life just like that Da mugun mamaki Engr ke kallon Amma bata taba masa magana makamanciyar haka ba gyara zama yayi kafin yace Amma what you thought of me was wrong yeah precisely abunda kika fadi gaskiya ne duk na miji me lafiya na bukatar mata but to Amma matar da nake so na kasance da ita guda dyace FATEEMA ce you perfectly knew that so ever since I lost her wani maganan soyayya ya fice daga raina aurena da Khadija rabon yaya ne and I ason yaran nan with all of my heart Fatima ta rasu Khadija ma ta rasu Amma keda yarana youre my only family babu abunda ya rage mun yanzu a rayuwa bayan naga na kyautata maku I Devoted my entire life to you and my kids Amma so pls ki daina kawo mun zance aure kinji Amma
Girgiza kai kawai Amma tayi cike da tausayawa danta Nazif a tare suka gama cin abinci da Engr kafin ya fice zuwa Company

_Around 230pm_
Nilam kwance jikin Amma tana ci gaba da kuka taki yarda da kowa sai Amma harta Nadiya ma taki yarda da ita Kaman daga sama tajiyo sallaman Larai da mamaki Amma ke kallon larai har ta karasa shigowa Amma ta sake baki tace Larai dama zan sake saka ki ido na Anty larai na murmushi ta karasa ta tsuguna kan makeken carpet din Turkey dake baje a tsakiyan parlorn tana fadin sannu Hajiya Amma ina nan wllhi ai tunda kika koma America shiknn sai satin bayan can nake ganinki gidan wani rasuwa alabarai shine nace ai ya zama dole na nemeki na gaisheki Amma tace ayya aiko na gode sosai larai Nan fah aka soma gaisawa tareda hiran yaushe rabo
Anty Larai ta mikama Nilam hannu tace yaki yan mata Nilam ta ake kafadu alamun oo Amma tace rigima takeji dashi wai me raininta da muka taho da ita daga America ta koma tofa shine duk wnn rigimar Anty Larai tace ayya halan yar gidan karamin Alhaji ne haka take kiran Engr Nazif a da lokacin da take aiki ma Amma n sa Amma tace eh ai itace autarsa mahaifiyar tasu ta rasu lokacin muna can Amurkan toh bayan rasuwarta ne muka dawo gaba daya Anty Larai tace ayya Allah yayi mata rahama Amma ta amsa da amin
Larai nace yanzu a ina kike aiki Amma ta tambaya
Anty Larai tace ai tun bayan tafiyarku Hajiya am na soma aiki da cibiyan goya marayu a can nake aiki yanzu kuma nice shugaban fannin kula da yan mata Amma tace ayya Allah ya taimaka Sun jima suna hira maaikata suka cika gaban Anty larai da kayan ciyeciye iri da kala wnn dabia na karrama bako wajen Hajiya Amma har yanzu na nan bata damu ko talaka bane ko me kudu yan adam du daya ta dauka
Koda Larai ta tashi tafiya sosai Amma ta cikata da kayan alheri snn sukayi musayan lambar waya akan ko tana neman wani abu koda na maaikata ne zata nemeta Sosai Amma taji dadin ziyaran da Larai ta kawo mata

Yau tana zaune tana tunanin ta aina zaa samo ma yaran nan Nanny dan kuwa fitinan yan biyu da Nilam ya isheta ita ga shekaru yaja ba komai zata iya da fitann su ba shi kuwa babansu yaki zancen aure
Tunanin Larai ya fado mata nan ta kirata ta tambayeta ina zata samu Nanny matashiya me hankali da nutsuwa da sanin addini sabida rayuwar jikokinta ya inganta Nan Anty larai tace bazai gagara ba zaa bincika inshaAllah da Alkawarin idan an samu zata jita sukayi sallama

MM BUILDERS
Yana zaune cikin Office dinsa fuskansa sanye da faran tabarau na kara karfin gani yana sanye cikin white long sleeve shirt irin wanda ake daura suite a sama sanye yake da bakar wando na suite din Files ne gabansa sai bincikasu yake yi wayan dake gefensa ne yayi distracting dinsa A hankali cikin nutsuwa ya daga kafin ywce yes Jane whats this Jane sakatariyan sa tace Sir you having a visitor she says you have an appointment
Da mamaki Engr yace appointment and you said its alady
Yes sir may I let her in
Kaman bazaice komai ba sai kuma yace send her in pls
Alright sir

Jane ta dubi Laila tace Miss you may go in now
Thank you Laila tace cikin kashe murya

Tunda ta shiga office din take binsa da mayen kallo shi kuwa har lokacin idonsa na kan takardun da yake dubawaOh mine Hes so cute and handsome haka Laila tace cikin zuciyanta dago ido Engr yayi yaga ta kafa masa ido tana sanye ciki riga da skirt na atampa wanda yasha dinkin wulakanci matashiyar mace wacce bazata wuce shekaru 32 zuwa da 33 ba Ganin kallon yayi yawa yasa Engr yni dan murmushi ya ajiye biron hanunsa yace Miss may I knw who you are and what are you here for
Laila tayi saurin saita kanta kafin tace Oh good morning sir am Laila Maaruf Sarki ya gane surname dinta dan haka take ya sakar mata murmushi yace pls seat down yana me nuni da kujeran dake gefe
Zama tayi tana mayaudariyan murmushi tace thank you
So how may I help you Engr ya tambaya
Laila ta wani juya ido kafin tace kardai baka gane ni ba Murmushi ya danyi sanda yake cire glasses idonsa yace na gane sunanki ke diyar aminin mahaifina ne am I right Gyada kanta tayi tace ai nice wacce kazo min taaziyan rasuwar mijina kwanaki Da mugun mamaki Engr ke kallonta kafin yace toh me ya kawo ki nan kuma despite the fact kina cikin kwanakin takaban ki if am not mistaken
Murmushi laila tayi tana juya ido kafin tace yeah hakane amma ai babu wani aibu a ciki Da sauri Engr ya katseta kwarai akwai aibu haramun ne mace ta fita babu wani babban uziri ko na ciwo ko makamancin haka alhali tana cikin kwanakin takabanta yanzu abunda nake so dake ki tashi ki koma dakinki snn ki cire wnn ado da kikayi dan kin aikata babban haramun
Zuciyan Laila ya cika da mamaki ganin mutumin nan daga America ya dawi amma ashe har yasan addini haka Ta dan sha jinin jikinta kafin tace Oh dama daga asibiti na fito sai nace barin dan tsaya mu gaisa snn na nemi aiki a companyn nan dan kasan mijina ya bar mun marainiya
Engr yasha mur sosai kafin yace ki tashi ki tafi yanzu snn kiyi yanda nace what ever should be the case akan maganar aikin zamuyi shi daga baya mahaifinki nada every right gameda wnn company so no need to be worried about looking for a job here
Jiki a sanyaye Laila ta mike tace haka ne na gode da tunasrwanka nima bada son raina nazo ba Alhj ko kadan baison nayi aiki a nan company din tun tuni yanzuma idan yaji nazo he will very mad at me So pls Engr do me a favor he shouldnt know that I was here
Engr baice mata komai sai gyada kansa da yayi jiki a sanyaye ta fice ta dauka turai ya gogesa sosai ya zabi rayuwarsu bata taba tsammanin samunsa haka ba Cike da haushi da takaici ta fice daga Office din
Engr kuwa girgiza kai kawai yayi gamida tabe baki a hankali ya furta some people dont even know their obligations

Tana shiga gidanta ta shiga neman layin Hajiyanta Hajiya Karima tana dagawa tace yaya kuka yi Wani dogon ysaki Laila ta buga kadin tace Hajiya yanda na samesa banyi tsammanin samunsa haka ba dagani zamu sha wuya dashi wani guntun waazi ya tsaya yimin saikace badaga America tushen wayewa ya fito ba yanzu dai kawai kiyi kokari ki fito kizo gidana ni na gaji da wnn takuran wai shi takaba Hajiya tace kwantar da hankalinki ina nan tafe Bayan sun gama wayan ne taji muryan surkuwanta wato uwar marigayi mijinta tana sallama
Wani dogon tsaki Laila ta buga ko amsa sallaman ma bata samu zaradin yi ba Karshe har Yakumbo ta kare ta sako kai cikin parlorn Ga mamakin Yakumbo zaune ta samu Laila a parlorn ta kure sautin tv tana jin kida ga kwalliy uwa amarya a wajen biki cingam ne a bakinta sai faman taunasa take Mamaki ya hana yakunbo furta koda kalma guda

QueenSamy ce

Mallakin waye 06

_Written by QueenSamy_

Mamaki ya hana Yakumbo furta koda kalma guda sallalami ta shiga yi tana tafe hannu sanda taga Laila ta dauko waya ta maka a kunne tana fadin hello sweetyna kanajina wllhi nima tsananin sonka kar ka damu mun kusa zama karkashin inuwa guda Yakumbo bata gama jiba ta shiga rera kuka tana fadin Yanzu laila mijin nakai ko wata guda beyi da mutuwa ba shine kike zancen aure da wani A hasale Laila ta mike tana fadin Would you stop backing like a dog kinzo sai cika min kunne kike kamar wata kariya ke barin fada maki karkiga da ina ragar maki dan ina auren danki toh yanzu abunda ya hada ya raba ki wuce ki fice min a gida tun kan ranki ya baci Sosai abin yabawa Yakumbo tsoro lallai abunda ake fadi akan Laila gaskiya ne Twasawn da Laila ta kuma daka mata yasata saurin dawowa hayyacinta zaki wuce ki fita ko saina fitar dake da karfi Aa me yayi tsanani zan fice daidai nan Hajiya Karima tayi sallama ta shigo kallon hadarin kaji Hajiya Karima tabi Yakumbo dashi kafin tace Dan nasuma ya mace bazasu barki ki huta da jaraban tsiyaba tayi maganar tana duban Laila tabe baki Laila tayi tace wllhi ko Hajiya dama isowarki nake jira wnn matan tazo sai cikani da hayaniya take Yakumbo ta girgiza kai kafin tace Karima ku kiyayi duniya keda diyarki A hasale Laila ta matso ido a tsefe take duban Yakumbo kafin tace Ke tsohuwar banza karki yarda ki gaya wa uwata magana dan yanzu zan iyar watsar maki da hakora a nan Hajiya ta rikota tace kyaleni da ita ni na isheta gyalen kanta Hajiya ta cire tace Shege ka fasa Girgiza kai kawai Yakumbo tayi kafin tace ni bazanyi fada daku ba ai kun tari fada da wanda ya fi karfin kowa yake iko da kowa wnn fada kuka tara da mahallicin mu tinda shi ya diba wa mace kwanakin da zatayi na idda kunga kuwa dan kunce zakuyi fada dani ai bana mamaki ba duniya tsaf xata koya maku hankali dan kuwa _Tafi gabaruwa iya jima_ Dangin mayu kwadayayyau ana jira uban yata ya mutu aci arziki toh sai dan naku ya riga mutuwa babu yanda zaku sami gadon yata shine kuke bakin ciki da hassada dan mayunwata idan banda kaddara da rabo mema zaisa yata ta auri danki Cewan Hajiya cikin masifa da balai shigowan Aziza ne tana sanye cikin uniform din makarantar ta yasanya Hajiya yin shiru Da gudu Aziza ta tafi ta rungume Hajiya tana fadin Hajiyata yaushe kika zo Hajiya ta wani rungume Aziza tace diyar Hajiya an girma an kusa zama yar jamia ko aure zakiyi Aziza ta tsoke baki tace Tab wani aure ai sai naci duniyata da tsinke ko yaya kikace mumYakumbo na murmushi tace yaki uwata wani harara Aziza ta wurga wa yakumbo kafin tace Mum tace ke mayya ce ke kika cinye daddy na ki fice mana a gida kafin muma ki cinyemu Da mugun alajabi Yakumbo ke kallon Aziza wasu hawayen takaici na zubo mata Girgiza kai tayi tasa kai zata fice Hajiya tace wuuu ashe abin haka ne toh kuwa kurwan yata da jikata kur kije can ki karaci maitanki gwara da Allah yasa ya tsaya akan danki dan kunfi kusa Yakumbo kam bata iya karasa jin zantukansu ba dan kuwa juwa ta soma gani wnn shine a dake ka a hanaka kuka

1 thought on “Mallakin Waye Hausa Novel”

Leave a Comment