Yar bangar siyasa complete hausa novel

Yar bangar siyasa complete hausa novel

 

YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

_KIRKIRARRAN LABARI NE BAAYI DAN ACI ZARAFIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAIDAI DA YANAYI NA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE_

_Pegen farko naki ne_
_Ummi yar bare bari na gaisheki kanuri kina kamshi ina binki da humra yar dakina Allah ya bar kauna ta dan Allah_

_Bisimillahi_

Free Pege
1

DORAYI
Wani rugujajan gida na hango na jar kasa duk katangar gidan ta zaizaye ta durkushe ta zama yar karama saboda tsabar wahala kofar gidan hanhai yake masu wucewa ma suna kallon cikin gidan Wani tattararran buhu na hango wata budurwa ta saki tana fadinHaba wannan wace irin masifa ce ace kullum gida a bude saboda tsabar mutunci duk kuna zaune a rasa wanda zai sakaya kofar ko kishin kanku ba kwayi meye amfanin talauci Allah ubangiji kayi mana katangar karfe dashi

Aa aunty Wasila kyalemu mu sake mu sha iska yo wannan gidan in ba abude shi ba me zaayi masa gida a rube da jar kasa ai wallahi ko ta halin Kaka sai nayi kudi in huce takaici nayi dakace dana fito ta tsatson babanmu duk shine ya cuce mu aikin banza kawai Ta karasa maganar tana jan dogon tsaki

Uwani dake sunkuye a bakin rijiya tana wanki taceKya fada Rashida ni kaina da kace nakeyi da auran babanku gashi ya mutu ya barni da wahala da kailulu kafin zuwansa gidanmu akwai manyan mutanan da suka fito zasu aureni nace shi nake so saboda naga fari kyakkyawa sai da tafiya tayi nisa a tsakaninmu na gane kyau bashi bane kawai ka auri mai kudi ka huce bakin cikin duniya

Rashi da turo daurin dankwali gaba taceAi wallahi Uwani nayi alkawarin sai nayi auran kece raini dan ba zan auri karamin mutun ba sai na zaba na durje sannan dan wannan kyawun nawa ba zai tashi a banza ba

Uwani taceYawwa yar gari kiyi komai ba komai nice Uwarku nice Ubanku babu shegen da ya isa ya sanya ido a kanku tunda babu wanda yake taimaka mana to kuwa banga dalilin da zai sanya ace dole sai kunyi aure ba ko wacce tayi abunda take so kwalliya kuwa ko wace iri ce kuyi ku futa ku samo manyan maza masu abun hannu ni kaina wannan kyawun da Allah ya baku bana so ya tashi a banza a wofi

Wasila dake tsaye tana sauraransu taceYanzu dai Uwani idan na fahimce ki kina so kice mu tafi yawon karuwanci ko

Uwani taceTo meye idan karuwanci kukayi ai halak dinku kuke nema da kuje ku dauki na wani gwara ku mika jikinku a biya bukata sai me waye zai gani abunda ba fitowa yake a saman goshi ba

Wasila taceTo sai dai in Rashida amma ni na fadi miki kome zakiyi wallahi bazan zubda daraja ta da mutunci na ba na yarda zanyi ko wace irin sanaa ce amma banda karuwanci

Uwani taceKece babba kuma kece mara wayo yo mara wayo mana duk wata sanaar da zakiyi a yanzu ba takai ta karuwanci ba itace yanzu yanzu zaki mika kiji dumus a hannunki yanzu sai kiga kina murza sitiyarin mota yanda kike da zubi ai nasan manyan mutane da sarai ne za suyi karakaina a kanki

Wasila ta harari mahaifiyar tata taceWallahi Uwani kinji kunya kwarai komai hudubarki ba zanyi wannan sanaa ba ina da ilimi daidai gwargwado sannan kuma ni babu abunda na tsana a duniya irin iskanci wallahi da in mika kaina gurin wani gardi gwara na kwana banci ba Sanaa kam nace zanyi ko wace iri ce banda karuwanci

Rashida taceWallahi aunty Wasila baki da wayo kin fini fa zubin jiki mai kyau da daukar hankali wallahi kina fadawa wannan harkar maza zasuyi caaaa a kanki shikkenan mu da talauci munyi hannun riga

Ashar ta lailaya mata taceKika sake mun irin wannan maganar sai ranki ya baci kema bana fata kiyi wannan sanaa in dai kudi ne ku bari ku gani ku dai ku taya ni da addua

Uwani na shanya kayan wankau din mutane taceTo shikkenan muna zuba ido mu gani a kasa uwar tsari yau ki shigo mana da gassasun kaji da lemo nan zamu gane kin zama yar kasuwa

Wasila taceUwani dan girman Allah da Annabi kar kuje yawon bin gidajan jamaa sannan kar ki tura Rashida tayi wannan sanaa wallahi bata dace damu ba a matsayinki na mahaifiyarmu ki kare mana martabarmu insha Allahu yau zan fita a saa zaa dace

Uwani taceTo tunda kince haka shikkenan Cin mu da shan mu duk ya rataya a wuyan ki TaceEh naji insha Allahu Allah zai bani ikon daukar nauyinku

Har ta daga buhun zata futa sai ta dawo tana kallon mahaifiyar tasu taceKo na futa dan Allah karku daga buhun nan ku barshi a haka yafi mutunci Uwani taceShikkenan Allah yq bada saa
Wasila ta amsa da ameeen tasa kai ta fice daga gidan

Tantiranci ko karuwanci hausa novel

_Muje zuwa_
BINTA UMAR ABBALE
1107 944 AM 234 906 548 4591 YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

httpswwwfacebookcom107980080946102referrerwhatsa

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko orange_

Free Pege2
Wasila na fita ta nufi gidansu Hadiza Yar camas kawarta ce sosai amma kuma halinsu ya bambamta Camas tana bin maza kuma tana dan taba shaye shaye sabanin Wasila da bata shan komai na maye sannan kuma bata bin maza kawai dai ku barta da tsiwa da rashin kunyarta

Camas na zauna a tsakar gidansu suna hira jefi jefi da mamanta Wasila tayi sallama ta shiga gidan Mahaifiyar Camas mai suna Asabe ta amsa tana fadinWasila kece a gidan TaceE wallahi ina wuni Suka gaisa a mutunce har Asabe na tambayarta Uwani taceTana nan lafiya

Camas TaceKe yar iska ina zuwa kuma nagan ki da mayafi yau ina hijab din Wasila taceDauko mayafinki muje Camas ta mike a hanzarce ta shiga dakinta ta dauko wani karamin mayafi ta yafa suka fita Asabe ta bisu da kallo tana girgiza kai alamarin na yar tata sai addua dan a zahiri ma gwara Wasila kanta komai ma Hadiza ya lalace har karatu duk ta watsar gwara Wasila nayin asha ruwan tsintsaye gurin zuwa makarantar

Sai da suka kusa futa daga layin sannan Wasila taceKe Camas yau fa a shirye nake wallahi Gidan gwammanti zamu je yanzu

Camas taceKai Wasila me zamuyi a gidan gwamnati kuma Wasila taceMuje kawai ina so in fara harkar Siyasa ne Camas taceHarkar Siyasa kuma lallai Wasila kina so ki jefa rayuwarki a rudani Siyasa masifa ce duk ga sanaoi nan da zakiyi ki rufawa kanki asiri sai kice siyasa za kiyi

Kinga Camas idan zakije to ni bana son wata doguwar magana anan gurin harkar Siyasar ma idan ta karbeka sai kaga ka samu kudi sannan kuma duniya ta san da zamanka

Camas taceKuma fa hakane wallahi hausawa nacewa matsoraci baya zama gwani kawai mu afka baasan inda rana zata fadi ba Wasila taceAshe kin gane kawata

Bakin titi suka fito suka samu a daidai ta sahu kai tsaye sukace ya kaisu gidan gwamna Mai dan sahu ya kallesu da mamaki sosai a tare dashi gidan gwamnati to me zai kai wadannan yaran can bashi da mai bashi amsa kawai ya ja babur din sukayi gabaYanda suke hirar ne ya fahimci inda suka dosa yaceYaya na ni dai shawarar da zan baku shine ko zakuyi wannan harkar dan Allah ku tsare mutuncin ku kar ku ku watsar da martabar da Allah yayi muku

Wasila taceInsha Allahu baba zamu kiyaye YaceTo nagode da kuka dauki magana ta Ana kiran sallahr magariba ya sauke su a bakin titi Wasila ta ciro dari biyu a bayan condem din wayarta ta bashi yaceAi saura dari dari uku ne kudin

Haba Baba kayi hakuri da wannan din ita kenan muka baka ka gani ko na dawowa ma bamu dashi YaceShikkenan Babur din yaja ya barsu a gurin

Camas taceShiyasa sam bana son shiga babur din dattijai duk yan buri ne gwara in shiga na samari masu tara suma su kunna maka kade kade in ta kama ma suce ka bar kudinki

Wasila hankalinta na kan wata mota dake kokarin shiga rukunin gidan gwamna taceWallahi haka maganarki take Yawwa kinga wata mota zata shiga bari na tsayar da ita sai ta hau dagawa mai motar hannu

A hankali motar ta tsaya inda take kana gilashin motar ya sauka a hankali mamalakin motar ya bayyanaWani kosashen mutun ne bayan motar a hakimce kana ganinsa kasan yaci ya tada kai da nera yana hada ido da Wasila ya hadiya wani yawu zuba mata ido yayi har suka karaso gurinManya manyan idanunta ta juya kana ta dafa motar da hannunta guda ta lankwasar da mirya ta taceBarka da wuni yallabai ya gida ya fama da jamaa

Alhaji Maaruf ya amsa yana washe baki sosai yaceLafiya yan mata jamaa kuma ku zaa tambaye

Ta saki wani shuumin murmushi taceYallabai kenan Dama muna neman wata alfarma ne YaceKo wace alfarma ce ku fadeta mutukar ta shafi gidan gwamnati to zanyi kokarin ganin kun sameta

Yawwa Yallabai muna so mu fara harkar siyasa ne shiyasa muka dacewar muzo muyi tambaya akai Alhaji Maaruf yayi mirmushi hade da shafa sajensa ya dan tura hular sa keya yaceTo ai kaya ne suka tsinke a gindin kaba babu matsala ku shigo mota muje zan shiga gurin mai girma Governor idan na fito sai muje daku guest hause dina in yaso sai muyi maganar

Ba tare da wata fargaba ba suka bude mota suka shiga suka zauna dravar yaja motar suka bar gurin
YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
httpswwwfacebookcom107980080946102referrerwhatsa

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko orange_

Free Pege3
Kunnanshi makale da waya ya fito daga bedroom din shi ya zauna daya daga cikin shirga shirga kujerun dake palon ya wani dora kafa daya kan daya yana masifaKhalifa wadannan mutanan fa babu Allah a tare dasu ni wallahi tuntuni na dawo daga rakiyarsu shin wai mulki hauka ne duk wannan kashe kashen da akeyi da sace sacen yara kananun mun san daga ina ne kawai saboda ana jin tsoronsu sai ayi shiru to wallahi daga yau na shirya damarar yaki dasu mulki suke so nima shi nake so Allah ya bawa mai rabo saa haba wannan alamarin ya ishi talakawa wuya tayi wuya mutane sai mutuwa sukeyi gobe ka fito da wuri zamu fara yawon kamfen insha Allah Khalifa dake daya bangaran yaceInsha Allahu zan fito da wuri amma yana da kyau ka tanadi matakan tsaro kafin fitar tamu YaceKar ka damu da wannan insha Allah Allah zai karemu tunda domunshi muke Sallama sukayi da juna ya kashe wayar tare da ajiyeta saman tevur din dake gabanshiZuba masa ido nayi ina kallo wai Allah yayi hallita a gurin kyakkyawa ne ajin farko fari gaggausa yana da dogon hanci da manya ido da gashin gira kewayayyiyar fuskarsa na dauke da sisirin sajensa wanda yasha gyara ya zauna das ya kawata fuskar tashiYa wuce ka kirashi yaro gaskiyar magana kenan domin idan ka tsaya ka kalleshi da kyau zaka fahimci shekaru sun dan tura masa a kalla yanzu shekarunsa arbain da biyu zuwa da uku
Ahamad Musa Ba iya ka ainin sunansa kenan Matashin saurayi mai jini a jiki mai tashen kudi wanda bai san iya adadinsu ba shi ya sanya jamaar gari suke kiranshi da wannan suna Ba Iya ka shima ya samo shi gurin mahaifinsa Alhaji Musa Ba iya ka wanda ya shahara yayi shura a zamaninsa Allah ka jikan maza
Ahamad kawai ya haifa shima kuma kafin ya haifeshi din sai da ya futar da rai da haihuwa lokacin duk girma ya baibayeshi ya auri wata yar filani ashe rabon a jikinta yake haduwarta ta farko ta dauki cikiFarin cikin da ya shiga a lokacin Allah yayi yawa dashi ya dinga sadake sadake yana kai mutane saudiya suyi wa matarshi addua Allah ya sauketa lafiya

Allah babu yanda baya tsara lamarinsa gurin haihuwar Ahamad mahaifyarsa ta rasu sosai iyalin Alhaji Musa sukaji mutuwar daga bisani suka barwa Allah lamarinsaSai suka dawo kan Ahamad suka dinga nuna masa so da kulawa mussaman mahaifinshi Allah ya jarrabeshi da kaunar yaron nashi ashe ba zasu dade da juna ba Allah ya dauki rayuwar Alhaji MusaMutuwar da ta girgixa zukatan alummar gari suka dinga kuka da fadinBango majin ginar talakawa ya fadi Jamaa sukayi dafifi a harabar gidan suna masa addua da fatan Allah ya kai rahama kabarinsa

Tunda Ahamad ya taso yaga yanda mahaifin shi ke taimakon alumma sai ya dora a inda ya tsaya tun yana dan shekara ashirin a duniya sunanshi ya bace a gari mutukar baka kira
Ba iya ka ba to babu in zaka kwana kana kiran Ahamad babu wanda zai gane wanda kake nufi

Ahamad jamaar gari ne suka kwadaita masa shaawar mulki da sam ba tsarinsa bane ya fiso yayi harkokinsa to shima kuma da ya zauna yayi nazarin yanda alamuran siyasar ya tabarbare sai kawai yayi shaawar fantsama kansa a harkar domin ya taimaki alummar da suke galabaita a jahar mussaman talakawa sune dama abun tausayi

Kallo guda za kayi masa ka gane yana da fuskar Salihai a zahirinsa kenan a badinsa kuwa mutum ne shi mara hakuri kuma sam baya barin ta kwana kamar zawo yake mutukar kayi masa abu idan bai rama ba sam baya jin dadibayan wannan halin nasa bai da wani mummunar hali dama ance adan adam tara yake bai cika goma ba Ahamad nada tausayi da taimako sai nace muku ma duk rabin neman kudinsa yanayi ne kan jamaar gari marasa galihu da na kasassu gami da marayuDalili kuwa bashi da nauyin kowa a kanshi tunda shi ba aurene dashi ba ballanta ayi maganar yara Jamaar gari duk sun dauka yana da aure da iyali shiyasa duk adduarsu a kan iyalinsa take karewa sai dai kawai amsa da ameeen

Nasan zakuyi mamakin namiji kamar Ahamad mai jini a jika sannan uwa uba kudi ga kyau da kwarjini da haiba da yake dasu amma me yasa bai aure ba Yana zaune hakane ba wai dan bashi da lafiya ba ko kuma rashin matar aure akwai yan mata bila adadin dan ba zasu lissafu ba kawai duk cikinsu bai ga wacce ta kwanta masa a ransa bane ya ajiye maganar aure a gefe saboda yasan cewa lokaci ne idan Allah ya kawo masa matar lokaci guda zaayi a gama

Daya daga cikin masu tsaronshi ne ya shigo palonYa daga kanshi yana kallonshi A nutse yaceYa akayi Garba yaceKana da bakuwa tana dakin baki mun sauketa

Jim yayi yana nazari wace bakuwa yayi kuma yanzu karfe goma na dare Ko da yake ai tunda ya fara wannan harkar kuma yayi ta ganin jamaa ya mike a nutse Garba ya bashi hanya ya wuce kana ya take bayanshi

YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko orange_

Free Pege5
Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya karaso inda yake tsayeKai a kasa Garba yaceSir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar Ido ya sanya masa a nutse yaceKamar name kenan Garba ya kara risinar da kanshi a kasa yaceAnya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba

Murmushi yayi yaceGarba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo saa
Garba yaceKa gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba Ya amsa da ameeen Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza Garba ya take masa baya

Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Maaruf a can tsallake a fakeranta duk a bace ta karasa bakin motarDan kwankwasa jikin motar tayi Camas da Alhaji Maaruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur ya bude mata motar yana fadin Ya akayi Yar gaske Allah yasa kin aiwatar da komai Rai a bace tace Wallahi yaki bada hadin kai dan iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba

Alhaji Maaruf yaceKai wannan dan iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji shaawarki ba anya ma kuwa yana da lafiya duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji shaawa ta kamashi Ya karashe maganar yana bin jikinta da kallo

Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas take kwance a kai Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka sheke Allah ya kyauta

Hijab dinta ta sanya taceAlhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku

Alhaji Maaruf ya kunna motarshi yana goge gumi yaceMaganar ki gaskiya ce Yar gaske shiyasa muke kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin

Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Maaruf na fada musu yanda suke dauki ba dadi a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kadangare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai karbeshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya

Wasila taceKa rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kadai ya isheshi sai nayi fatafata da rayuwarshi

Alhaji Maaruf yaji dadi maganar ta yaceMu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya Yar gaske zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu

Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa Ba iyak ka har sai taga abunda ya turewa buzu nadi

Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen

Yar kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana dakon dawowar yar tata

Wasila ta mayar da kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu kamar ba dare ba

Uwani da Rashida suka fito a guje Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshiUwani na ganin Sabbin yan dubudubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu ta rungume yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar guda ta dinga rangadawa tana sakarwa yar tata kirariIta kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya

Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete

 

Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige rubabbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga hadddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya wai yaushe rabon duniya da ayya raye Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannuntaWasila taceYanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa

Uwani taceKi dan gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh duniya kenan

Wasila taceUwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fadinAi dama ni nasan jari na haifa ke ba karamar mace bace idan baaso ki dan komai ba a so ki dan kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina

Wasila taceUwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sanaa muka fita mukayi ko ba haka ba Camas Tafada tana kallon Camas dake irga kudinta

Camas taceKwarai kuwa sanaar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba

Uwani taceKai amma wannan sanaa ta karbeku wallahi Allah ya bada saa ya taimake ku

Suka amsa da ameen Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada hakarkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita Sanaa

_Muje Zuwa_
BINTA UMAR ABBALE
711 941 PM Bintu YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko orange_

 

Free pege4
Cikin takun girma gami da kasaita ya shiga dakin lokaci guda kamshin turaransa ya karade hancinta ta dago shanyayyun idananunta ta zubasu a kansa tun kafin ya karaso inda take zaune ya kare mata kalau black beauty mara tsayi sosai da cikar kirji dauke kansa yayi daga kanta ya hade fuska sosai wannan bakuwar tashi ba ta arziki bace duba da yanayin suturar dake cikinta

Tana sanye da wata matsatstsiyar t_shart da dogon wandon jins wanda ya fitar mata da zahirin hallitarta ta sanya karamin hijab wanda ko kirjinta bai rufe ba tsakiyar kanta yayi tozo da tsayi da alama tana da gashi sosai tunda ga alamunsa nan ya nuna saman goshinta

Hannunsa cikin aljuhu ya isa inda take ta mike tsaye da sauri tana marmar da shegun idanunta masu rikita lissafin da namijiYa kura ma jikinta kallo tayi sosai dan bai hango makusa a tattare da ita ba ta cika har ta batse kuma tana da abubuwan da yake balain so a jikin ya mace sai dai kash ba wannan ne a gabansa ba abunda ke gabansa a halin yanzu shine ya zaayi talakawa su samu walwala da farin ciki

Fuskarshi ya sake tamkewa tamau yaceBaiwar Allah daga ina ance dani nayi bakuwa na dauka ta arziki ce sai a ka samu akasi

Wasila taji ciwon maganarshi kasancewar ta macen da bata daukar raini mussaman ga da namiji basarwa tayi ta matsa kusa dashi cikin salon janye hankali taceDaga duniya na fito nazo ne in debe maka kewa nasan namiji lafiyayye kamar ka na bukatar lafiyayyar mace ka mata

Tsawa ya buga mata yana nuna ta da hannuKe cikin gidana kika shigo kina min wannan maganar ashe dama zargin da nake miki gaske ne okey get out from my house Maimakon ta fita sai ta durfafeshi tana so ta rungumeshi ya kai mata wani wawan mari yana ya tsine fuska sai karkade jikinsa yake kamar wanda ya rabi motar daukar kashiYa mutsa fuska yake yana korar shaidan yace Za kici Ubanki yanzu yanzu zan sanya a xane miki jiki har gida zaki shigo ki kawo min iskanci ni bairinku bane Fita yayi yana kwalawa Garba kira

Wasila ta dauke hannunta dake fuskarta gaskiya yana da taurin kai ta lura ba zai bari hakansu ya cimma ba ruwa ba dan iska kawai tayi irin wannan shigar ya dinga kauda kai yana ya tsine fuska anya ma kuwa lafiyayye ne bata da mai bata amsa sai tayi maxa ta dauki jakarta zata futa suka buga karo dashi yazo zai shigo kirjinta ya daki kirjinsa yayi saurin ja gefe guda yana kallonta sai wani gumi yake kamar wanda yayi tsere

A ya tsine ta kalleshi taceNa dauka ai lafiyayyan namiji ne ashe hotiho ne har kana zagina kato da kai baka kunyar zagi anzo a jiyar da kai dadi kana gudu Allah ya kyauta kaje ka nemi magani

Wata shaka ya kai mata ya matse ta a jikin bango garo ta dinga kakari idanunta sunyi jajawur Cikin kaushin murya yaceIdan zaa hada min iriirin irinki guda dari duk zan gama musu aiki ba tare da nagaji ba karyar iskanci kike yarinya da ina da bukatar mace a yanzu dana fatattaka ki kuma in kwana lafiya yar iska mara galihu

Hannu tasa tana kokarin bambare hannunsa dake shake da wuyanta duk ta muzanta sai kyarmar jiki take tana cizan lebantaSai da ya gama galabaitar da isa sannan ya saketa aikuwa ba tayi watawata ba ta kai hanni gabanshi zata damka yayi gaggawar rike hannunta yana kallonta da mamaki a tare dashi

Sun jima suna kallon juna ita dashi mugun mamakin karfin halin yarinyar yake wato shammatarsa take so tayi ta nakasta shiIdo jawur taceSake min hannuna Ya kara rike hannun tamau yana sakin wani killer smile yaceKina so ki taba ne Wasila tayi tsurutsuru tana kallonsa sam ba tayi tsammanin guy zai samu galaba a kanta ba

Wannan kayan aikin da kike gani yafi karfin irinku yan iska na kamilar mace ne mai addani ba irinki mai yawon ta zubar ba A fusace ta fuzge hannunta ta watsa masa kallon raini fuuuuu ta kama hanyar fitaTaku uku yayi ya cimmata tare kofa yayi yana me bin jikinta da wani shuumin kallo

Sosai kikayi babu wata makusa a jikinki duk inda yan mace ta kai kin kai yarinya sai dai sam baki burgeni ba idan ma turo ki akayi to sai kije ki sake sabon shiri ki sani Ahamad ya wuce tunaninki Yana kare maganarshi ya kwalawa Garba kira

Ya shigo da sauri yana fadin Yallabai gani Yace Maza rakata da bulala idan tayi gardama ka zane kafafunta Garba Ya kalleta Wuce muje Yafada cikin bin umarnin Ubangidansa

Wasila kamar ta hadiye zuciya ta mace tunda take a rayuwa baa taba tozarta irin yau ba lallai guy bashi da mutunci amma babu komai sun daura idan kere na yawo zabo na yawo watarana zaa hadu
Kallon uku shaura kwata tayi masa kana ta gyada kai ta wuce shiGarba ya bita a baya da zabgegiyar bulalarsaHarbar gidan ya fito ya tsanya tare da zuba hannuwansa cikin aljuhu yana kallo Garba ya tasa keyarta har bakin gate yanayi yana cauda bulala a kasa kamar zai daketa hakan ya sake kular da ita ta sake kullatar guy girgiza kai kurrum take tabbas maganar da chamas tayi gaskiya ne babu abunda yake cikin harkar Siyasa sai tozarci da wulakanci Garba na ganin tayi nisa da layin sai ya juya ya koma cikin gidan

 

 

_Muje Zuwa_
BINTA UMAR ABBALE
712 839 AM Bintu YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko orange_

Free Pege5
Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya karaso inda yake tsayeKai a kasa Garba yaceSir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar Ido ya sanya masa a nutse yaceKamar name kenan Garba ya kara risinar da kanshi a kasa yaceAnya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba

Murmushi yayi yaceGarba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo saa
Garba yaceKa gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba Ya amsa da ameeen Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza Garba ya take masa baya

Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Maaruf a can tsallake a fakeranta duk a bace ta karasa bakin motarDan kwankwasa jikin motar tayi Camas da Alhaji Maaruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur ya bude mata motar yana fadin Ya akayi Yar gaske Allah yasa kin aiwatar da komai Rai a bace tace Wallahi yaki bada hadin kai dan iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba

Alhaji Maaruf yaceKai wannan dan iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji shaawarki ba anya ma kuwa yana da lafiya duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji shaawa ta kamashi Ya karashe maganar yana bin jikinta da kallo

Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas take kwance a kai Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka sheke Allah ya kyauta

Hijab dinta ta sanya taceAlhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku

Alhaji Maaruf ya kunna motarshi yana goge gumi yaceMaganar ki gaskiya ce Yar gaske shiyasa muke kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin

Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Maaruf na fada musu yanda suke dauki ba dadi a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kadangare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai karbeshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya

Wasila taceKa rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kadai ya isheshi sai nayi fatafata da rayuwarshi

Alhaji Maaruf yaji dadi maganar ta yaceMu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya Yar gaske zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu

Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa Ba iyak ka har sai taga abunda ya turewa buzu nadi

Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen

Yar kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana dakon dawowar yar tata

Wasila ta mayar da kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu kamar ba dare ba

Uwani da Rashida suka fito a guje Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshiUwani na ganin Sabbin yan dubudubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu ta rungume yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar guda ta dinga rangadawa tana sakarwa yar tata kirariIta kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya

Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige rubabbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga hadddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya wai yaushe rabon duniya da ayya raye Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannuntaWasila taceYanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa

Uwani taceKi dan gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh duniya kenan

Wasila taceUwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fadinAi dama ni nasan jari na haifa ke ba karamar mace bace idan baaso ki dan komai ba a so ki dan kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina

Wasila taceUwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sanaa muka fita mukayi ko ba haka ba Camas Tafada tana kallon Camas dake irga kudinta

Camas taceKwarai kuwa sanaar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba

Uwani taceKai amma wannan sanaa ta karbeku wallahi Allah ya bada saa ya taimake ku

Suka amsa da ameen Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada hakarkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita Sanaa

 

 

 

_Muje Zuwa_
BINTA UMAR ABBALE
713 107 AM Bintu YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko orange

Free Pege6
Da safe suka tashi da wurwuri sukayi wanka tsaf suka shirya tuni Uwani ta ta fasa musu shayi Rashida ta siyo su madara da milo da bread har da su kwai Uwani ta soya musu yau karin kullamo sukayi rigijib suka karasa cinye sauran kajinsu na jiyaWasila ta kalli Camas dake gyara daurin dankwali taceYa kamata kije gida mamanku ta ganki kafin mu tafi ko Camas taceKe kin san idan na shiga gida yanzu babanmu nanan ba zai bari na sake fita ba kawai ki kyalesu idan na dawo ma hadu

TaceShikkenan ke Rashida zan bada dubu talatin ayi aikin gidanan a sanya kokafi data waje data bandaki saboda bana so in doso layin nan wallahi in hango ku kamar tumaki a akurki wai sunan kuna cikin gida a zaune amma jamaar dake waje na ganinku wannan gidan ai sunansa kango ba gida ba

Uwani taceNaji kinyi maganar dubu talatin duk a aikin gidan anya kuwa basuyi yawa ba TaceNa fiso ayi komai da inganci a sa kofofi masu kyau insha Allah yau ma idan mun fita zamu samo kudi Uwani taceTo Allah yasa Wasila ta irga dubu talatin da biyar ta bawasu Uwani talatin na gyaran gida biyar kuma tace su dan auno kwanan shinkafa suyi cefane kafin ta dawoHaka sukayi musu sallama suka kama hanya suka tafi can guest house din Alhaji Maaruf dake a can yace su hadu

Suna shiga harabar gurin suka wasu gugun matasa rukuni rukuni amma yan daba da shayeshaye sunfi yawaAlhaji Maaruf da wani mutumi suna tsaye a kansu suna magana dasu

Kai tsaye can suka nufa Alhaji Maaruf na ganinsu ya washe baki ya kalli Alhaji Tasiu Yawwa kaga yan halak ko yanzu yanzu mu ka gama zancensu ashe suna tafe

Wasila tace Aikuwa dai muna hanya wallahi kun san matsalar abun hawa sai a hankali Alhaji Tasiu ya kalli abokinsa yana nuna Wasila da bakinsa yaceKo baka fada mun ba na gane wannan ce Wasila Yar gaske YaceKwarai kuwa Alhaji kayi mamakin ganinta yar karama ko YaceDaidai kenan duk da kankantar ta nasan zata bamu gudumawar da muke bukata daga gareta Wasila naji kina maganar abun hawa da sauransu ki kwantar da hankalinki zan siya miki mota ta kece raini ke dai kawai ki bamu goyon baya domin zamuyi amfani dake domin cimma manufarmu

A dake taceKar ka damu Alhaji a shirye nake wallahi domin harkar na shigo gadan gadan duk inda nasan zan samu nan zan nufa in zaku sakar min kudi magana ta kare

Alhaji Maaruf da Alhaji Tasiu suka fashe da dariya suna tafawa Sai bayan sun tsaigata da dariyar ne Alhaji Tasiu yaceKunga wadancan mutanan dake zazzaune ko Suka ceEh yaceTo zaku fita dasu yawon kamfen saboda mun samu labarin Ahamadu Ba iya ka zai fita zagaye gari domin yada munufarsa a kan talakawa to muna so duk inda suka shiga suna yada manufarsu su shi ku soke ku watsa jamaa akwai kayan aiki a tare dasu Lauje karkuji komai kuyi aiki sosai mune muke da mulki a hannunmu babu wani abu da zai same ku

Wasila taceKar ka damu alhaji nayi maka alkawari bakin rai bakin fama Alhaji Maaruf ya kalli Camas yana lumshe mata ido yaceKefa baki ce komai ba

TaceHaba karfa ku damu nima na dauki alkawari insha Allah sai mun rusa shirin Ba iya ka

Alhaji Tasiu ya nunawa matasan nan su Wasila yace sune abokanan tafiyarsu su kula dasu a matsayinsu na mata har bakin mota suka rakasu suka shishhiga akalla sai da suka cika motaci hudu irin na haya saboda yawansu sun kai su ashirin da wani abunKai tsaye suka dauki titin da zai futar da mutun cikin gari

Cikin shadda fara kal ya fito yana daura agogon silvar a hannunshi hularshi ya karba daga hannun Garba ya dora a kanshi Ba kano zallah yayi kyau har ya gaji ya zaune gefan gujera yana sanya safa Garba ya gama goge masa takalminsa sawu ciki ya mika masa ya sanya a kafafunsa yana mikewa Khalifa babban amininsa ya shigo shima yana sanya da manyan kaya shi harda babbar riga cikin kamala da mutumta juna suka gaisa kai kana ganin muamularsu zaka gane masu ilimi ne suna kuma aiki dashisuna fita harabar gidan suka tadda matasa sun kai su goma duk suna jiran fitowarsaAikuwa ya dinga amsa gaisuwarsu yana daga musu hannu su kuma sun rude da fadin Sai kayi Ko garin ba kowa mu muna tare da kai kane zabin talakawa Kano sai Dan Musa
Ahamad ya daga dukanin hannuwasa biyu sama da karfi yace CPC Suka amsa da Saa YaceSaa ta mai rabo ce Sukace Kaine kake da Saa mai Saa Ya saki murmushi da fadin Allah ya bawa mai rabo Saa Suka amsa da ameeen Da sauri Garba ya bude masa bayan wata hadaddiyar mota ya shiga Khalifa yabi bayanshi Garba da Dan uwanshi Hadi suka shiga sai direba ya shiga mazauninsaKafin kice kwabo kin nemi jamaar gurin nan kin rasa duk sun shisshige motocin dake fake a gurin domin su raka dan takararsu yada munufarshiKai tsaye titin da zai sadaka da wata unguwa a cikin gari suka nufa mai suna Jakara nan yake so ya fara zuwa saboda yanda yake jin labarin unguwar babu kyau ga tabarbarewar alamura da yawa tarbiyar yara matasa ta lalace babu sanaar yi sai jagaliya da harkar gwangwan da sauransu yana so ya fara zuwa unguwar ya yada munfarashi kafin ya shiga sauran unguwanni

A kan idonsu motocinsu suka dinga parking dake duk rabin unguwar Jakara kasuwa ce kafin kice kwabo guri ya hargitse da kayakaya jin cewar ga dan takarar gwamna nan yazo yada munufarshi masoya Ahamdu Musa Ba Iya ka suka dinga turereniya domin suje su daga masa hannuMatasan nan suka fito da tarin pastocinsa suka fara aikin mannawa a bango da shagunan mutane gefan titi suka dinga bi suna mannawa guri ya cika makil Khalifa ya bude masa samar mota ya fito da jikinsa ya daga hannuwansa biyu yana fadin CPC Sai gurin ya rude da fadin Saa Su Wasila suka keto gurin da motocinsu a guje A take mutane suka watse kowa na ceton ransaParking din motocin sukayi suka fito a fusace ko wanne da makami a hannunsaA sai guri ya hargitse ihu kawai kakaji da gudu radadada

Hankalin Ahamad ya tashi sosai gashi Police guda biyu kacal ya dauka kuma suma alamarin yafi karfinsu domin yan daban gidan gwamnati suna da muggan makamai Ya ware murya sosai yana fadinKowa yayi takansa ya tsira da rashi Wani Dan daba ya bullo daga wata hanya dake da maraba da wata katuwar kwata hannunsa rike da wata sharbebiyar addah sai kartar ta yake a kas yana sakin wani uban ihu da fadin Sai kayi ko garin ba kowa Eh yane mu zaa kawo wa raini a unguwar tamu ashe yau sai an zubar da jini wallah Huhhhhhh ya kurma wani uban ihu yayi kan Yan daban Gidan gwamnati yana sararsu ta koina

Wasila dake can aikin Yabawa Fastocin Ahamad kwata da bakin mai ta hango abunda ke faruwa Abokanan tafiyar ta sun suna shigewa mota saboda Kumdum dan daban nan ya soma fitarwa da wasu jini sai suka razana suka soma shiga motaDa gudu tazo shiga mota Kumdum ya fuzgo hijab din jikinta ta dawo baya Kara ta kwallara ganin yana kokarin kai mata sara da katuwar addar dake hannunsa ta rintse ido gabanta na buguwa fat fat fat shikkenan ta mutu Shiru taji gurin yayi ta bude idonta a hankali tana bin mutanan gurin da kalloShi ta gani tsaye a gabanta hannuwansa cikin aljihu yana mata wani mummunan kallo still ga Kumdum rike da sharbebiyar addarsa a hannu

Kallon juna suke ita dashi tsaf ya gane yarinyar nan ce da shigo masa gida jiya tabbas ga maganar Garba ta fito ashe da wata manufa ta ziyarceshi ya gode Allah da bai sanya masa kwadayin mata ba da badan hakaba da tuni bukatarsu ta biya a kansa

Ya kalli Kumdum dake zare ido yana ciccije baki YaceRabu da ita kar kayi mata rauni ko ka zubar mata da jini taci albarkacin sunan mace da ta amsa mace duk inda akasanta mai daraja ce da kame kai Astagafurullah wannan yarinyar ta batawa mata sunansu idan ka daketa ko ka zubar mata da jini duk a banza tunda na lura da akwai bakin iyaye a kanta so ka kyaleta taji da abunda ke damunta zamu dai cigaba da yi mata addua idan mai shiryuwa ce kuma insha Allahu muka samu mulki a hannunmu duk zamu tattara ire irensu mu samu mu hadasu da mazaje daidai dasu muyi musu aure babu shakka zaa samu sassaucin wasu abubuwan
Kumdum ya saki hijab din Wasila dake damke a hannunsa yana fadinEh Yanda kace haka zakayi mahadi mai dogon xamani insha Allahu kano ta kace ko ana ha maza ha mata sai ka tuge wancan wawan da bai iya komai ba sai hauka Jamaar dake gurin suka sa ihu da fadinMaganarka haka take Kumdum Kano ta dan Musa ce ko ana so ko baa so sai yayi Wannan damar da Wasila ta samu ya sanya tayi wuf ta bar gurin can inda motocinsu suke ta nufa ta tarar duk an ragargaza gilashin motocin Camas ta bude motar ta shiga da sauri wani matashi ya daki motar da kafarsa yana musu ihu Sai da suka yi nisa da gurin sai suka saki wakar gwamnan dake ci a yanzu Mai taken Munyi muku fintinkau Kano sai kallo daga nesa mai raba gardama yazo Enginer Lawan Rabo duk wanda zai ja dakai shine wawa Wasila ta fito da jikinta ta saman mota tana watsawa Ahamad dakuwa da dukanin hannunta tana sake fadid
Wanda zai ja da Engener Lawan Rabo shine wawa Ahamad yana kallon sanda take watsa masa hannayenta da sunan dakuwa Zagi ransa ya baci sosai lallai yarinyar nan bata da kirki ya lura yar adawa ce mutuka dole ne ya sanya ayi masa bunkice akanta domin abun nata ya wuce gona da iri

Mota ya shiga tare da jamaarshi jamaar gurin sai daga masa hannu suke suna masa fatan alkairi yana amsa musu cikin sakin fuska amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin zaka tarar tayi bakikkirin sakamakon zagin da Wasila tayi masa wanda ba kowa ne zai fahinta ba sai shi wanda akayi dominsa

 

 

_Muje Zuwa_
BINTA UMAR ABBALE
713 415 PM Bintu YAR BANGAR SIYASA
romantic love story
NA
BINTA UMAR ABBALE
Manazarta Writes asso
_Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura 300 Vip gruop 600 accont din da zaa tura kudin0542382124Binta Umar gtbankIdan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din07084653262_08089965176 sai na fadi yanda zaa biya kudinMutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars90899076_88137740 katin airtal ko Orange_

Free Pege7
Wani irin gudu motocinsu sukeyi kan kwalta suna sakin ihuWakar injiniya Lawan Rabo ta tashi a motocinsu jamaar gari suma suka dinga ihu da fadin Ba mayi insha Allahu kano ta dan Musa ce su dinga jifan motocinsu da duwatsu suna ihu Su Wasila da kyar suka sha amma dai hakan yayi musu dadi tunda dai sun rusa shirin Ahamadu sun hanashi aiwatar da nufinsa wannan ya nuna musu suke da nasara a kanshi

Khalifa ya kalli fuskarshi ya ganta a murtuke yasan ranshi a bace yake gyaran murya yayi yace Wai wannan cin maganin da kakeyi na menene dole fa ka fuskanci irin wannan kalubalan alamarin siyasa sai addua komai mutuncinka sai ya zube kauda kanka kawai zakayi

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya dan gyara zamanshi yaceKhalifa sam abunda mutanan suka turo ayi mun bai dameni ba saboda nasan sunyi abunda yafi wannanShin wai baka ganin zagin da yarinyar tayi min ne
Khalifa ya dan gyara zaman hularshi yana sakin murmushi a hankali yaceDuk akan idona alamarin ya faru sosai nayi mamakin tsaurin idonta na fahimci kuma harkar takeyi da gaske so kar ka damu da wannan Siyasa ce a gabanka ma sai a zage ka a jefe ka kai dai tunda kace za kayi to sai ka daura damara

No Karya ne wallahi Yafada a zafafe ya kalli Khalifan da jajayen idanunsa da suka rine da bacin rai yaceKhalifa Siyasa ba hauka bace kamar ni wannan yarinyar gantafalfala ta zageni kai kanka kasan halina bana ya fiya mutukar mutum ya shiga gonata ban hanata tayi min komai ba na yarda siyasar kasa ce amma banda zagi sai na ci mutuncinta wallahi

Clm dwon mana ka nutsu fa baa saurin yankw hukunci da gaggawa ka kyaleta kawai idan ta sake sai ka dauki mataki a kanta amma yanzu kana yi mata wani abu zasu kulla maka wani sharrin kasan halin su dai

Ya rintse ido yana sake hango lokacin da take watsa masa hannuwanta da sunan zagi Ya bude ido yana sauke numfashi idan fa bai rama abunda yarinyar tayi masa zuciyarsa zata iya tarwatsewa mutum ne shi mai balain kishin kansa da kaunar iyayensa ya tsani na kasa dashi ya raina shi ko ya zageshi baya daukar irin wannan rainin shiyasa yanzu hankalinsa ya tashi mutuka duba da yanda yarinya kankanuwa wacce bata wuce yar cikinsa ba ta zageshi dole yayi bunkice a kanta

Khalifa ya dinga tausarsa da kalamai masu sanyi yana nuna masa haka lamarin siyasa yake dole fa sai ya kauda kansa ga dukanin abunda yan adawa zasuyi masa idan ba hakaba kuwa zai bata rawarsa da tsalle kawai ya share yarinyar ya bari kawai duk sanda ta sake to suma baza su kyale ba

Garba Da Hadi suka ce Sir da ka bari wannan dan daban ya koya mata hankali wallahi yarinyar bata da mutunci ko kadan muma munga abunda tayi maka wallahi munyi rantsuwar duk sanda ta sake maimaita abunda tayi sai munyi mata tsirara sai mun tujara ta a gari karyar iskanci takeyi

Ajiyar zuciya ya sauke ya dan ji sanyi cikin ranshi Yace Na rabu da ita saboda maganganunku ammafa ku sani duk sanda ta sake kwatanta zagina wallahi ranar sai ta raina kanta sai tayi nadamar zuwanta duniya babu ruwana

Khalifa yaceYawwa mai girma Governor haka ake son shugaba da daukar shawara insha Allahu kai ke da nasara a kansu Hannu ya bashi suka rike suna sakin dariya Ahamadu yace CPC gabadanyansu suka amsa da Saa Ya sake fadin CPC Suka amsa da Saa Yace Mulki na Allah ne suka amsa da fadin Insha Allahu kai Allah zai bawa Ya amsa da Allah ya bamu Saa Suma suka amsa da ameen

Wasu Wasila kuwa kai tsaye gidan Governor suka nufa domin su alhaji Maaruf nacan gidan suna meeting sai sukace su samesu a can suka samu wata katuwar rumfa suka zazzauna kamar wasu almajirai suna jiran fitowarsuCan sai gasu sun fito daga wani dakin wanda yake nuna alamun dakin taro ne sun kai su goma wannan yana wane wannan sun sha lafiyayyun shaddodi sai motsi takeyi tana sheki masu Cot a cikinsu kadan neKai tsaye rumfar dasu Wasilar suke suka nufa ta ganinsu sun doso gurinsu sai ta mike da saurin gaske ganin harda Governor ya sanya ta fara masa kirari da bambadanci dama Wasila akwai shegen zakin murya tsiya Governor tun kafin su karaso yake murmushi babu shakka wannan yarinyar zaaje da ita irin wannan washi haka Gabadayansu suka mike tsaye ganin sun iso gurin Lauje dake jin haushin abunda Wasila takeyi ya buga mata tsawa da fadinAi sai ki saurara haka domin mai girma governor ya iso ki bamu damar magana Wasila tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya

Gaisuwa suka mike garesu suka amsa sosai Alhaji Maaruf ya kalli Lauje yaceKaine wakilin tafiyar ya akayi alamu na nuna mana cewa akwai nasara a tafiyar Kafin Lauje yace komai Wasila tayi karaf taceAlhamdullihi muke da nasara insha Allah domin tun zuwanmu gurin muka watsa shirinsu muka tashi hankalinsa dana jamaarsa ni da kaina na dinga bin pastes dinsa da suke mannawa ina yagewa ina watsa masa ruwan kwata da bakin mai da kyar nasha a hannun wani dan daba

Governor Ya kallesu yana fadinDa gaske maganar haka take Duk suka amsa da Hakane ranka ya dade Lauje yaji tamkar yaje ya shake wuyan Wasila shin wai me take nufi ne yarinyar fa ta zake da yawa anya ba sai ya taka mata burki ba kuwa

Governor Ya kalli Wasila yana murmushi YaceDama tun kafin na ganki na samu labarinki gurinsu Alhaji Maaruf gaskiya ne Yar gaske kin cancanci ayi miki komai zamu zauna dake insha Allahu ki fada mun dukanin bukatunki Wasila aka saki murmushi ana gyara tsayuwa farin ciki duk ya isheta taceGodiya nake mahadi mai dogon zamani governor da ba tabayin irinshi ba ba zaayi ba insha Allah tana gama maganarta Ta koma ta zauna inda take kana ganinta zaka gane tana cikin farin ciki babu shakka bukatarta ta kusa biya sun kusa yin hannun riga da talauci

1 thought on “Yar bangar siyasa complete hausa novel”

Leave a Comment