Tantiranci ko karuwanci hausa novel

Tantiranci ko karuwanci hausa novel

 

TANTIRANCI KO KARUWANCI

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa Rahma Muhmd Rufai Nal

Page 1

Alhamdulillah Alhamdulillah nagodema Allah daya bani ikwan dawowa ya bani damar kawo muku wannan labari nawa wato TANTIRANCI KO KARUWANCI
Yanayin me daukar hankali ne Tafiyar abar dubawa ce Karatun abin tunani ne Ina san nayi amfani da Wannan damar wajen rokwan masoya littattafaina wato AN MATA wayanda nayi musu ba daidai ba kan SAMAREEN BANAH part 2 da LEEKITAN ZUCHIYA dana hanesu karantawa Toh ga dama tazo gareku Zanso kubude kunnuwanku da ware idanuwanku dan Wannan littafin mallakinku ne Na sadaukar dashi ga duk BUDURWAR da zata karanta Sannan Inayi muku fatan kukai qarshensa da lafiya Kamar yanda kuke yimin adduar gamawa cikin nasara Rahma nalele dai takuce yan hannuna Auntyn luv

Waige waige yakeyi acikin layin nasu Sam bazai wacce shekaru ashirin da biyar ba Yaro ne kyakkyawa ajin farko wanda kallo daya zaka mai kasan ya hadu tako taina
Ya tara abubuwa kamar hakaTantiranci Wayewar zamana Ilimi Iya wanka
ABDUL DAN KASADA kenan me karatu
Abokansa ne suka sakamai wannan sunan ashekara biyu kadal kuma ya bishi

ABDUL ya rasa abubuwa uku arayuwarsa
Ya rasa soyayyar Mahaifiyarsa da yan uwansa
Sam mahaifiyarsa Mama Saude bata qaunarsa arayuwarta Bata da abun qi kamarsa a rayuwa
Tunda ABDUL ya tashi bai taba ganin ranar daya zauna shida ita sukayi magana irinta uwa da da ba
Kullum cikin cikin hantaransa take da nuna masa tsana Kai baqin hali dai iri iri ba wanda ABDUL baya gani agun Mahaifiyar tasa
Kaf cikin gidansu da unguwarsu ba wanda baisan da zaman qiyayyar da Mahaifiyar tasa take masa ba Hatta abokansa suna mamakin irin tsanar da Mahaifiyar tasa take masa
ABDUL yana da aboki AMEER
AMEER layinsu daya da ABDUL
Saidai AMEER iyayansa masu kudin gaske ne Sam bazaka taba hada gidansu AMEER danasu ABDUL ba
Saboda gidansu ABDUL shine gidan talakawa na biyar acikin unguwar tasu

AMEER tun tasowarsa arayuwa yake da rashin ji Sam AMEER baya ganin kowa da gashi
Ya rigada yayi suna wajen rashin mutunci
Ga satan kudin iyayensa da shaye shayen tsiya dabin mata kamar dan akuya
Sam bazakiso hada Yarki aure da AMEER ba
Gashi su biyu kacal iyayensu suka Haifa shida qanwarsa Abida
Suna sansu suna qaunarsu shiyasa yake amfani da Wannan damar yake iskancin dayaga dama

Azahirin Gaskiya iyayensa suna matuar qoqari kan ya kintsu
Dan basu san halaiyarsa kaf Dan ko kadan baiyiyo halinsu ba
Kasancewarsu nagari Kawai sun yarda bata yanda Allah baya jarabtar bawansa
Hakan yasa suke mai addua babu dare Babu ranah

Bambancin rashin jin AMEER da ABDUL abu biyu ne
Sam shi ABDUL baya bin mata baya aikata zina Sannan idan abinka zaikai shekara agaban ABDUL bazai taba daukar maka shi ba Maana anan baya sata baya aikata zina
Saidai fa duk rashin mutuncin AMEER ABDUL yafishi Dan shi idan yace yes baya dawowa yace no
Idan yace saiya aikata abu to Wallahi saiya aikata kodako abin nan zai kaisa ga caji office ne
Sam ABDUL bashi da tsoro

Gidansu ABDUL gidan yawa ne gidane irin gidan family house dinnan
Akwalla ba akasara ba yawan mutanan gidan zasukai su dari
Gidan babban gida ne wanda yayi suna acikin unguwar Suna kiran gidan da GIDAN YAWA Saboda tsabar yawansu

Alhaji Ali me katifa shike da mallakin gidan
Yana da yara Ashirin da daya aduniya dukkansu maza
Kuma kaf dinsu sunyi aure kuma agidan suke zaune da matansu da yaransu Kasancewar gidan babban gida kowa idan yatashi auransa yankan wani shashi yake anan cikin gidan ya gina ya zauna da iyalinsa

Mama Saude a ce ga qanwar Alhaji Ali yar autarsu Amma ta rasu shekarun baya da suka wucce wajen haihuwan qanwar Mama Sauden wato ZAINAB

Toh tunkan Mahaifiyar tata tarasu Alhaji Ali yake san Ya mace kasancewar duk yaransa Ashirin da dayan nan duk maza ne
Hakan yasa ya dauki Saude tun tana qarama ya kawota gabansa wajen matarsa Hajjiya Ladi wacce kaf yan gidan suke kiranta da Hajjiya Kakah
Ita ta raineta har takai munzalin aure sai alhaji Alin ya Aurar da ita ga dansa Shehu
Shine suke zaune suma agidan har tasamu cikin ABDUL ta haifesa wanda tunda ta haifesa take nuna masa tsana dan qiri qiri qin shayar dashi tayi Wai nononta nayi mata ciwo idan takai masa nonon bakinsa jitake kamar kan nononta zai gutsire Jin hakan sai Hajjiya Kakah ta dauki ABDUL tashayar dashi da madara irin ta yara kamarsa awannan lokacin
Kowa agidan Gani yake anya kuwa Saude itace ta haifi ABDUL
Saboda sunga yanda take nuna mai tsana da tsangwama kala kala

ABDUL ya tashi a nutse bashi da kwaramniya irin ta yara marasa ji
Saidai daga lokacin dayakai shekara Ashirin da uku aduniya daga lokacin ABDUL yazama TANTIRIN dan iska Ammafa injisu da fada saidai me karatu kagyara zama muji shin da gaske ne ko akwai sabani cikin maganar tasu

Lokaci daya kuma ya juye yazama hakan
Saboda tunda ABDUL ya gama karatu zai fara aiki a companyn abokin babansa wato mahaifi ga abokinsa AMEER kasancewar business ya karanta shikenan fa kamai ya jagule ma ABDUL din alokacin
An rasa tayaya meyasa hakan yajuye masa

Bashi da abokanaye sai yan iska Yan daba Yan shaye shaye masu jaye jayen magana
Masu aikata lefuka TANTIRAI dai kawai
Toh alokacin ne AMEER ya kulla abokantaka da ABDUL kuma ABDUL ya yarda

Hajjiya Kakah tatara malamai kan suyi mata istahara ko Allah zai basu haske kan lamarin nasa Sai malaman suka bata tabbaci akan asiri akama ABDUL din kuma wallahi mugun asiri ne
Makaryar asirin shine ranar da zaa daura ma ABDUL din aure
Dazaran an daura masa Aure to ba makawa wannan asirin ya karye kenan

Tunda Hajjiya Kakah taji hakan hankalinta ya tashi dan tasan me dai hankali bazai taba daukar yarsa yaba ABDUL ba
Nan tashiga ba ABDUL magungunan tsari da karya sammu amma kamar bata basa dan ba abinda yake canjawa

Saita fara kici kicin neman wacce tadace dashi a dangi
Saidai kaf iyayen yaran da sunji zaa hada yayansu Aure da ABDUL nan suke tsalle su dira suce su bazasu yarda a daurama yaransu aure da ABDUL ba
Saboda sunyi duba da yanda TANTIRANCINSA yake qara habbaka

Lokacin da mahaifin ABDUL yaji wannan batu har kuka sanda yayi saboda baqin cikin abin da sukace
Amma daga baya dayayi duba da irin tsanar da Saude Mahaifiyar ABDUL din da take masa saiya share komai Dan Inda ace bata nuna tsana agaresa da zasuji kunyar fadin hakan
Danshi dai kaf cikin yayan nasa bashi da abinso kamar ABDUL din
Kullum cikin yimai adduar kintsuwa yake Tare da yimai nasiha akan ya kintsu
Saboda har sakin Saude yayi kan tsanar da takema ABDUL danta dena ta yantar dashi kamar yanda ta yantar da sauran yaranta amma taqi Haka dai Hajjiya Kakah ta bashi hakuri ya maida ita dakinsa awannan lokaci

Sam Hajjiya Kakah bata dena nemama ABDUL maganin tsari ba Haka adduar babu dare babu rana haka take mai kan Allah ya karya lamarin dan tasan tunda dangi suka hanata yayansu danta aurama ABDUL din tatabbatar bare dai bame bata yarsa danta Aura masa asirin ya karye

Tunda asirin ya kama ABDUL shikenan ya dena ganin mutuncin kowa agidan saina Hajjiya Kakah da mahaifinsa da qanwar mahaifiyarsa wato AUNTY ZAINAB

AUNTY ZAINAB qanwace ga mama Saude idan me karatu ya koma baya kamar yanda na fada muku

Mama Saude tana da shekara goma sha biyar aduniya aka mata aure
Kuma tana shiga dakin nata tasamu cikin ABDUL
Lokacin data haifi ABDUL lokacin shekarun ZAINAB qanwarta biyar aduniya
Dake ZAINAB itama Alhaji Ali ya dawo da ita gun Hajjiya Kakah saiya kasance tunda ZAINAB ta qilla ido taga ABDUL sai taji ba wanda take so kamarsa
Bini bini tana naniqe da ABDUL
Tun a lokacin kowa agidan ya fara mamakin qaunar da ZAINAB takema ABDUL
Idan taga ABDUL na kuka nan itama zata hau kuka wiwi har sai Hajjiya Kakah tayi nasarar shawo kan kukan ABDUL din

Toh wannan shine silar faruwar shaquwar ABDUL da ZAINAB AUNTYNSA

Tunkan ABDUL yayi wayo yasan ZAINAB me qaunarsa ce

ZAINAB bata iya san abu ba arayuwarta Dan idan tatashi san abu sanshi take gabaki daya kuma da gaske
Haka kuma bata iya qin abu ba Idan taqi abu taqishi kenan har abada

ZAINAB tana matuqar jin tsanar ar uwar tata mama Saude aranta
Saboda qiyayyar da takema ABDUL shine dalilin dayasa itama take jin qiyayyarta aranta

Hankalin ZAINAB yayi matuqar tashi dataji wani sirrin Yar uwar tata akan ABDUL Wannan yasa taqara qaunar ABDUL a ranta da qarin jin tsanar Yar uwar tata

Tunda mama Saude tagane qanwar tata taji sirrin nata shikenan suka samu rashin jituwa
Dama ita ZAINAB tanajin qiyayyar yayar tata akan tsanar dataga tana nunama ABDUL din
Saidai koda wasa bata taba nuna mata afuska ba
Sanda taji wannan sirrin nata tukunna tadena ganinta da mutunci tafito da tsanar da take mata afili har kowa ya gane hakan

Mama Saude ranta na baqi da yanda ZAINAB din tadena ganin mutuncin nata
Saidai ta share tunda ta gane barazanarta tayi tasiri akan ZAINAB din dan gaya mata tayi idan har tatona mata asirin nan nata kowa yaji ya sani wallahi saita kashe ABDUL kotawata hanya saidai itama a kasheta

Jin hakan shiyasa ZAINAB rufa mata asirin saboda tatabbatar a irin qiyayyar da Sauden takema ABDUL din ba makawa zata kashe shin Saidai ko a kashetan dan Wallahi zata aikata hakan kamar yanda tace

Ita kuma tana qaunar ABDUL din dan duk wani abu dazai taba mata ABDUL din ya shiga damuwa ko ciwo ya kamasa ba sanshi take ba hakan ne yasata yin shuru da bakinta kawai tazubama sarautar Allah ido dan tasan dole Allah saiya tona mata asirin da bata san kowa yasani

Hakan ya faru ne ana saura wata biyar Auran ZAINAB din
ZAINAB takamu da san wani Salisu dan gaye haka Yana santa sosai kasancewarta abin san kowane da namiji
Danta kasance kyakkyawa ajin farko Tatara duk wani abu da da namiji yake so ajikin mace
Farace sul sul gwanin ban shaawa

ABDUL yakan zauna yata kallanta lokacin yana qarami yace Wai AUNTY ZAINAB dani dake wayafi wani kyau ne
Murmushi kawai take yi dan shi ABDUL wankan tarwada ne bazaka kirasa fari ba kuma bazaka kirasa baqi ba
Kalansa abinso Ga fatarsa kogaggiya dan gaskiya mahaifinsa yayi qoqari sosai wajen ganin ya kyautata rayuwar ABDUL din
Dan sam ABDUL ba abinda yake nema ya rasa agun mahaifin nasa
Daga kayan sawa na wanka irin na yaran zamani kudin makaranta har dan dai kudin kashewa ba wanda ABDUL yayi missing arayuwarsa har yagama karatunsa yasamu nasarar amshe takaddarsa cikin nasara
Gashi dai bawai suna dashi bane kawai wadatar zuci ne irin na mahaifin nasa da qaunar da yake masa
Haka wajen Hajjiya Kakah bata yima ABDUL rowar duk wani abu nata naci da yayanta suke bata
Dan haka sam ABDUL bai tashi ta kwadayi irin na yara ba

 

ZAINAB sanda ta Auri Salisu tagane tantirin dan iska ne manemin mata dan shaye shaye
Tayi kuka tayi kuka lokacin data gane hakan
Saboda tasan bazata iya rayuwa babu shi ba
Dan tana mai wani so ne wanda yafi qarfin akirasa da MASEEFAR SO

Baya dawowa gida sai qarfe goma sha daya ko sha biyu na dare
Sannan abuge yake dawo mata
Wani lokacin ya mata dukan tsiya idan tana masa fada kan yadena abunda yake yi Sai yace wai tayi mai rashin kunya dan haka sai ya hauta da duka
Idan washe gari tayi kuma saiya hau bata hakuri
Ahaka zaita lallabata har ta hakura

Ahaka ahaka har tadena hakuri da zaran ya daketa sai tayo GIDAN YAWA
Haka zai zo bikwanta idan yadawo hayyacinsa
Sam Hajjiya Kakah bata bashi ita saita ciccimishi
Daga baya tagane idan tana mai fada ran ZAINAB din na baci sai kawai tadena yimai
Idan ZAINAB din ta gudo cemata take tazauna idan yazo tafiya da ita tabishi ba saima tayi mata sallama ba

Sarai ZAINAB tagane gatse tayi mata amma bata damuwa dazaran yazo ko tana dan jamishi aji kadan ya lallameta Saidai Hajjiya Kakah tanemeta ta rasa tabi mijinta

_

TANTIRANCI KO KARUWANCI

_
Fadi alkairi ko kayi shuru
A true life story
Follow me on Wattpad rahamanalele

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa Rahma Muhmd Rufai Nalele

httpsmobilefacebookcomRealHausaFulaniWritersforumRHFWF173984973194167refid52refopera_speed_dial__tn__HR

Page 2

Sam Salisu bai qare ZAINAB da komai na rayuwa ba
Komai yanayi mata na rayuwa hakan ne yake sawa kaganta fes kamar wata yar tsana Fatarta kullum agoge take Tana dai jin dadin rayuwa na kayan more rayuwa
Matsalarta biyuce arayuwa Na farko shine bin matan da mijin nata yakeyi da shaye shayen daya keyi Na biyu shine rashin haihuwanta Dan yanxu haka watanta tara da auren nasu amma uwar mijinta dake bata santa haka tabi tasata agaba wai bata haihuwa dan maseefa kamar shekara taran tayi ba wata tara ba

___Wannan shine labarin ABDUL DAN KASADA da mahaifiyarsa Mama Saude da AUNTYNSA ZAINAB da kakarsa Hajjiya Kakah

 

Andawo labari

ABDUL na gama waige wai gensa ya fada gidan AUNTYN tasa ZAINAB kasancewar anan bayan layin nasu gidan nata yake sam gidanta baiyi nisa da gidan nasu ba

Da sauri ya fada falan nata da sallama sam bata jishi ba Sai hakan ya bashi damar boyewa cikin wani lungu anan cikin falan nata
Gam gagam Zainab taji ana buga mata ofar falan nata kamar zaa balla Da mamaki tafito daga kitchen dinta tana me yarfe hannu da qarema yan sandan biyu kallo daga sama har qasa tace Lafiya meya faru
Afusace daya daga cikinsu yaceABDUL DAN KASADA mukazo nema ABDUL Ta maimaita da mamaki Kana taciga da cewa Toh baizo nan ba
Kinga malama karki raina mana hankali Dama ance kece kike boyesa anan gidan To bari kiji idan kullum kin saba boyesa yau baki isa boyesa ba dan lefinsa me girma ne
Wallahi sai mun shiga koina lungu da sako nacikin gidan nan mun zakulo shi dan iska Yaro kawai

Dama na gaya muku arayuwar Zainab bata da abin so kamar ABDUL Kuma duk yanda kuke da ita idan zakaci mutuncin ABDUL nan zata saba maka Sun shaqu iya shaquwa ita dashi Kowa yasan da wannan shaquwar dake tsakaninsu
Dan haka nan take taji ranta ya baci da titsiyan da suka sakata agaba suna masu yi mata Dan haka cikin tabe baki tace Rainin hankali kuma na nawa Ainade da raina muku hankali Tunda nace muku baizo ba aisaiku ba wandanku iska ku qara gaba
Wane ma rainin hankali ne wannan zaku shigomin gida ina matar Aure kanku tsaye batare da sallama na baku izini ba Haka dukar takoya muku To Wallahi baku isa ku shiga koina acikin gidana kucajemin shi ba
Tunda wanda kuke nema nagaya muku baizo nan din ba
Baku da hurumin daza ku shigarmin gida ina matar Aure mijina baya nan kuhau cajemin shi haka siddan ba
Dan haka saiku qara gaba tunkan na kulla muku wani sharrin dazaku rasa aikinku dan kunsan ba wanda yakai mace iya sharri Bare ni kuma da nake matar aure wacce kuka fadoma cikin gida kamar wasu dabbobi Taqarashe zancan nata da turo dan kwalinta gaba alamar duk rashin mutuncin da suke tafe dashi nata yafi nasu Dan tasha zuwa wajen yan sanda ana artabu da ita akan ABDUL din Sam ZAINAB bata tsoran yan sanda

Da matuqar bacin rai sukace mata haka tace Tace haka tace
Rai bace suka ficce daga gidan suna masu cewa wallahi saidai in kwana zaiyi agidan amma indai zai fito suna nan suna jiransa akofar gidan nata
Jan tsaki tayi da cewa Aikin banza Tana fadin hakan ta koma falanta da zama kan kujera mecin mutum biyu tana meci gaba da cewa Wato shi ABDUL bazai dena jawoma kansa magana ba ko Wai har sai yaushe zai dena abubuwan nan ne
Kai amma mama Saude tacuci rayuwarsa Daga hannunta sama tayi daci gaba da cewa
Ina rokwanka ALLAH dakayi gaggawar warware Wannan kullin Kaifa kace muroqeka zaka biya mana buqatunmu Gashi dare da rana aikina kenan wajan rokwanka kan wayannan alamuran

ABDUL din dake inda yake boye fittowa yayi da nufota yana cewa Kici gaba dayi min addua MY AUNTY insha Allah zan zama yanda kike so
Kallansa tayi a dan tsorace dan bata san da gaske yazo gidan ba Taja numfashi da cewa Wai dama da gaske kashigo ne ban sani ba
Eh Har nayi miki sallama naji shuru alamar kina kitchen
ABDUL kama kanka fada kadena aikata abubuwan nan dan Allah
AUNTY zan dena insha Allah
Toh yanxu gayamin meya faru suka biyoka Kawai AUNTY kishare Idan naqi sharewa fah Wai har sai yaushe zaka gane raina na mugun baci idan naga ka aikata wani abu wanda akema kallan Allah wadai Har sai yaushe zaka gane ina jin ciwo araina idan naga ankawo qararka ko anzo da niyar kamaka
Kallanta ABDUL yayi cikin wani hali yace Nasan kina jin bacin ran dajin ciwo aranki MY AUNTY Amma nima ina iya qoqarina wajen Ganin ban baki kunya ba Kuma nasan kema kinsan da hakan
Wata shegiyar harara ZAINAB ta galla masa da cewa Wane qoqari kakeyi ABDUL Kokarin baa cikakken sati sai anzo nemanka Koko qoqarin qara qirqiran tantiranci
Shuru yayi mata
Ganin hakan sai yasata jan numfashi da tashi taje ta duba abincinta tadawo kamar zatayi kuka taci gaba da cewa Dan Allah Dan Annabi ABDUL kaji tausayina ni me qaunarka Ka duba qaunar da nake maka kadena jawoma kanka magana
Kawar da kallansa daga gareta yayi da cewa Toh
Yauwa ABDUL kokai fah
Yanxu bani labarin me yasa suke nemanka
AUNTY kinsan bana gujema hukuma akan duk wani lefi da nasan bani na aikata ba
Kana nufin yanxuma kai ka aikata lefin kenan
Daga mata kai yayi akunyace
Murmushin yaqe ZAINAB tayi dacigaba da cewa Toh ina jinka meya faru
Wani Alhaji ne yazo wucce wajen majalisarnu shine fa ya wani fitto yana zaginmu wai yan iskan yara marasa tarbiya iyayenmu basu iya aihuwa ba Tunda suka haifa yan daba yan wiwi wayanda basu san darajar na gaba dasu ba Kawai AUNTY ki share dan yayi mana zagin cin mutunci Kinsan kuma ni bazan iya jurewa ba Musamman danaga ba abinda muka masa haka kawai ya fitto ya fara barar mana da kalamai Dan haka ina tashi na daga Addata da niyar sauke mai aka dan ya San dasuwa yake Amma sai Allah ya temakesa ya kauce nasamesa a kafada Yankan bai wani shigesa ba Dan haka na qara daga sandar na sauke mai a damatsan hannunsa Nanma naga bata shigesa ba Saina qara dagawa da niyar nayi mai me gabaki daya Sai Allah ya temakesa abokan nawa sukace in barsa haka saboda yarigada ya sume MY AUNTY
Shine fa muka tafi muka barsa agun Toh da alama jamaa sun gammu ne shiyasa yanxu da muke kan hanya dan zuwa duba AMEER jamian tsoran sukaso Ram damu Sai kuma muka ankare dasu Hakan yasa muka watse ni nayo nan
Jan numfashi ZAINAB tare da girgiza kanta hawaye ya zubo mata Aduk duniya ba macen datake jin tsanarta kamar Yayarta Saude mahaifiyar ABDUL din
Dan duk itace tajama ABDUL din wannan matsalar
ABDUL da ko jini yagani ajikin mutum yana zuba hankalinsa tashi yake Amma yanzu da kansa yake yankan mutum har yazo yana fada ba wani jin komai aransa

AUNTY kidena kuka nasan amin da ciwo ace yau naka ya lalace AUNTY nima bansan ya akayi nazama haka ba AUNTY ina tashi natsinci kaina cikin wannan balain Kina dai gani duk da iskancina bana wasa da ibada Kuma rokwan Allah nake kan ya dawo dani daidai yanda nake da danutsuwa dan kawai naga farin cikinki ABDUL yakai qershen zancen nasa da damuwa akan fuskarsa.

Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete

Goge fuskarta ZAINAB tayi dacewa Nadena ABDUL Kuma nasan duk abinda kakeyi badasan ranka kake ba
Nasan kasan baka kyautawa
Nidai fatana kadinga ragewa kadena kodan kaba maqiyanka kunya
Akan idona kwanaki Hajjiya Kakah taso yimaka aure da yaran dangi amma fur iyayensu sukaqi saboda wannan halin da kake ciki Kaga da ace kai nutsattsene ba iyayen da zasu qika Saboda katara komai da a mace take buqata agun da namiji

Kallanta ABDUL yayi da tabe baki yace Itama Hajjiya Kakah da rikici Banda haka miye nawani yimin aure ina qaramin Yaro haka tukunna mah Inkai matar ina
Kai wani aikin sai tsofaffi

Ita dai ZAINAB shuru tamai Danta fuskanci sam baisan meyake faruwa akan batun da ita tasani na yanda Hajjiya Kakah tagaya mata wai asirine yake dawainiya dashi ba

Tashi tayi taje ta sauke abincinta da zubomai tana mai cewa Kaga mutuniyarka nayi wato shinkafa da miya da salat
Aunty nifa bazanci ba harsai kingaya min dalilin dayasa Hajjiya kaka taso yimin aure batare da sanina ba Kumama wai acikin dangi Dangin da take da tabbacin basu sona
Haba ABDUL abinda nasani Shifa nagayama Zanqi gaya maka wani batu ne wanda ya dace kasani Ko kadan bansan wani dalilinta ba
Nayarda saidai kinsan bana cin abincin gidanki
Yauwa meyasa baka san cin abincin gidana Tunda aka kawoni daqer kakesan ruwan gidana
Kwantar da hankalinki bafa wani abu bane kawai naga mijin naki ne dan rainin hankali ne Saiya dingama mutane wani kallo haka haka Kamar wani abu nake zuwa yimasa agida
Wallahi kija masa kunne yadena yimin wannan dan iskan kallan idan ya ganni dake Idan ba haka ba toh
Idan ba haka ba tome ZAINAB tafadi atsorace Dan bata san iskancin ABDUL din ya taba mijinta dan tasan sarai idan yace zaiyima mutum abu Wallahi saiyayi hankalinsa yake kwantawa
Idan ba haka ba wallahi zan yanke masa kunne daya
Musamman idan ya qara dukanki shima saina nada masa na jaki Wallahi Haka kawai Dan iskanci saiya dinga garoki gida cikin dare kamar wata taya
Ba garoni yake ba nice nake zuwa dan ganin damata Wallahi Salisu bai taba cewa naje gidanmu Sannan dan Allah bani san katabamin lafiyar miji Dan wallahi idan naga kunansa a yanke narantse saina saba maka Sai nayi maka abinda baka taba tunani ba
Saboda kasan ina mutuwar san mijina ABDUL ina qaunar mijina kasan sarai ban iya so ba Haka ban iya qin abu ba
Karka aikatama mijina wani abun dazaisa naqika
Wallahi kozaki mutu idan ya aikata ba dai dai ba agabana saina mishi hukunci daidai da abunda yayi
ZAINAB najin hakan tasaka kuka wiwi Aiko yana ganin hakan yaci gaba da cewa kawai AUNTY ZAINAB ki matse Najenye tunda kina san abinki Amma wallahi kija masa kunne yadena yimin wannan kallan iskancin
Sauke ajiyar zuciya ZAINAB tayi da sakin murmushi tace Yau ce ranah tafarko danaga kafara sauke abu idan kadauka da zafi Eh yanxun ma dan naga kukanki ne To yanxu kabi ta kofar baya kaficce daga gidan nan tunkan suqara shigowa Dan kasan yau asabar Salisu yana dawowa iyanxu yayi wanka ya yayi gidansu daga nan ya wucce yawan nasa na fama
kuma kasan yana ganinsu zaune kofar gida ce musu zaiyi sushigo su caje gidan kasan tsoran yan sanda yake ba dan kadan ba
Tashi ABDUL yayi da murmushi yana cewa Sai AUNTYNA takaina Har abada bazan mance qaunar da kikemin ba Insha Allah shekaru masu zuwa idan nadena wannan abubuwan nayi Aure sunan yata tafari AUNTY ZAINAB
Murmushi tayi da cewa Allah ya kaimu lokacin ina maraba da zuwan little zainab Tana fadin hakan ne tana bude masa wata kofarta tabaya wacce zata sadasa da layin nasu cikin sauqi basai yayi wani zagaye ba
Ficce yayi yana tafiya irinta gogaggun tantirai dinnan
Murmushi kawai tayi da kulle kofar tadawo falanta da soma cin abincin data zubomai tana zancen zuci dayi mai fatan alkairi arayuwarsa

Can kuma saita fara tunanin karfa yayar tata tayi abinda tasaba yimai idan yan sanda na nemansa
Aiko nan tafara kallan agogo tana Allah Allah mijin nata ya dawo tayi gidan nasu

official Auntyn Luv

_

TANTIRANCI KO KARUWANCI

_
Fadi alkairi ko kayi shuru
A true life story
Follow me on Wattpad rahamanalele

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa Rahma Muhmd Rufai Nalele

httpsmobilefacebookcomRealHausaFulaniWritersforumRHFWF173984973194167refid52refopera_speed_dial__tn__HR

Page 3

Can taga kodai tadauki gyalanta taje ne Ita Wallahi bata san abinda zai dinga kai ABDUL hannun folisawa Dan haka daukar wayarta tayi takira mijin nata tagayamai yayi sauri ya dawo gida ba lafiya dan imba haka tace mai ba zabai dawo ba

ABDUL ko yana shiga gidan nasu shashin Hajjiya Kakah yayi Aiko tana ganinsa tarufesa da fada tana me cewa Me kuma yanxu yayi yan sanda sukazo nemansa a gaggauce
Murmushi yayi mata da fada mata komai daya faru sam ABDUL bai iya boye abu ba Idan dai katambayesa gaskiya zai gaya maka babu wani kunbiya kunbiya

Ai shikenan Ka kyauta Kaidai kam Allah yayi wadaranka Shegen Yaro me jaye kayen masifa da balai Ahaka zaka qare rayuwarka da yawan bel bel Yawan shaye shaye da aiki irin na yan daban Da rayuwa irinta qaskantattu Mama Saude Mahaifiyarsa ce me wannan furucin dan dama taga shigowarsa shine tabiyo bayansa taji me zai gayama Hajjiya Kakah Kamar yanda idan ya aikata wani abun take biyosa ta qare masa tanadi

Idan da sabo Hajjiya Kakah da jamaar gidan sunyi sabo da mugayen kalaman da mama Saude take gayama ABDUL sam ABDUL bai taba ganin ranar da mahaifiyar tasa tafadi alkairi akansa ba
Kuma idan zata mishi zagin duniyar nan da kalamai na bacin rai ABDUL baya taba bude baki yayi mata wani magana ko wani kwun kwuni
Dan shi gaisuwa ce kawai take hadasa da ita Idan ta amsa ya wucceta idan bata amsa bama ya wucceta

Ran Hajjiya Kakah ya baci kamar yanda ako da yaushe ranta yake baci idan mama Sauden tayima ABDUL mugayen maganganu na qara tabarbarewar rayuwa
Dan haka afusace tace da ita Amma ko ke Saude Allah yayi wadaran baqin halinki Anya kuwa ke kika haifi ABDUL da kike jifansa da mugayen maganganu Ni wannan abu naban ammaki dan ban taba ganin muguwar uwa irinki ba
Ai dama haka zakice mana Hajjiya Kakah Wannan dan burauban Yaro ne In banda jaye jayen magana ba abinda ya iya yi Sannan idan nazo ina yi masa fada kibi kihauni da balai Toh wallahi kamar yanda nasaba saina kira numbar yan sandan nagaya musu gashi ya dawo yana gida suzo su kamasa matsiyaci kawai Mama Sauden takatse Hajjiya Kakah da fadin hakan tana me warga hannaye gefe da gefe irin na mafadaciyar mace nan Sannan ta tazaro wayarta daga rigar mama takira numbar yan sandan da sukaje gidan ZAINAB dazu Dama idan hakan ta kasance tana da numbarsu Nanko tace dasu ga ABDUL din ya dawo gida suzo su kamasa suci ubansa da kyau

Nan mutanan gidan da suka firfito jin abinda yake wakana kamar yanda idan hakan tafara sukeyi Nan suka rangada buda da sheqewa da dariya suna masu cewa Sai Mama Saude Aikinki na kyau Irinki jamaa suke so mace me danqa danta ga hukuma
Sai suka kalli ABDUL Wanda dama idan hakan tafaru baya nuna komai ko ajikinsa dan yasaba da baqin halin uwar tasa Kuma ko ana ha maza ha mata yasan AUNTYNSA ZAINAB ko AMEER ko babansa ko Hajjiya Kakah ko maman AMEER zasu fito dashi Kai abokansu ma bazasu iya zama batare dasun fito dashi ba

Nan suka qaremai kallo da cewa Kaidai ABDUL kana shaaninka Dan koka aikata lefi ana fito dakai aikai dan gatan ZAINAB da Hajjiya Kakah ne Banda kai wazasuma hakan

Eh Ku fadi kanku tsaye ku qara da wayyo Idan zai shiga sau dari zamu fitto dashi sau dari
Nan gabaki dayansu suka juyo da kallansu game basu amsar Sunsan sarai sai ZAINAB itace me basu amsa daidai da kalamansu

Ta watsa musu wani mugun kallo hannayenta riqe da qugunta ta kalli yayar tata da wani matsiyacin kallo na nuna tsantsar tsana Kana tacigaba da cewa
Akwai ranar da nadamar duniya zata saukar miki akan baqin halin da kike nunama ABDUL kuma ranar bazata taba amfanarki ba Dan alokacin lokaci ya rigada ya qure miki Idan har ina raye ni dakaina zan hana ABDUL yafe miki
Da sauri ABDUL ya kalli ZAINAB da cewa AUNTY Mahaifiyata ce fah
Kowa agun sanda ya kallesa
ZAINAB tayi murmushin yaqe da cewa Eh Mahaifiyarka ce Amma ni kuma ai yayata ce
Kana da damar da zaka kanani fadin mata kalaman danayi niya ne
aa kawai dai gani nayi koda tayi min abinda yafi hakan zan iya yafe mata
Murmushin yaqen ZAINAB taqara yi da cewa Awannan ranah na tabbatar bazaka taba yafe mata ba musamman idan nace maka karka yafe matan
Zaiyi magana cikin sauri da fusata Mama Saude tace ALLAH ya tsareni da zuwan wannan ranah Har abada bazan taba Neman gafarar ABDUL ba Dan banga uwar uban abinda nayi masa Wanda zaisa namemi yafiyarsa ba
Kaji min yar iskar yarinya ba dama kizo kiga ina zartar da hukunci akan ABDUL saiki hauni da magana kamar wata saarki Wallahi kishiga taitayinki Kinsan dai banda uwarmu haihuwa tazo mata da Hutu kinsan ke saidai kizo aqanwata ta shidda
Kan ZAINAB tabata amsa saiga yan sandar nan sun iso gidan da Farin ciki
Ba bata lokaci suka tasa qeyar ABDUL suna masu godema Mama Sauden da jinjina mata Ita ko sai washare baki takeyi irin tayi abinda ranta keso
ZAINAB ta qara yimata kallan tsana taja tsaki da shigewa falan Hajjiya Kakah ta banko ofar falan a fusace Ji kake garam
Nan mutan gidan suka sheqe da dariya harda tafawa Kana sai kowa ta koma shashinta

Mama Saude ko zuwa wajen window na Hajjiya Kakah tayi ta labe kamar yanda tasaba atunaninta ko ZAINAB zata gayama Hajjiya Kakah wannan sirrin nata

Fansar Budurcina Hausa Novel

AMEER na zaune kan dining na falan Dadynsa yana cin abinci Sai wani abokinsu yakirasa ya shaida masa yan sanda sun tafi da ABDUL fah
Nan AMEER ya furzar da abincin dake bakinsa ya tashi jikinsa na rawa yahau tambayar me kuma ABDUL din yayi
Nan abokin nasu ya kwashe komai ya gaya masa
Aiko sai AMEER yayi jifa da wayarsa yana me kutuntuma ashar Fadi yake Wallahi qarya ne bazai yuhu ba
Akan wane dalili mutumin zai fito ya zagesu Sannan a kullemin ABDUL wallahi alhajin nan ya jama kansa balai Sai munje har gidan munyi mai balli balli

A rikice momynsa da Dady suka tashi daga kan kujerar da suke tare da qarasowa wajensa suna masu tambayarsa me kuma ya faru

Nan cikin raini ya kashe komai ya gaya musu

Toh bani san tashin hankali Kawai zansan yanda zaayi ABDUL din ya fito
Amma bani san kaje gidan alhajin ka dada jawo mana wata fitinar Dadynsa ya fadi hakan cikin damuwa Yana tuna tantiranci irin na ABDUL da AMEER
Kallan raini AMEER din yama Dadyn nasa da cewa Kasan ya tabo manyan yara Dan haka wallahi saina hukuntashi Kaima kasan baka isa hanani aikata abinda nace zanyi ba Yana fadin hakan ya dauki wayarsa da ficcewa daga falan zuwa cikin motarsa yana me neman numbar ZAINAB AUNTYN su

Suko da kallo sukabi AMEER din
Momynsa tace Kasan AMEER zai aikata abinda yace Dan haka ka hanzarta kaje ka fidda ABDUL din kasan shine kadai zai iya gayama AMEER yabar abinda zaiyi agidan Alhajin ya kuma barin Bacin haka kasan taurin kan AMEER ba Wanda ya isa dashi
Jan numfashi Dadyn yayi cikin tausayin kansu Kullum acikin tashin hankali suke tunda AMEER yayi wayo kullum cikin jamusu magana yake Kuma basu isa dashi ba Duk da cewar suna iya qoqarinsu na ganin sun bashi hakkinsa Wanda ya rataya akansu

Kumafa haka ne Dadyn ya fadi hakan da saurin ficcewa daga falan
Ita kuma momyn ta koma kan kujeta tare da godema Allah da qaddarar basu AMEER din da yayi matsayin da
Ahaka Abida tafito daga dakinta tasameta dan dama tana sallah ne lokacin amma taji komai daya wakana tsakaninsu da yayan nata
Ita dai bata san abinda yakeyi Shiyasa sam bata shiri dashi Amma tarasa dalilin da yasa take san ABDUL dan indai akansa AMEER yake hauka bata damuwa sosai

 

Anan ko hawaye Hajjiya Kakah tashare dacema ZAINAB Yanxu ya zamuyi kinga sun tafi dashi Wallahi bani san ya kwana acan
Itama ZAINAB din share hawayen tayi da bata amsa wajen cewa Yanda muka saba haka zamuyi Hajjiya Kakah
Kiran wayar AMEER ne ya shigo wayarta tadauka da cewa AMEER sun tafi da ABDUL
Yace mata Kwantar da hankalinki AUNTY ZAINAB yau dinnan zai fito
Murmushi ZAINAB tayi dacewa toh Kana takashe wayar

Yanxu zuwanka sitetion dinnan nawa DAN KASADA
Kallan DPOn folisawan ABDUL yayi da cewa 72 Sabain da biyu
Kallansa sosai dan sandan yayi da cewa Kadai tuna anya baikai sabain da uku ba
Wani daga cikin yan sandan ne yace Oga ina tayashi lissafi yau sabain da biyun ne kamar yanda yace
Ok kai shi ciki ka kulle yau dakwai cin kaza banqararriya
Dariya kowa acikinsu yayi kana sukayi ciki da ABDUL
Bayan sun kullesa sun dawo kallansu ogan nasu yayi daci gaba da cewa Anjima kadan zakuga baban AMEER din nan yazo fito dashi Kai yaran nan suna abinda suke so
Wani acikinsu ya amshe da cewa Suna kam abinda suke so Mudai fatanmu kakarbi kudi da yawa gunsa dan kasan konawa kacemai baka zaiyi
Ai kuyi shuru kawai Tunda nace muku yau akwai cin kaza ai akwai cin ne
Dariya suka qara sawa daci gaba da gwalmar Dadyn AMEER
Ahaka yazo ya samesu kamar yandako sukayi harsashe
Nan suka fara ciniki inda ogan nasu yake cewa Gaskiya alhaji lefin da yaran nan ya aikata wannan karan me girma ne
Dan Alhaji sabo yayima aika aika

official Auntyn Luv

_

TANTIRANCI KO KARUWANCI

_
Fadi alkairi ko kayi shuru
A true life story
Follow me on Wattpad rahamanalele

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa Rahma Muhmd Rufai Nalele

httpsmobilefacebookcomRealHausaFulaniWritersforumRHFWF173984973194167refid52refopera_speed_dial__tn__HR

Page 4

Dadyn yace Nidai yanxu koma miye kuyi hakuri Yaran yanxu ne mun haifesu bamu haifi halinsu ba Kuduba AMEER dana kuga duk danginmu baa taba yin TANTIRI kamarsa ba ko labari banjiyo irin hakan ba kowa yasan da zaman hali irin nawa dana mahaifiyarsa sam bai yiyo halin daya daga cikinmu ba to kunga ai dole sai munayi muna kai zuciyarmu nesa dan haka dan Allah kubani bellin ABDUL kamar yanda kuka saba
Zamu baka belinsa Alhaji kamar yanda muka saba baka dan mutuncinka da kuke gani amma dan Allah kudinga qara jamusu kunne dan ba abu bane me kyau ace kullum kaine wajen yan sanda Yanxu zaka iya bamu dubu Hamsin DPO ya fadi hakan da tsaida Kallansa ga Dadyn AMEER din
Shuru Dadyn AMEER yayi can yace zan iya baku indai zaku bani shi
Nan suka bashi takadda ya cike ya basu kudin sannan suka sako ABDUL

Dadyn yana tuqin motar tasa yana kallan ABDUL lokaci lokaci Can dai ya faka motar tashi kan hanya ya tsaida kallan nasa kan Abdul din yace Na rasa dalilin dayasa nake jin qaunarka cikin raina fiye da AMEER ina sanka ABDUL sosai cikin raina yauma bata canja zani ba zan wara rokwanka a karon babu adadi kan kagyara rayuwarka kozaka iya gyaramin rayuwar dana hakika ina rokwan Allah kan ya kintsar daku amma nasan yana jina kuma lokaci ya bani nasan zai kintsar daku Kasani nasani AMEER bayajin maganar kowa sai taka idan mukace mai gashi baya kalla amma idan kai kace mai gashi yana kalla nasani Allah ne ya doraka akansa dan ban taba ganin wanda AMEER yake so kamarka ba da wannan nake rokwanka daka kintsu ko shima zai kintsu AMEER yafika aikata abubuwan ashsha nasani dan ina kallo ina kuma ji ana kawomin qara kai idan ka aika tsiya kana dawowa kayi nadama kayi dana sani amma AMEER bayijin komai bare yayi nadama kai Yaro ne kin tsattse wanda kazama abin kwatance kaf fain unguwar nan tamu hankalina ya tashi matuqa danaga ka tabarbare lokaci daya dan Allah ABDUL ka dawo da rayuwarka kamar tada dan nasamu yanda nake wajen dana

Kallansa ABDUL yayi cikin jin tausayinsa hakika yana jin tausayin dattijan aransa yana san shi yana qaunarsa kamar yanda yake jin mahaifinsa aransa da kakarsa da kuma AUNTYNSA ZAINAB

Kaci gaba dayi mana addua Dady insha Allah zan gyara rayuwata albarkacin adduar da kuke mana Wallahi bana jin dadi abubuwan da muke aikatawa na kanyi nadama ayayin dana aikata Dady har kuka nakeyi cikin dare na rasa mafari na rasa dalili na rasa meyasa hakan ta kasance dani
Zan gyaru zan gyaru nayi maka aikawari Dadyna ABDUL yakai qarshen zancensa da zubda hawaye
Ai nan take qaunarsa taqara cafkar zuciyar Dadyn nan ya rungumesa yana cewa Nagode my son Allah yayi muku alkarka dena hawaye nasan zaka dawo yanda kake da yanxu kira AMEER ka dakatar dashi zuwa gidan Alhajin daka yanka dan yace saiyaje yayimai aika aika
Zare jikinsa ABDUL yayi batare dayace komai ba yahau kiran number na AMEER Yana dauka Yace dashi Dan uwa kashare batun zuwa gidan Alhajin nan pls dan baqaramin barma nayi mai ba

AMEER dake cikin motarsa bakin wani kebabban shago yana jiran abokansu su fito daga shagwan dan sun shiga siya masu kayan maye ne Sai kawai yaga kiran wayar ABDUL
Nan ya dauka bayan yaji abinda Abdul din yace mai sai yayi murmushi dacewa Saifa naje dan yasan suwa ya tsaya yana zagi
ABDUL yaja numfashi da cewa Tunda nace maka kashare ka share mana
Na share dan uwa
Yauwa to yanxu kana ina
Ina wajen shagwan Ali nasa su Abba tabare su siya mana harka
Yayi yanzu ina kan hanyata tazuwa gida kasameni cikin dakina
Ok babu matsala sai munxo

Sai ABDUL ya kashe wayar da kallan Dady yace Komai ya wucce Dady bashi ba zuwa gidan ka kwantar da hankalinka toh naji dadi my son Allah yayi muku albarka ameen ABDUL yace sai Dadyn yaja motar suka bar kan haryar

Akofar gidan nasu Dadyn ya saukesa Nanko ya shiga cikin gidan nasu dajin wani nishai irin yanxu akazo aka fitar dashi daga gidan yanxu kuma aka dawo dashi

Direct dakin Hajjiya Kakah yayi nanko yaganta ita da ZAINAB sunyi jugum amma suna ganinsa nan suka saki faraa ZAINAB tatashi da sauri takama hannunsa Saidai nan take tayi saurin sake hannun nasa shima cikin tsoro yajanye hannun nasa harda boyesa a bayansa
ZAINAB tace Jikinka shocking yakeyi ABDUL
Murmushi yayi da cewa aa Aunty nakine yake shocking din dan daga jikinki ya fito
Nan ZAINAB tahau kallan jikinta atsorace tana dube dube da cewa dan Allah da gaske kakeyi pls karka tsoratar dani
Murmushi ya qarayi da fain Toh jeki taba Hajjiya Kakah mugani
Nan tataba Hajjiya Kakah amma bataji komai ba hakan ne yasata sakin ajiyar zuciya ta hararesa da cewa kasan Allah na dauka da gaske kakeyi
Murmushi dai ya qara sakar mata da basu labarin Dadyn AMEER ne ya fito dashi Nanko suka dada yimai nasiha ya nuna yajisu dayin shashinsa mama Saude ta sauke labulan windanta zuciyarta cike da dakaicin yanda ana kamasa yake fitowa kwafa ta iya yi kawai dan ba yanda zatayi

Shiko ABDUL bayan ya shiga dakin nasa fadawa kan katifarsa yayi Wanda take yashe a qasa kan kafet dakin natsaf dashi irin na mazaje masu tsafta Ba komai a dakin daga katifar sai kayan kallo sai durowa sai tarin littattafan addini dana turawa komai dai a kintse tsaf gwanin ban shaawa Kafet dinnan tas dashi sai tashin kamshin daki yake
Nan yaja wayarsa ya bude data dan yaga wata wainar ake toyawa a yanar gizo saidai bai kaiga nisa a dube duben nasa ba wani wan mahaifinsa me suna Baba Shehu mafadici suna kiransa da Baba Nan ya banko ofar ABDUL din afusace kamar zai tashi sama yahau ce dashi Kai dai kam kai dai kam anyi yaran banza yaran hofi mara mutunci wanda baisan mutuncin mutane ba yanxu ba wanda ya isa ya gaya maka kenan kaji lokaci daya ka maida kanka dan iska dan burauba me shaye shaye tantiri angaya ma yanxu rayuwar dakasa agaba rayuwace me kyau kabi ka raina kowa baka ganin kowa da gashi dan tsabar tantirancewa to wallahi bari kaji nagaji dajin magana akanka atareni kan hanya ana gayamin duk randa kaqara aikata wani abu Wallahi saika bar gidan nan dan ba gidan ubanka bane gidan ubanmu ne cewa yayi kowa ya yanka ya gida babamu yayi ba bare kace gidan ubanka ne Idan ka gagari kowa ni bazaka gagareni ba Yana fain hakan ya juya ya tafi afusacen yana meci gaba da surutan takaici

Cije bakinsa ABDUL yayi cikin bacin rai yake cewa a bayyane Ammafa mutumin nan ya raina ni ya dace na gyara tunaninsa dan yasan dawa yake yasan ABDUL din daya sani da bashi bane yanzu Yana zuwa nan a zancensa yayi shuru yana tunanin wane hukunci ya dace yayi masa dan yasan TANTIRANCINSA ba irin na yara qanana bane

By AUNTYN LUV

_

TANTIRANCI KO KARUWANCI

_
Fadi alkairi ko kayi shuru
A true life story
Follow me on Wattpad rahamanalele

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa Rahma Muhmd Rufai Nalele

httpsmobilefacebookcomRealHausaFulaniWritersforumRHFWF173984973194167refid52refopera_speed_dial__tn__HR

Page 5

Yana cikin tunanin ne AMEER ya shigo shi da wasu abokansu biyu
Dan uwa naso naje na daddatsa alhajin nan Wallahi AMEER ya fadi hakan yana me kwanciya kan katifar ABDUL din
Kawai ka share dan uwa idan halinsa ne zai sake mana wata ranah ai Ni yanzu Kasan waye nake san nayima balli balli ABDUL yakai qarshen zancensa da maida hankalinsa gabaki daya ga AMEER
Murmushi AMEER yayi da cewa aa saika fada
Wannan yayan baban nawa mana Baba Shehu
Wallahi AMEER yau ina san namai balli balli yanda idan na hada ido dashi saiya sunkuyar da kansa
Dariya abokan nasu sukayi har suna hada baki wajen cewa Ai dama ya dace kayimai tun da dadewa Idan mukayi duba da yanda yake shiga maka hanci da duqunqune ya dace ka facoshi dan kagyara tunaninsa
Murmushin mugunta AMEER yayi da cewa Kuje ku sace mai shi kukaisa dakin tsaro dan dama ni haushinsa nake ji
ABDUL yace Hakan yayi sosai Maza kuje dan yau ina san ya gane shayi ruwa ne
Aiko ba musu abokan nasu suka ficce dan aiwatar da abinda sukace masu
Nan ABDUL da AMEER suka dinga hirarsu irinta abokai irinsu Zasu sha kayan maye ne ABDUL yaji ankira sallar laasar dan haka da qarfi da yaji ya hana AMEER shan kayan mayen yace sai sunje sunyi sallah

Jamaa dadama suna mamakin TANTIRANCIN ABDUL Dan duk tantirancinsa baya wasa da sallah Dashi ake sallah a masallaci
Idan kaganshi da AMEER a masallacin to dama katabbatar shine ya saka AMEER din agaba dan shima yayi sallar akan lokaci

AMEER yafi ganewa tarukus sallat
Ya hada Azahar da laasar magrib isha
Toh yanxu dai ya dan fara ragewa Saboda dorasa kan hanya da ABDUL yake

Bayan an idar da sallah abokan nasu suka sanar dasu kan sunfa kama Baba Shehun Yana can dakin tsaron nasu
Toh ABDUL yace musu kana suka koma dakin ABDUL din suka dan maki kayan shaye shayen nasu suka bilgire
Basu suka tashi ba sai lokacin sallar magrib

 

Qarfe taran dare ABDUL ya nufi dakin tsaro Dakin tsaro wani daki ne da AMEER ya ware musu nan cikin gidansu ta ofar baya
Anan suke hukunta mutanan da suke musu shishshigi cikin alamuransu
Suna shiga da mutum cikin dakin ne bayan sun fitar dashi daga hayyacinsa
Haka lokacin da zasu fitta dakai nan ma saisun fitar dakai daga hayyacinka Dankarka gane inda aka kawoka

Ahankali AMEER ya bude dakin da shiga cikinsa
Baba Shehu ne zaune daure jikin wata kujera anrufe idansa da wani yadi Sai mutsul mutsul yake alamar yana san kunce kansa

Murmushi ABDUL yayi da qarasowa garesa ya kunce mai yadin da suka daure mai idon
Aiko nan Baba Shehu ya kalli ABDUL da mamaki yana me qarema dakin kallo Tas dakin yake dan har da gado da kayan kallo da toilet aciki dakin dai yayi kamar na ajiye baqi
Shidai yasan bayan ya gama zagin ABDUL kasuwa ya nufa Saidai yana kan hanyarsa ta dawowa ne ya karyo kwanar layinsu dake wajen ba cukowar mutane sai kawai yaji an makesa aka Toh shine bai tashi tsintar kansa ba sai anan ido lullube

Da qarin mamaki yace Kai dan ubaka me nakeyi anan Waya kawoni nan Me zaka min nan din
Janyo wata kujera ABDUL yayi da wata zanbadediyar dodunarsa a hannu ya zauna yana me kallan Baba Shehun yace Nagane kai idan katashi tambayar mutum baka masa tambaya daya saika jera mai uku masu maana daya
Amsar daya ce kawai nasa yara sun kawo min kai nan ne dan in gayama fadanka gareni yayi yawa
Cikin mamaki Baba Shehu yace Ni zaka nunama TANTIRANCI Abdullahi Ni wan mahaifinka wanda muka fito ciki daya Ashe TANTIRANCIN naka ya shahara haka ban sani ba

Tashi ABDUL yayi da fara tsula mishi bulalar nan da farko yaso nuna jarumta irinta iyaye Daga bisani kuma dayaga bazai iya jurewa ba kawai sai yahau ihu yana neman temako amma ABDUL bai sarara masa ba
Fadi yake Wallahi na tuba bazan qara yi maka fada bare zagi ba dan Allah kayi hakuri
Ina ABDUL yasaka aransa saiyayi masa lilis
Dan haka ko saurararsa baiyi ba yaci gaba da zanesa yana mai ihu daneman doki

Gefe guda momyn AMEER dake falo suna hira sai taji kamar ana ihu
Itafa tana yawan jin kukan mutane a gidan nata Amma bata gane daga ina kukan yake fitowa
Kallan AMEER tayi Wanda yake aikin murmushin aikin da ABDUL keyi Tace waini daga ina kukan nan yake fitowa ne Lokaci lokaci ina yawan ji Saidai bana gane daga inda yake fitowa
Abida taja numfashi tace Nima ina yawan ji lokaci lokaci haka
Dan daure fuska AMEER yayi cikin rashin ladabi yace Tayaya ni zan sani
Ai lura nayi kamar idan kana cikin gidan ne ko Abdul idan yana nan nake jiyo hakan
Shuru AMEER yayi Tabbas tayi gaskiya Dan haka tsarin nasu yake Idan shine yake hukunta mutanan ABDUL zama yake dasu momyn yana dauke hankakinsu da hira Haka idan ABDUL din ne yake hukuncin shine yake zama kamar yanda yake tare dasu yanxu
Ahankali yanxu yace da ita Ba mamaki ko makwaftammu ne Amma nan gidan ina iyamu kenan waye zaizo yana mana kuka a gida
Momyn taja numfashi da cewa Ba mamaki kam ko hakan ne to Allah ya kyauta
Abida tace amiin

Koina na jikin Babah Shehu sanda ya zanu Dan baqaramin duka ABDUL yayi masa ba
Kuka kam babah Shehu yasha Bai taba tunanin tantirancin ABDUL yakai haka ba Nan take tsoranshi ya zagaye jinin jikinsa
Kallo daya zakamai kasan saiya dauki sati biyu yana jinyar kansa

ABDUL kiran AMEER yayi yace mishi ya gama mai balli ballin Dan haka ya fitto suyi gaba dan ana jiransu ne
Shi kansa AMEER ya tsorata da dukan rashin mutuncin da ABDUL din yama babah shehun Hakan ne ya tabbatar masa da cewa lalle lefin nashi bana yau bane ya dade yana tarasa
Haka suka qara kullesa bayan sun dirga masa ruwa daniyarsu na sai gobe zasu sakesa

Direct gidan wani Alhaji sukayi Wanda yake basu hudar ibilis ta maye suje su rabama mutanansa

Yana ganinsu ya saki murmushi da cewa Saiku yarana Nafara tunanin zan fara turaku Lagos kuna rabama manyan mutanan kayan namu
AMEER yayi murmushi bayan sun zauna kan kuje mecin mutum uku yace Aini banda matsala ko ina zaka turamu zan baka hadin kai Alhaji matuqar zaka saki bakin aljihu yanda nake so Matsalar dayace shine ABDUL
AMEER yakai qarshen zancen da kallan ABDUL wanda ya dora kafa daya kan daya yana me qarema falan kallo cikin wani salo kamar lokacin yasan falan
Alhajin yaja numfashi tabbas AMEER baida matsala ABDUL ne yake da matsalar Dan idan yace bazaiyi abu ba Toh bazai yi ba Koda ko zaka sakar mishi bakin aljihu Sam kudi basa gaban ABDUL Dan baya wani abu dasu
Kasancewar baya hulda da mata kamar yanda AMEER yakeyi
Tara kudinsa kawai ABDUL yake a banki Idan ya fuskanci masu buqata saiyaje ya ciro ya basu
Ko idan AMEER din yana da buqata ya basa
Ko shi kansa idan yana san shiga kasuwa yama kansa shopping na kayan sawa da wasu alamuran na rayuwa wanda bazai zama lalle mahaifinsa yayi masa ba Wannan shine kawai amfanin da kudin sukema ABDUL

Kallansa dakyau Alhajin yayi da cewa Toh kaji abinda dan uwanka AMEER yace Allah yasa kaima kace min hakan
Iya tsawan wane lokaci zamu dauka a Lagos din ABDUL ya fada cikin san sani
Eh bazaku wucce wata daya ba Alhajin ya bashi amsa cikin tabbaci

Tashi ABDUL yayi da daukar feroz dake kan table din gabansu yana cewa Babu matsala Kawai muna buqatar kabamu miliyan daya Mu raba Idan yayi maka toh Idan baiyi ba Bana tunanin zamuje can Yana zuwa nan a zancensa ya kalli AMEER daci gaba da cewa Koya kagani dan uwa
Jan numfashi AMEER yayi da cewa Sosai hakan yayi
Murmushi Alhajin yayi da fadin Idan dan wannan ne babu damuwa Zan iya baku fiyema da hakan Idan har baku bani matsala ba

Murmushi ABDUL da qarasawa kusa da Alhajin yace Bar batun samun matsala Alhaji Dan bama kawo maka ita Amma koda hakan tafaru wallahi saika bamu kudinmu dan kasan ba kullum ake kwana a gado ba ABDUL na fadin hakan ya kalli AMEER damai alamar ya tashi su tafi sannan ya ficce daga falan
Da kallo alhajin ya bishi Gaskiya yaran ya hadu Yana magana da izza Babu tsoro ko shakko cikin idansa Yana jin dain harka da yaran Zai jure duk wani bacin rai dazai fuskanta daga garesu Dan ba qaramin samu yake dasu ba
Tashi AMEER yayi da Murmushi kan fuskarsa yana kallan Alhajin ganin yabi bayan ABDUL da kallo yace ABDUL kenan ake gaya maka Alhaji Sam bashi da tsora akan komai kana dai gani na rigashi shiga tantiranci amma yafini sanin yanda ake tafiya da irinku Hmm yanxu dai Ina buqatar dubu ishirin zan iya samu
Murmushi Alhajin yayi dace masa Zaka samu mana
Nanya zuge wata jaka ya bashi dubu Ashirin din Kana yabar falan zuwa cikin motarsu inda ABDUL yake

Bayan ya shiga ABDUL yaja motar kallansa ABDUL din yayi da cewa Sanda ka karbi wasu kudi gunsa ko
Eh mana Na hannuna ne bazasu kaini jin dadin da nake san ji yau a club ba
Yayi kyau hakan Yanxu muhucce direct club dinne ko akwai inda zamu

1 thought on “Tantiranci ko karuwanci hausa novel”

Leave a Comment