Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete

Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete: Romance Love And Sympathetic Story Written By Aisha Mamanteddy

Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete

 

Page 01

Ga masu buatar na tallah ta masu hajar su zasu na biya 2000 Idan a status kacal zaa yi Miki advert in zaki biya 1000 only Sai ku tuntui wannan number nawa 08081202932 Please wacce tasan zata karata Wannan labarin ta karanta shi yanzu tun daga page 1 bana so sai nayi nisa ki biyo ni akan na baki from the beginning ba zan iya ba gaskiya ayi mun uzuri hidimomin nada yawaSannan Ayi Hauri da posting din zaku ga ba tsawo babu yawan read more

830pm
A hankali take shiga layin tana kallon iyar nata lokaci bayan lokaci wacce tayi lawaam a hannu mahaifiyar nata are ma matan kallo nayi tare da yarinyar wacce ba zata Wuce shekara aya ba a duniya Malam mai Adaidaita maza yi gaba wurin Wancen Gidan mai Dakali zaka Sauke ni Cikin an aga murya mai Adaidaitan yayi magana duba ga yanda ake tsala Ruwan Sama dole sai ya aga murya na bayan sa zai jiyo sa Saboda aran Saukar Ruwan saman Ina kenan Hajiya Da hannu tayi masa Alama yayin da cikin sauri ya arika bakin ofar Gidan yana fain Hajiya mun iso Sauke Gajeruwan numfashi tayi tana saukowa daga napep din cikin sauri tare da kudundune yarinyar nata da Mayafin ta Kaan jira Ni mintuna biyu zaka koma dani filin Saukar jirgi na nan aviation Kamin me keken ya bata amsa tayi saurin shigewa cikin Zauren Wannan Gida saboda Ruwan da ake yi

Tun daga zauren Gidan take jiyo hayaniyar matan Gidan tamkar ba ruwa ake yi sama asa ba Girgiza Kai tayi tana kallon Amrah yarinyar da bata san komai ba a rayuwar ta a hankali ta furta Allah ka gani ga Amrah nan ba barma A hannun ka da kulawar ka Allah ka kare mun Amrah daga cikin sharrin mutanen Gidan nan Rintse ido tayi tana tuno da Sasa sasa na wannan Gidan don gidan yawa ne yawan su kuma ya haura mutum sabain yara da manyan su Rungume Yarinyar tayi idanun ta na Saukar da Hawaye masu zafi da raai ina Son ki Amrah amma dole ce tasa zan barkinan shine Miki dahir dole tasa zan kawo ga dangin ki Ni mai saui ce Nasan ko mun daewa zaki nemi ne domin kuwa ke Yar halak ce duk dan Halak baya mantawa da Uwar da ta haife shi Motsawa tayi da arfi tana aga afarta tare da shiga Gidan kai tsaye bakin ta auke da Sallama Assalamu alaikum Tayi maganan tana kutsa kanta zuwa Farfajiyar tsakar Gidan Mata ne ta gani sunfi Ashirin a cikin ruwa wannan tana sukola wannan tana Aikin shiga madafi Kitchen inda ko rufi babu sai uban hayain itace dake fita kaman An ona taya Kowa Aikin gaban sa yake a ruwa sam basu damu da lafiyar su ba kona yaran su da suke ta aikin taya su aikin gidan

Hasko fitila Larai tayi tana furta Innalillahi wainna ilaihir kasa arikewa tayi saboda gulma dake cin ta a rai cike da aga Murya ta ke fadin Hafsatu kece Jummai ne dake kitchen tayi Saurin fitowa tana fain Wacce Hafsatun ke kuma da Wane haka Wata kuwa Hafsatu kika sani bayan Dakta Hafsa dai da kika sani Sakin fitila Jummai tayi a asa tana kama wankwaso tare da cewa Au kin dawo kenan Kin karasa inda zaki kai Yar zinan taki shine kike kokarin maala mawa mamacin da ya mutu shekaru Bakwai da rasuwar shi sai a yanzu zaki kawo yarinya yar shekara daya kice wai cikin Auwalu ne Kai Hafsatu kiji tsoron Allah dakta Hafsa ki tuna ALLAH fa aya ne Kayya Jummai Ai da kin barta munji ta bakin ta da kuma mene tazo yau Wancen karon dai munji tace ta Haihu yanzu kuma fa mene ya faru Baba Zuwai tayi maganan wacce take fitowa daga akin ta duka kuma sunyi zaman kishi da Hafsatu

wallah ne ya gangaro fuskar dakta Hafsa a hankali ta furta ba sai na maimaita maku matsalar da aka samu ba domin na faa muku tun fari amma Amrah Wallahi Bata da Uban da ya wuce Auwal aidu Lahaila Muryar mata da yawa na tsakar Gidan suka hada baki suna fadin aidu kika ce bayan Sunan mijin naki mai rasuwa har sunan uban da ya haife shi kika fai Jummai ne ta kalli Baba Zuwai tana cewa Aa Illar Auren bariki kenan ai A bariki ya Auro ta yo duk mijin da ya Auri mace yar Lagos ai dama sharri da bariki a jinin su take To ki tattara ki fita kamin mu hadu muyi Miki shegen duka Allah sai mun sauya kamannin ki wanda ke kanki ba zaki gane kan ki ba Zuwai tayi maganan cike da zafin kishi yayin da Jummai ta kalli Hafsatu tana cewa Kece dai Yar bariki amma mijin mu ALLAH yajian sa da Rahma mutumin kirki ne soja adali kisisinan ku ta yan duniya kikayi kika shigo kika Aure sa A yanzu ya mutu Baki da Gado mai Gwai shine kika yi cikin shege tsawon shekaru biyar sai yanzu kice wai kina da cikin shi kwanciya cikin yayi sai yanzu ya fito duniya Dalla tattara ki bar mana cikin gida kamin Ya isa Jummai Hafsatu tayi maganan tana tsiyayar da Hawaye Ruwa na dukan tsakiyar kan ta Fiddo da Amra tayi wacce ta rufe a Mayafin ta kana tace Ga Amrah Nan ne Gidan su ba da ita nazo cikin gidan nan ba anan na same ta Don haka itama yar Gida ce Na kawo ta Wurin ku saboda bata da Wasu bayan ku Ku rie Amrah koma duk Abin da zakuyi mata Ni dai na sauke nauyin da ya rataya mun na dawo da ita dangin mahaifin ta

Kan uba Waye zaki kawo mawa Yar Zina ya rie Jummai tayi maganan tana kama ugu kamin Baba Zuwai tace To da yake akwai annin Auwalu da yayyi ku matan su ai sai ku amsa tun da zaa nuna mana boko dole a rufe mana ido ga gaskiya mun san shi Mata ne sunfi talatin suka taru duka matan gidan ne wasu jin Hayaniya yasa su fitowa jin maganan da Jummai tayi yasa su duka hada baki suna cewa Wane Ta ai ko babu mazaunin yar zina a aku nan mu Baba Zuwai ce ta kalli Hafsa wanda gudun Hawayen idanun ta ke aruwa To kin dai ji don Allah ki dauki yar ki ki fita da ita kar ku bata mana suna ace gidan Kanol Auwal aidu har da yar zina Kinga kin cuce mu mijin mu baiyi yawon duniya ba ki rufa mana Asiri

Kallon Amrah tayi tana Fiddo da ita tare da Aje ta a asa Ruwa sama ruwa asa Wani irin tsala ihu yarinyar ta fara Wacce ko tsayuwa ba tayi sai rarrafe Ga Amrah nan duk yanda kuka yi da ita mai kyau ne Ko ku rie ta tamkar a ko kuma ku auke ta AR TSAKAR GIDAduka wannan zain naku ne Nayi gaba kuma ba zan Waiwayi Amrah ba har girman ta Tana gama Fain haka ta juya tana ficewa daga cikin gidan Yayin da su Baba Zuwai ke fadin kai da Allah kowa ta tafi akin ta mu shige da kanta idan ta leko taga yar ta a Tsakar gidan zata auke ta waye zai rie ar Zina Aa wane kuwa Matan suka mara mata baya suna shigewa dakunan su har da masu rufo kofa wasu na sakin Labulayen su Wani irin ihu Yarinyar Jaririyar da Bata wuce Shekara daya ba take yi a tsakar gidan tana rarrafawa tare da bulayi a tsakar Gidan ruwa na dukan ta haka take yanka ihu tana ware ko zata ga Mahaifiyar nata amma kuma bata ganta ba.

Karanta: Kuyanga Hausa Novel Complete

2 thoughts on “Yar Tsakar Gida Hausa Novel Complete”

Leave a Comment